Ticker

6/recent/ticker-posts

Zazzau

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Jinjimin gari Zazzau,

Mai Sarakunan baiwa,

Zazzau garin bakwa,

Mai sarakunan baiwa.

 

Ya Huwallazi Allah mai aro a yo mulki,
Na taho da ɗan ƙoƙo ƙarfafe ni kan mulki,

Za na wassafo Zazzau ka hanan rawar baki,

Daga zamanin Bawa kan Shehu ɗan baiwa.

 

Rabbana salatinka ka daɗa gurin Manzo,

Mahmudu Manzona laƙabinsa ne Manzo,

Sanadi na bunƙasar Islama tai buzowa,

Yanzu dukkan sassa Islama ya je wa.

 

Zazzau garin Bakwa za na zana tarihi,

Na Sarakunan haɓe sittin a tarihi,

Bakwa zuwa Makau kun ji haɓe tarihi,

Ya zuwa rabon tutar Usumanu ɗan baiwa.

 

Zan taƙaita tarihin haɓen garin Zazzau,

Tsakure kawai zan yi in wuce mutan Zazzau,

Zan fi karkata lotan tutarka mai Zazzau,

Loton su Ya Musa ya zuwa ga ɗan baiwa.

 

Can baya tarihi lardin garin Zazzau,

Dausayi take yalwa ba gari kamar Zazzau,

Shi ya sa masarrautu ke zawartakar Zazzau,

Kowansu burinsa mallakar ta dan yalwa.

 

Shi ya sa Sarauniya Ƙueen Amina mai Zazzau,

Da ta zama ɗiyar Bakwa mashahuriyar Zazzau,

Tac ci ɗammarar yaƙin kare garin Zazzau,

Har zuwa fa kowarta yaƙe-yaƙe tai yowa.

 

 Kun san a tarihi Zariya garin yalwa,

Zariya suna ne na ɗiya ta Bakwa kuwa,

Ƙanwa ta Amina Ƙueen Amina ‘yar baiwa,

Zazzau takobi ne na sarautakar baiwa.

 

Za ni waiga tarihi masana ku yo aniya,

Ɗalibai ku ɗau waraƙa da ƙalam ku yo aniya,

Za na karkata Zazzau ku juyo farar aniya,

Ku ji salsalar Zazzau ku ji yo abin sha’awa.

 

Rayuwa ta tsuntsaye ta ishe ka in ka kula,

They are migrated daga ƙuddurar Allah,

Sanadin fatauci ko kiwo idan ka kula,

Ko biɗar sanin ilimi sanadin gurin haɗuwa.

 

Sanadin da na je ruwa za na ɗau baƙi in fasa,

Shi ya tarkato Mallam Ya Musa har Musa,

Abdulkarim Sarki da ya shanye daularsa,

Har da Abdulsalami ɓangaren Sulluɓawa.

 

Za ni bi da bi in kasa rukunin masarautu,

Farko da Mallawa za na busa algaitu,

In kira yi Mallam Musa da baituka da batu,

Ƙarƙashinsa in jero Masarauta Mallawa.

 

Malami taƙiyi ne masani da addini,

Masani na fanni da ulum na Ƙur’ani,

A alif ɗari takwas da huɗu ta can ƙarni,

Shi ya karɓi tutar Sheik Usumanu ɗan baiwa.

 

Shi da Abdulkadir na cikinsu Mallawa,

Ƙa’imin Saraki ne a cikinsu Mallawa,

Martabarsa ta zarce wallafa da waƙewa,

Ga na fari ga na shida a sarakunan baiwa.

 

 

 

Sai Abubakar na tara a mamallakan baiwa,

Haka zabamallene malle babu gogewa,

A alif takwas da bakwai ne ya sha ya mulkawa,

Haziƙi abin ƙauna ya yi babu gantsarwa.

 

Sai Aliyu Ɗan Sidi a alif tara da uku,

Rukuni na jeranyar mulki na sha uku,

Dattijo Ɗan Sidi jarimin da ba na uku,

Na rufe gidan Malle da saraku Mallewa.

 

Sai kason gidan Barno Sarki fa Ya Musa,

Ya Musa Mallam ne masani gwanin sassa,

Shi ya zamto na biyu daga Musa Ya Musa,

Mai wakiltakar Barno ɗan Babarbarin baiwa.

 

A cikin sahun ƙirge lisahi cikin ƙa’ida,

Sarki kashi na huɗu Abdullah Hammada,

A barebari yake shi Abdullahi Hammada,

Jarimin Sarakoki ya yi ya kuma yowa.

 

Daga nan ko sai Mamman Sani az zubi na biyar,

Shi ya karɓi Hammada lamba four da lamba biyar,

Ya ɗare gadon mulki a cikin wata na biyar,

A barebarin Sarki yake kar ku mantawa.

 

Daga nan fa Abdullahi ya zamo uban tafiya,

Shekara alif da takwas da biyar bawkai ka jiya,

Na takwas a jeranyar haziƙan sara ku jiya,

A sahun mutan Barno yake kar ku mantawa.

 

Za na waiwayo Sarki Ru na cikon sha ɗaya,

Daga yeru sai Kwasau sha biyu daga sha ɗaya,

Shekara biyar Kwasau ya yi ba ɗigo na ɗaya,

A mamallakan Zazzau a barebarin baiwa.

 

 

 

 

A alif ɗari da tara nineteen twenty year,

Ɗalhatu ne Sarki in a kai ma tambaya,

Na ciko a lissafi goma sha huɗu na biya,

A barebari kumawa har wayau karantowa.

 

A alif ɗari da tara ashirin da huɗɗu kuma,

Sarki na sha biyar kuma Ibbirahima,

Shi ya karɓi Ɗalhatu M. Ibirahima,

Daga shi na sha shida ma duk Babarbare aka wa.

 

Shekara alif da tara da salasa was saba’a,

Ja’afaru Ɗan Isiyaku saman ka sa rufu’a,

Murfin gidan Barno akai masa bai’a,

Sarki na sha shida ne Ja’afaru Ɗan baiwa.

 

Za ni je gidan Katsina a sarakunan Zazzau,

Abdulkarim Sarki na uku gidan Zazzau,

Abdussalamu kuma na bakwai garin Zazzau,

Shi Basulluɓe ne Abdussalamu ɗan baiwa.

 

A gida kashi na huɗu rukunin Sulluɓawa,

Ma’ana ta Sulluɓawa ina nufin Sakkwatawa,

Abdussalmu kaɗai shi akai wa mulkawa,

Shi kaɗai ya zam Sarki rukunin Sulluɓawa.

 

Za na ƙarashe ƙirge na sarakunan Katsina,

Baya kun ji Mallawa Sulluɓawa ga Katsina,

Kun jiyo Barebari ma yanzu sai mu je Katsina,

Abdulkarim Sarki ku mu je in ɗorawa.

 

Ku ji sarki na goma ya fito gidan Katsina,

Martabarka dai Sambo darajar gidan Katsina,

Sai Muhammadu Aminu har wayau gidan Katsina,

Sarki na sha bakwai ALA Saini Ɗan baiwa.

 

 

Sarki na sha takwas rukunin gidan Katsina,

Ga cikamakin Sarki da na sa a waƙena,

Murfi na tarihi da ya zo a waƙena,

Shehu Iddiris Zazzau ALA raini san kowa.

 

Marmara ka faɗawa a rugurguje baba,

Haka nan a faɗa ma ba a sha da daɗi ba,

Girgije alum na ruwa takenka ne baba,

Inuwa gurin bayi ga marar uba baba,

Shehu Iddiris Zazzau gangaren garemu uba,

Allah raini mai Zazzau shugaba majamu gaba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments