Tamburan ‘Yan Maza: Nuhu Mamman Sunusi

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Tamburan 'yan maza daban mazaje yake,

    Nuhu Mamman Sunusi ka gama lafiya.

     

    Shimfiɗa

    Ga masaba masarrafi ƙarafa yake,

    Da tama assalin dukan ƙarafa suke,

    Korami ko ma'ajiyar kalumma yake,

    Na ji sarkin dawa batun da zaki ake,

    Marmara ko kashin kasa hakan nan ta ke,

    Ka ji gambun gari ashe da danki ake,

    Mai asarki uban Sunusi sarki kake,

    Dogaron ka Ubangiji abin a fake,

    Mabuwayin da gunsa dukka komai yake,

    Ga ni na zo yabon uban sarakai nake.

     

    Za ni fara da ambaton Ilahi nake,

    Makaɗaici da shi a keɓe bauta take,

    Mawadacin da gunsa dukka komai yake,

    Bani ƙarfi yabon uban sarakai na ke.

     

    Mai sarauta ta dukkanin ɗigon tsittsige,

    Ka nufe ni da jure dukka cin diddige,

    Ga magauta ka sa na zam masu kardage,

    Mabuwayi a gunka duk buƙata take

     

    Ga yabon Annabin da gunsa sirrai suke,

    Matsayai na mu'ujjiza a gunsa duka sun fake,

    Sayyadul alamina nan muƙamai suke,

    Ali wassabihi abin riƙo a fake.

     

     

     

     

     

    Attakawa hahuna a zuci take,

    Masu tsoron Ubangiji daban-ban suke,

    Masu aiki a kan sani tafarki suke,

    Ilimi damfare da masu aiki yake.

     

    Yau ƙasar Dutse za ni in yabon mai gida,

    Mai amale ɗawisu jimmina mai gada,

    Mai asarki mai kuka mai duwatsun gada-

    Yau ƙasar dutse ƙarƙashinsa komai yake.

     

    Lafiya bijimin sarakuna zakkara,

    Da fitowarka jamma'a suke kabbara,

    'Yan ma'abba suna ta jinjina kyarkyara,

    Ka zamo alfijir fitonka haske yake.

     

    Duk mayaƙi da ya fito ya sa kwalkwali,

    Ya ci sulke da gariyo ya na ƙyalƙyali

    Nuhu sarki da zikkiri yake walwali,

    Kariyarsa da dogaro ga Allah suke.

     

    Ga kurada na sassake halin biddi'a,

    Abi Allah da tsantseni a bar biddi'a,

    To ya tsafi da canfe-caffe na biddi'a,

    Nuhu horo da bin Buwayi Allah yake.

     

    Duka sarki na ƙarƙashi na Ɗanfodiyo,

    Ma'ana Fulbe mai riƙo da Ɗanfodiyo,

    Shugaba ne zaƙaƙuri abin kwaikwayo,

    Bisa tsarin mujaddadi na Allah yake,

     

    Malaminku uban garinku sarki yake,

    Jaruminku zaƙaƙurinku sarki ya ke,

    Hadiminku mataimakinku sarki yake,

    Kwatankwacin makiyayi Danfulani yake.

     

     

     

    Na karaɗe Africa inda sarki yake,

    Na ji daula ta da da yanzu yarda suke,

    Futatoro da Futajalo bando suke,

    Ya zuwa Futofodiyo Fulani suke.

     

    Ga dabi'u guda biyar a ƙirga suke,

    Yakana ga sauƙin hali a shirye suke,

    Ga sadaukin kyauta hannu a buɗe yake,

    Kana tsoron Allah kullum a rainai yake.

     

    Kuma ya zamma adali hali nai yake,

    A sarakai na yanzu gunsa tuta take,

    Ba kamar Ɗan Muhammadu nazar na tuke.

    Mai hali dubu abin yabon yabawa suke.

     

    Makasau ubangida gurin shamaki,

    Ɗan rimi da sallama suna kan taki,

    Jajirtau da ya yi hani na ɗaukar haki,

    Haɗari sa gabanka in da son ka yake.

     

    Daga Haɓe zuwa ga Shehu Ɗanfodiyo,

    Yalligawa da Jalligawa na waiwayo,

    An yi sarki kala-kala da zan waiwayo,

    Adadi sha tara na sha taran zan riƙe.

     

    Ka ji sarki Nuhu ya zo gidan sha yara,

    Haka zaure fadarsa ta zamo ƙwar tara,

    Haka hali na kyautayinsa ma sha tara,

    Sha taran arziki uban marayu yake.

     

    Na ga zaure guda tara da ba tankiya,

    Ma'ana fada inda an ka yi mulkiya,

    Ni ganau ne bare a ce a min tankiya,

    Bisa hujjar ganin ido kamar in suke.

     

     

     

    Na ga zauren naɗi na hakimai ba riya,

    Daga nan in a kai naɗi a kai tamkiya,

    Sai ko faɗa ta rantsuwa da doka biya,

    Inda sarki yake wa hakimi rantsiya,

    A biya massu yarda al'amarri yake.

     

    Na ga zaure zauren duhu da ba zullumi,

    Inda sarki yake zaman karatu ƙwami,

    Na ga zauren zaman ubanmu kuma malami,

    Inda 'ya'yan sarki suke zama sui ƙwami

     

    Na ga zaure zauren ta'ammalin jangali,

    Mai taga a can sama ta saka jangali,

    Na ga zaure da ke da hotunan jaddawali,

    Na sarakan da sukka mulki dutse cike.

     

    Maguzawa da Yalligawa an firfitar,

    Jalligawa da rukkunin an fitar,

    Na ga hoto na Makuri da Gwajabo tar,

    Ai kamar kai kira su amsa hoton yake.

     

    Jalligawa Fulani ke gwadi assali,

    Na ga sali da musa bello 'yan assali,

    Yalligawa ko Hausa ke gwadi assali,

    Ibrahim Irema Abdukadir ci ke.

     

    Ibrahim na biyu Abdulkadir na biyu,

    Abdulkadiri na uku aban na biyu,

    Daga nan Halidu ya karbi tuta biyu,

    Daga zankon nasara nan abin yattuke.

     

    Hamida Abdullahi Bello sai mai Kano,

    Sulemanu Dutse Majje ne mai Kano,

    Dutse Maje Hotoro mai darajja a Kano,

    Lokacin rimi yayyi darraja ta tuke.

     

     

    Sai Muhammad Sunusi yaz zamo maliya,

    Dotti mai kyan hali gadon Nuhu maliya,

    Daga shi sai zaƙaƙuri Nuhu maliya,

    Ya ɗare karraga mahassada na tuke.

     

    Makasau bakin cikin maga hassada,

    Lamarinka Ubangiji da nurul huda,

    Masu kishin Ubangiji da ba za'ida,

    Lamarinsu gaban gaba a kullum ya ke.

     

    Kar ku manta ina batu a kan zauruka,

    Inda sarki yake ta sussuka yai daka,

    Ma'ana kansa sha'ani akan mallaka,

    Na tafikar da zarrafin sarauta ya ke.

     

    Na ga office na mai gida uban masu gida,

    Personal ofishi na mai gida a gida,

    Na ga zauren maraba mai kamar wanni gida,

    Fada sai ɗan Muhammadu Sanasi take.

     

    Gwargwadon martaba da addadi ne ake,

    Sauke baƙi a fada inda mulki yake,

    Na ga fadar da nats tsaya na yo kassake,

    Ta'ajibi na kyau da yarda tsari yake.

     

    Na ga fadar da shugaban ƙasa yass shigo,

    Na ga taron na ‘yan siyasa ma sun shigo,

    Na ga falo na 'yan majalisa in figo,

    Na ga filin hawa da daba kai ya tuƙe.

     

    Na tuno sha'ani na ba da zakka kuma,

    Makasau ka issa jinjina ak kuma,

    Yarda tsarin yake na gunduma-gunduma,

    Ko sarakai na dutse kun ga zagga yake.

     

     

     

    Ga shirinsa na ijtihadi bai son faɗi,

    Mu ko’in mun sani ya zamma wajib faɗi,

    Manufarmu a samu masu ko yi daɗi,

    Kwaikwayo mai halin yabo da lada yake.

     

    Inda ba kwa zato Nuhu yana bibiya,

    Musuluntar da Maguzawa ba karraya,

    Zuri'ar Niger Dalta na gidan Maliya,

    Musulunci ya sa su ba musu hakka yake.

    Sha'aninka abin yabo da koyi yake,

    Mai sulke da kwalkwali uban mai kuge,

    Na yaba ka mai taguwa uban mai nage,

    Allah kawo rabo na saduwa ni da kai.

     

    Ƙasaita ta sa nake yabon ka Nuhu,

    Cancanta ta sa yabon gwanina Nuhu,

    Mai kyauta ya ma daɗi da ƙarin buhu,

    Bari in zana yadda dai sarautar take.

     

    Ƙarƙashin Dutse kwai garuruwa har bakwai,

    Gundumomi a ƙarƙashin garin nan bakwai,

    Ashirin da takwas cikin garurra bakwai,

    Duka mulkinsu ƙarƙashi na sarki ya ke.

     

    Bari in zana ginshiƙan garurra bakwai,

    Da suke ƙarƙashin uban sarakai bakwai,

    Dutse kanta Dutse gadawur na 'yan bakwai,

    Ga Gwaram Buji ga Kiyawa na 'yan bakwai,

    Miga birnin Kudu Jahun cikin ƙwar bakwai,

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.