Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Tagwayen Masu

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Yau murna da shekaru aba'in da biyar a kan karagar mulki,

 

Allah ƙara ja da nisan kwana,

Allah ƙara lafiya da karama,

Ɗan Bayerro karimin sarki.

 

Mai martaba magajin Dabo,

Taka lafiya a sannu a sannu,

Ɗan Abdullah mai tagwayen masu,

Sarki Allah ƙara nisan kwana.

 

Ya sattaru kaliƙi mabuwayi,

Allah nai nufin yabo ba shayi,

Don cika alƙawar da nai yi wa bayi,

A yau kaliƙi gwani mabuwayi,

Allah kar ka yarda in yi bulayi.

 

Allah kai daɗin salati dubbai,

Gun Mahamudu alihi da sahabbai,

Mai horo ga masu bauta baibai,

Arnaku da masu tsubbu a baibai,

Tsanina da sonsa za na yi dubbai.

 

 

 

Hujjata ta baituka ga Kanawa,

Batun alƙawar nake cikasawa,

Talifin hawa zuwa Nasarawa,

Fanisau da Ɗorayin da na cewa,

Hawan Daushe zan ida sanarwa.

 

Kanawa ku zo ku ji ku jiyarwa,

Tarihi a yau na maimaitawa,

Mai jan hankali da ilmantarwa,

Al’adunmu kwai abin birgewa,

Allah sa ku ji ni ba ƙosawa.

 

Farko za ni waiwaya Nasarawa,

Shekaru kusan ɗari da ɗarawa,

Zamanin Abbas sarki na Kanawa,

Gidan Shattima ke zuwa gaisawa,

Rasdan kan tare shi don gaisawa.

 

Gobe da safe sai hawan Nasarawa,

Zuwa Rassidan hawus Kanawa,

Daga nan sarki yana zagawa,

Bigiran bauba’i na Kanawa,

Yai masa ramako a gaggaisawa.

 

Fanisau fa shekaru uku baya,

Sarki Rumfa zamaninsa a baya,

Kafin Ussumanu Fodiyo ku jiya,

Baƙo yaf fito na magrib ku jiya,

Don tajdidin Islamiyya.

 

Shehu Magili ya zo alƙarya,

Shehu ya zagaya cikin zawiyya,

Wajen tsohuwar mayanka ku jiya,

Sabodaz zuwan Muhammadiyya.

 

 

 

Sarki Rumfa sahibin addini,

Ma'abocin kusantuwa da masanni,

Tsararren gida abin so a gani,

Fanisau a can akai massa gini.

 

Daga ƙarshe Zauren Tudu fa ya dawo,

Shi ne ya zamo a san da ya jawo,

Da'irar shariftaka da ta kawo,

Asalin salsalar sharifai kawo,

Har a naɗe ƙasa suna daɗa yalwo.

 

Kun ji fa salsalar hawan Fanisau,

Allah sa ku gane kar ku yi nusau,

Ala ko a gobe ya yo nusau,

Labaran da nai zaya maye sau,

Ga ta'alifin abin ba nusau.

 

Adadin shekara ɗari can baya,

Da ɗori na hamsin can baya,

Aka somo hawa na daushe ka jiya,

Asali Shamaki na sarki ku jiya,

Sarki Ussumanu mai alkunya.

 

Shi ne yai hawa na salla babba,

Shamakinsa bai fa samu zuwa ba,

Sunan shamaki na sarki babba

Daushe an kace lakab ba wai ba,

Ba shi da lafiya a kai bai je ba.

 

Samun lafiya ta daushen sarki,

Sai yai azzama ta gaida saraki,

Ya je gaisuwa a fadar sarki,

Yac ce an hawa ina jin jiki,

Zan maka naka inji babban sarki.

 

 

 

Kun ji fa assalin hawan daushenku,

Za ni in bayyano hawan dabarku,

Ku ba ni aro na hankula kunnuwanku,

Tin asalin sarauniyar ingilan ku,

Ta je indiyan ziyarar mako.

 

Sai suka karramata an kai yi bikki,

Sun ka aza ta bissa doki na biki,

Shi ne assalin zaman mana biki,

Domin karrama ga dukkan baƙi,

Kun ji hawan biki na daba a doki.

 

Sai fa hawan durumin shure saraki,

Hawan kewaya na gonar sarki,

Ranar issuwa Haɗeja saraki,

Tarihinsa ya ɓace a saraki,

Ba a yin hawan a yau a saraki.

 

Zan yi batun hawan Gogel kumama wa,

Birnin massana a da na Kanawa,

Mafakar ‘ya’yan saraki Kanawa,

Lokacin da za a fafatawa,

Gogel can ake zuwa ɓoyewa.

 

Can ma da ana hawa na musamman,

Salla a kai ziyara ɗin nan,

Yau ya zamma sai a tarihin nan,

Ba a yin hawa a je birnin nan,

Gogel ta zamo a tarihin nan.

 

Hawan Ɗorayi na ƙarshe Kanawa,

Abdullahi Bayero na Kanawa,

Shi ya assasa shi don hutawa,

Gandu ne guda da shi yaka jewa,

Ɗebe kewarsa kun ji Kanawa.

 

 

Mai mulkin Kano adon alƙaryu,

Bayero ba ya goya marayu,

Malafa ta sarakunan alƙaryu,

Ka ga naɗin da yaw wuce yuyuyu,

Sarki maganin miyagu mayu.

 

Tsafi bashi cin ka don alhayyu,

Gatan makkarantun islamiyyu,

Na sake kiranka goya marayu,

Mai ɗebe hasan marasashin tanyu,

Allah ƙara lafiya alhaiyyu.

 

Ala Kannawiyu ne fa Kanawa,

Mai sautin yabo da alkintawa,

Domin taskace tarihin Kanawa,

Kar ku sake abin ya zam sheƙewa,

Mun haɗu marrina da majjemawa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments