Sarkin Bauchi Ka Gama Lafiya

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi 

    Taka lafiya Lirwanu sarki mai ƙasar Bauchi,

    Godewa kainuwa dashen Allah buwayayye.

     

    ShimfiÉ—a

    Taka lafiya zakin sarakai mai ƙasar Bauchi,

    Hauni lafiya Lurwan sadauki ka'imin sarki,

    Limamin gari hadimin gari Lurwanu hamshaƙi,

    Limamin sarakai sarakuna sun ka don jinƙai,

    Jeka lafiya ƙas! Arna mai tausai ga mussakai,

    Ga amawali na sarakuna na Arewa ba miki,

    Mai gidan tara burijinka mai ƙarfi farin sarki,

    Tuta tara rijiya tara dutse tara sarki,

    Soro tara rijiya tara mai kibbiya zabgai,

    Haika lafiya Lurwanu kai mulkin masoyana.

     

    Ya sarki Allah yadda kay yi ba mai ce da kai a’a,

    Yadda duk ka so babu masu cewa lala ko a’a,

    Na yi sujjada yarda duk ka so ka yi na yi ma É—a'a

    Sami'ina Allah Rabbu wa adana ba ni ba a’a.

     

    Mai iko Allah mai tasarrafin duka jinnu insanu,

    Kun fa ya kunu na akasa na iko naka Rahamanu,

    Lamuninka ne na aron sarautar bawa Rudwanu,

    Ga Alan waƙa na tujaddudin sarkin ga Rudwanu

     

    Allah na gode da ka yi ni bawa naka insanu,

    Ka ara mani sunan masoyi naka Aminu,

    Baban FaÉ—ima Al'aminu bawa naka Mannanu,

    Alfarmar ƙauna ta sa duk abin da na yo da alfanu.

     

    Ka ji begilan za ka tar da soja maza É—iyan gama,

    Ka ji jiniya za ka tad da gomna ko uban fama,

    Ka ji tambari ko duma na girke ana bugun fama,

    Jeka kag gano za ka tad da mai rawani na alfarma.


     

     

    Ka ji baituka na hawa da sauƙa babu kakaci.

    Ka ji baituka ba harigidu sam babu gwaranci,

    Ka ji salsala jere ba kwatar harshe da ninanci,

    To yabo nake yi wa mai sarauta babu lalaci.

     

    Linzami da wuta magani na sangarta tunanina,

    Jadari na kasa magani na mai kabido masoyina,

    Iskar guguwa mai sauya al'amra a hangena,

    Igiya ta ruwa mai sanya kogi yai ta kara-kaina.

     

    Ginshiƙi na suga sha lasar bayi kwatancena,

    Sararin gudu mai sa fatake su yi ta kara-kaina,

    Hadarin bana ya taho da alkhairi da alfana,

    Zauna lafiya Rudwanu kai mulki masoyina,

     

    Zauna lafiya Lurwanu zauna da kyau farin sarki,

    Miƙe lafiya Lurwanu miƙe da kyau farin sarki,

    Hauni lafiya Lurwanu dama da hauni ba miki,

    Namijin giye Lurwanu ka zama jinjimin sarki.

     

    Duka É—an tsuntsu ya san da kukan shirwa ba wai ba,

    Haka É—an dabba ya san da kukan zaki ba wai ba,

    Jinsin mutum za ni in bayani ba da wai wai ba,

    Ana ce maka sarki kawai juya kana haiba.

     

    Kai ka gaji Yakuba mai ƙasar garin Bauchi

    Kai ka gaji Ibrahim a cikin garin garin Bauchi

    Kai ka gaji Usmanu mulkin garin Bauchi,

    Kai ka gaji Ummaru da riƙon garin Bauchi.

     

    Kai ka gaji Mu'allayidi a garin ƙasar Bauchi,

    Kai ka gaji sarki Hasan a cikin garin Bauchi

    Kai ka gaji Yakuba na biyu a garin Bauchi

    Kai ka gaji Yakuba na uku a garin Bauchi.

     

    Kai ka gaji Adamu Gimba anan garin Bauchi,

    Kai ka gaji sarki Sulemanu a garin Bauchi,

    Mai martaba ta É—aya a cikin garin Bauchi

    Turka lafiya taka sannu-sannu don garin Bauchi.

     

    Ƙofa tara zani in karanto babu karkarewa,

    Ƙofa taran, ƙofar Wunti, ƙofar Nasarawa,

    Ƙofa ta Wase da ƙofar Jahun ku jiyowa,

    Ƙofar Dumi da ƙofar Inkil na zanowa.

     

    Kofa ta Wambai ta takkwas a karantowa,

    Kofa ta Tirwun ta tarra aji na zanowa.

    Zan zayyano maku dutse tarra ba kwawa,

    Daraja da alfarmar mai ikon uban kowa.

     

     

     

    Dutsen Wurinje da dutsen Kobi na faÉ—owa,

    Dutsen Iya dutse na Gayya na jero wa,

    Dutse na Ƙofar Dumi a ciki na sanyowa,

    Dutse na Bauchi da dutsen Shi ku jiyowa.

     

    Kirari

     

    Taka lafiya dai zaki Rilwanu sadauki,

    Limamin sarakuna,

    Taka lafiya ƙas arna,

    Sarki sa É—ar da zumunci,

    Amawalin Arewa,

    Sarki me ƙofofi tara,

    Duwatsu tara,

    Soro tara,

    Rijiyoyi tara,

    Tutoti tara,

    Me zabgai da ƙare dangi.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.