Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yan Mazan Gidan Soja

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 

Doka tambarin nasara, ‘yan mazan gidan soja.

Yusufu Tukur Buratai, ‘yan mazan gidan soja.

 

Mai isa da duk lamari Zuljalali Sarkina,

Mai tajarrabin komai Rabbana maƙagina,

Mai isa da masu isa na taho da waƙena,

‘Yan mazammu zan waƙe soja yau a bakina.

 

Kui kiɗa kiɗan kurya zan yaba wa ogana,

Kui kiɗa kiɗan jauje za ni waƙe ogana,

Ko badujalar begila busa tambarin ɓauna,

Za ni waƙe ɗan Yusufu shugaban mazajena.

 

Tafiya mazan tafiya bak ka zo da wasa ba,

Anniya mazan aniya bak ka zo da wargi ba,

Mun ga burbushin nasara ba da tada kura ba,

Mu muna saye da kashi ku kuna kisan gaba.

 

Da watanni ‘yan baya ba zama na daɗi ba,

Ba zaman lumana ba, ba zama na aiki ba,

Ba zama na ƙauna ba, ba zaman zumunci ba,

Da zuwan Tukur Isuhu ba mu ƙara wannan ba.

 

Garkuwa ga sojoji Yusufu Tukur nawa,

Garkuwa ga al'umma Yusufu Tukur nawa,

Jiya ana kisan soja ba makamin ramawa,

Yau kisan fa an ƙare kan faɗi da ƙiftawa.

 

Tattalin Arewawa wanda an ka rusawa,

Kasuwa wajen aiki wanda anka ƙonawa,

Dukkanin wajen bauta da wajen karantarwa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments