Amshi
Sadaukin lafiya mai girma ga kansalin fama,
Abubakari namijin fama na Laraba gogarma.
Allahu ya ja kwanan sarki na lafiya dumfama,
Don ya yi naɗin namijin fama na Laraba mai girma.
Shimfiɗa
Sabo da maza aka ce jari na Laraba mai girma,
In ka ji sadauki ba dama ba yanzu in sheda ma,
Karon battar ƙarfe ne ma amo na mazan fama,
Duk wanda akai wa naɗin girma sadauki dumfama,
Matsa ka ji ba da garaje ba batunsa fagen fama,
Fagen ilimi ba wasa ba bare a fagen himma,
Fagen jarumta ba wai ba kira shi mazan fama,
Duk inda ka juya ba dama kira shi da gogarma,
Sadaukin lafiya mai girma Allahu ya dafa ma,
Ga baitoci don alfarma na Laraba sha fama.
Allahu abin a yi wa bauta da babu ɗigon wauta,
Sarki makaɗaici wanzajje da yay yi halittata,
Wanda na kaɗaita kwalli dai mai amsa buƙatata,
Ka ƙara azurtan ƙirjina ka ninka fasahata.
Tsira da aminci ƙara wa Habibu masoyinka,
Wannan da ya sa mu fahince ka mu ƙarfafa bautarka,
Don shi ya rabe tauhidanka saninsu a bautar ka,
Rububiyya da kuluhiyya da tsarkake sunanka.
Waƙa ta tukuicin ƙauna ce domin ta masoyi ce,
Ƙauna ga na Laraba gun sarki ta mai rawanin zarce,
Ƙaunar ALA a gurin barde ta zamma saɓe zarce,
Ta shafi sadaukin alfarma na lafiya kai zarce.
Mai saurare bari mamaki a kanta batun ƙauna,
Ƙauna matsayinta muhallinta ya zarci tunanina,
Dan lura idan ka kira Allah ka ambaci manzona
Ƙauna ce tai sanadin wannan a gane jawabina.
Abubakari bari in zano waɗansu hasashena,
A kan sanadi na naɗin sarki kaɗan a sanin kaina,
Hasashe tuntuni tarihi a ba ya da yanzun na,
Rukunnan da ka naɗin sarki ka ji daga bakina.
Da fari akwai jarumta kau tana rawanin sarki,
Sannan ilimi rukuni na biyu yana tawanin sarki,
Sai wanda ya gaji gadon sarki yana rawanin sarki,
Ko mai mulki daga zamani yana rawanin sarki.
A cikinsu na Laraba wane ne ciki ba ka taka ba,
Ina rabe masu jinin sarki da iddo da na duba,
A kyakkyawa ta mu'amilla ake rabe ɗan babba,
Ɗiyan girma suka san girma ko da ba a duba ba.
Muƙami sakkatare kay yi da na zuwa Hajji,
Jagoran masu zuwa Makka na Laraba alhaji,
Aikin nan sai da gwadin ƙarfi ba wai na gwajin ƙwanji,
Mai ƙarfin halin jajirta zai ja ragamar hajji.
Idan ko na kalli mu'amilla kana da halin kirki,
Mutum da halinka fa yai jari saboda halin kirki,
Hali tarago a fagen tafiya ga masu halin kirki,
Irinka siyasa da za sui da an ga halin kirki.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.