Ticker

6/recent/ticker-posts

Sadaukin Lafiya Maigirma

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Sadaukin lafiya maigirma,

Allahu ya ƙara alfarma,

Farar aniya abar jewa,

Ga mai nasabar gidan girma.

 

Shimfiɗa

Farar laya abar sa wa ga mai aniya ta alfarma,

Tuwon girma miyar nama yana a gidan halin girma,

Halin girma ake yi wa yabon girma da alfarma,

Da an nema ake samu da an yi gamo da alfarma,

Da masu kama ake ƙota sadaukin lafiya mai girma,

Da mai da kama ake aika sadaukin ba dama,

Baƙar niya baƙin hali yana a wajensu ‘yan nema.

 

Abin bauta abin roƙo Allahu Ubangijin kowa,

Muna ta yabo da gode ma abin da ka yo ka karawa,

Kai alƙawari da mun gode ka ce kuma za ka ƙarawa,

Sadaukin lafiya ya gode ka ƙara yi mai naɗin girma.

 

Muna ta yabo gurin Mamman Habibullahi son kowa,

Da Ali kaza sahabbai nai madubin kwaikwayon kowa,

Haɗa ataba'u har ulama madubi gwadaben kowa,

Alhamdu Ubangijin kowa muna daɗa godiyar girma.

 

Ina waƙa ta murna ce da ba ka sadauki mai girma,

Allah ya riƙa maka gwarzo na Laraba mai halin girma,

Hali aka ce ya zam jari ga mai ƙuduri na alfarma,

Da mai manufa ta alkhairi nake yi wa tamburan girma.

 

Katafare da hamshaƙi cikinsu ina kwatancinka,

Uban tafiyar maje Hajji ina tuna randa na gan ka,

Kamala kwarjini haiba mu'amilla irin taka,

Abin sai ka gani Malam ka ce Allah sanya albarka.

 

Ɗiyan girma irin girma suke da hali irin naka,

Ko da a cikin dubu Malam yana da wuya irin naka,

Ku tambayi maigida Wambai a kanka yana faɗin barka,

Chiroman san Kano gwarzo yana yaba nasabar girma.

 

Uban gayya maja aiki kawai a kira ka dumfama,

Idan na kira ka dumfama yana ma'ana ta sha fama,

Kabiru na Bayero barde yana ta yabon halin girma,

Sadaukin lafiya hamshaƙi katafare gidan girma.

 

Nagarta ce ta sa sarki ya yi maka tambarin girma,

Sadaukin lafiya mai girma na Laraba ka ci alfarma,

Allahu ya ja tsawon kwana na sarkin lafiya mai girma,

Muna ta yabon farin sarki Allahu ya ƙara alfarma.

 

Sadaukin lafiya daji da ba shi yiwo a mai ƙyaure.

Magauta sun yi sun ƙosa a ƙarshe ma fa sun tsere,

Abin sha'awa fagen kallo abin ƙauna da saurare,

Sadaukin lafiya mai girma na Laraba ka yi ba dama.

 

Abin ƙauna abin fari ubanmu na lafiya mai girma,

Dakta Isa Mustafa Aggwai Allah daɗa martaba girma,

Aliyu Muhammadu Oga Andoma ina yabon girma,

Abdullahi Amegwa Agbo na yaba taka alfarma,

Osana na kena ciki na masu yabo a alfarma,

Maigirma uban gayya Ummaru Tanko ba dama,

Umar Tanko Almakura na yaba taka mai girma,

Gai da sarauniyar mata uwa ga Abubakar ce ma,

Uwa ga na Laraba Mairo Tanko ina yabon girma,

Mairo Tanko Almakura na yi yabonki don girma,

 

Tanimu Tansy mai girma na yi yabo na alfarma,

Yabon barde a zangon nan gidan girma tsatson girma,

Kabiru na Adamu sarki na Bayero ka yi ba dama,

Ina ta yabo ga Barista Chairman Commision Hajji,

Abdullahi ɗan Mamman maje haji na yabon girma,

Ina ɗaga jinjina gun Nas Aliyu wada halin girma,

Ina ta yabo gurin sambo na shehu balaraben zazzau,

Gurin sarkin kudun Zazzau Allahu ya ƙara alfarma.

 

Ina ta yabo gurin wambai Aminu na sankano sarki,

Mai girma ɗan gidan girma abin fahari da alfarma,

Cikinsa yabo da chirroma na sarki ka yi ba dama,

Nasiru Adamu sarki Allah ya jiƙan mazan fama,

Fage na yabon ɗiyan sarki na sa da murabus mai girma,

Sanusi mujahidi babba Allahu ya ƙara alfarma,

Na sa da Aliyu ɗan Ado na Bayero mai hagun dama,

Aliyu santurakin nan Kano na nuna alfarma,

 

Abas Nuhu ɗan Bamallin nan Allahu ya ƙara alfarma,

Ciki Ibrahimu da gun Balarabe mai halin girma,

Na kagara santurakin nan ina ta yabon halin girma,

Hasan ɗan baba ka yi agar a masu halin jinin girma,

Magaji na garin Sokoto ina ta yabo ga alfarma,

Alhaji ga yabo isa dogon yaro mai girma,

Ina Abdulmalik Shehu Mahdi ga yabon girma,

Ina Attah Ikeleji dan Usumanu mai girma,

 

Baba Sule a gaishe ka wakilin Zazzau girma,

Na saka gaisuwar ɗan Moyi na lafiyar girma,

Na saka gaisuwar ɗan Morin na lafiyar girma,

 

Jakadan sarakunna, nasarawa ina yabon girma,

Alhaji Babayaro Mukhtaru ina yabon girma,

Abdallah na Laraba mai alfarma ga yabon girma,

Makaman Keana mai girma,

Mustapha na Laraba mai girma,

Zainab jafaru mai girma,

Fatima Mohammadu Osana,

Ina ta yabon halin girma,

 

 

 

 

Rakiya Abubakar Igomu,

Ina ta yabo na alfarma,

Maryam Yusuf Oshafu,

Ina ta yabo da ba dama,

Hassana Hassan na Laraba.

Ina ta yabon halin girma,

Aisha ali Almakura na yi yabo da alfarma,

Halima Umsy dana, ina ta yabo da alfarma,

Mairo Bulama na zo in ƙara yabon halin girma,

Anty Hajjo P.A ciki a yabo na alfarma,

 

Amina abubakar na Laraba na yi yabo da alfarma,

A’isha Abubakar na Laraba na yi yabo da alfarma,

 

Abar alfaharin kowa A’isha mahaifiyar girma,

A yau badali ake murna na Laraba yai halin girma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments