Ticker

6/recent/ticker-posts

Santuraki Ali Ado Bayeronmu

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Santuraki Ali Ado Bayeronmu uba,

Mai hali na gari ba shi ganin ahir da atir.

 

Shimfiɗa

Mai kwarjininmu Ali mai hali da ba bidiri,

Alfaharinmu Ali jagora da ba garari,

Adon ganinmu Ali hamshaƙi abin fahari,

Mai kyauta yi da isa kai gadon hali na gari,

Mai kyan hali da kama annuri fa ga sururi,

Ga hakiminmu Ali tauraron tsakar sarari,

 

Burin ganinmu Ali,

Adon cikinmu Ali,

Mai kwarjininmu Ali,

Fatan dukanmu ali

Zaƙaƙurinmu Ali,

Mai haƙƙurinmu Ali,

Ga jaruminmu Ali,

Ga haziƙinmu Ali,

Mai martabarmu Ali.

Ubangidanmu Ali,

Mai taimakonmu Ali,

Bai kyankyaminmu Ali,

Mu addu'armu Ali,

Allah ka baiwa Ali,

Gadon gidansu Ali,

Santuraki Ali Ado Bayeronmu uba,

Mai hali na gari ba shi ganin ahir da atir.

 

Ya massanin lamari mai iko a kan lamari,

Mai kyauta yi da isa mai juyi na al'amari,

Roƙon bara na taho gun Sarki na al'amari,

Alƙauwarin da ka yo na zo gunka Alƙadari.

 

Kafin na ce uffan nai kamun ƙafar Bashari,

Mubasshiru sabiri wanda ya ida alƙawari,

Muhammadul bashari mai bushira da alƙawari,

Don so da bin ahali Allah karɓi duk ƙuduri.

 

Bayinka ne Ahadun masu buƙatuwa ƙuduri,

Buri zuwa ƙuduri ba mu nufin waninka gari,

Ka ce inni u'udi kai aka kai wa duk lamari,

Mai amsa al'amari amsa ƙudurduran sha'iri.

 

Rana idan ta fito ba a hana ta haska gari,

Ga haddari ta gabas ba a hana shi nashe gari,

Yana jiran izinin al-mukutaddiru Ƙadiri,

Gagara al'amari mun miƙa maka lamari.

 

Taka a sannu Ali ƙara daɗin ɗigon haƙuri,

Matsa gurin Muhuyi mai iko na raya gari,

Kyauta gurin ahadi ta fi zubar ruwan madari,

Matsa da yin zikiri babu dare da waye gari.

 

Kwatankwacin sukari ne da maɗi zuma a gari,

Kowansu na da guri babu gamin zuma sukari,

Daɗi da gyara jiki ga asararu gyara gari,

Hakan yake a waje ko daga da'irar shi'iri.

 

Ubangida na gari ja mu ka kai mu ba bidiri,

Shugaba na gari linzamin mazauna hari,

Hasken ɗiyan sarki tauraro da ke marari,

Alanka ke ta yabo bana wuri ba koko ɗari

 

Nasan Kanonmu Ali ƙanin Wamban Kanonmu Ali,

Ƙanin Chiroma Ali jinsin Ɗanburan fa Ali,

Jini na Dabo Ali jikan Bayeronmu Ali,

Jikan Abashe Ali tauraro da ke marari.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments