Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubakar Na Laraba

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amsoshi

Na doka tambarin girma,

Sadaukin lafiyar girma,

Abubakar na Laraba,

Rabbu Allah ya makka jagora.

 

Doktoro tinjimin sarki,

Dakta isa agwai uban kowa.

Sarkin gari na alfarma,

Ya yi naɗi na alfarma.

 

Shimfiɗa

Togonmu Rabbana sarki Rabbu,

Kare mu kan ɓatan hanya,

Don Musɗafanmu maigirma,

Sarkin rabo na alfarma,

Mai tambarin gidan girma,

Mai tambura na alfarma,

Dumfama kuma sha fama,

Baban ɗiya ta alfarma,

Zahara’u kuma Faɗima,

Sai mai rabo da alfarma,

 

Allah Buwayi Sarkina mai tsare rayuwa dare rana,

Duk malakutu na gunka tasarifi na kauni Sarkina,

Kun fa yakunu in kac ce zai kasance a take Sarkina,

Yarje a baitukan ALA ka zamo mai tsaro ga bakina,

 

Farko da goɗiyar Sarki za ni faro batu a waƙena,

Mai tambura da kakaki mai ƙasar lafiya abin ƙauna,

Jinsin gidansu allimi ga irin sef Ali sarkina,

Doktoro Isa mai girma na karatu na miƙa godena.

 

 

 

Toro ubangidan giwa inda duk yab bi nan ake hanya,

Dukan da za a wa jaki walla sai dai a yi shi kan jinya,

Fili wajen kure doki kyale jaki a bar shi kan hanya,

Kwana anai a kan hanya walla sai raƙumi uban hanya,

 

Jaɓɓama Bubakar gwarzo ka zamo dogari na alƙarya,

Da mai kama ake ƙota in da kaj ji sadauki ba ƙarya,

Ƙarya fure take goga ciɗiya ta wuce icen ƙarya,

Zauna sadauki mai girma ga sadauki na lafiya ƙarya.

 

Taka da lafiya gwanki yau fa ranarka ce muna zarya,

Damanka lafiya alher haka hauninka lafiya hayya,

Jirga a sannu saddauki nal Laraba Garba mai kunya,

Ya Rabbana ya dafa ma yaz zamo mai saka ka kan hanya.

 

Duk wanda dogaronsa ya zam Allahu mai tsaron bayi,

Ya mai da lammarinsa a gun Allahu mai biyan bayi,

Ba wanda zai ji shakka dukka abin da yai nufi zai yi,

Komai gare shi zai sauƙi ya zamo kamar ruwan sanyi.

 

Ka ƙara gode Allah Garba a kan abin da yau kay yi,

Ka dubi jamma'a taron ga a yau halinka ne yay yi,

Duk wanda hasada ta makanta ba shi gane me kay yi,

Zai ɗora soke-soke yana cewa su wane ma sun yi.

 

Taka a sannu sannu na Laraba ka zamo sahun girma,

A yau fa kai ɗarin tsara duka sai su zo su dafa ma,

Su zo kawai su gaishe ka daga duƙe don halin girma,

Ga tamburan sadaukin lafiya mai hali na alfarma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments