Ticker

6/recent/ticker-posts

Jabbama Marafa Abubakar

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

Allah ya riƙa maka,

Allah ya taya maka,

Jaɓɓama na ce maka,

Turmi ka ke sha daka,

Tirmin luguden daka,

Hatsi sha sussuka,

Gamji sha sassaƙa,

Bai'a aka ma duka,

Ba wanda ya ja maka,

Yau ga ni da baituka,

Marafa a kai maka.

Marafa Abubakar Allah ya yi maka ɗaukaka.

 

Amshi

Marafa abubakar na zo nake yi wa tambura,

Jaɓɓama Abubakar Habu Marafa garin Kano.

 

Rabbun nasi mai duka wajenka nika zuwa bara,

Mai ba ni a duniya shi ne zai ba ni a lahira,

Mulkinsa daban yake Allahn da na yi wa kabbara,

Allahu abin riƙo wajensa ne muka tattara.

 

Allah daɗa darraja wajen Habibu madogara,

Wannan da mu kai riƙo da sunna tai muka dogara,

Ɗan Abdu majingina ga tsani gunsa na tokara,

Ƙauna ta zamar mani hujja ranar tsayuwar jira.

 

A yau tuna baya zan yabon ubanmu a nan Kano,

Allah ya jiƙan maza Allah jiƙan Marafan Kano,

Allah ya riƙan Habu wanne? Na yau Marafan Kano,

Gurbin na ubanmu ne Habu a kanka ta mirgino.

 

 

 

 

Mafara a nan Kano na fari sai Sule Minjibir,

Marafa garin Kano na biyu ɗan Sule Minjibir,

Bara in yi waiwaye ado na mai tafiya zubur,

In waiwayi talifin Marafa ɗan Sule Munjibir.

 

Marafa sarautaka a Sokkoto aka yo aro,

Marafa a Sokoto ba a naɗa ta ga makkwaro,

Marafa sarautaka ba a naɗa wa madankaro,

Sai ɗan babban gida ake naɗa masa kwarkwaro.

 

Shekaru casa'in da bakwai akai Marafa a Sokoto,

Tun alif da ɗari tara ashirin Marafa a Sokoto,

Mu alif da ɗari tara da sittin ta zo daga Sokoto,

Shekaru hamsin da huɗu a nan Kano daga Sokoto.

 

Habu Sule Minjibir da naj ji za a naɗi Kano,

Cikin rukunin naɗi cikinsu har Marafan Kano,

Sai nai kasaƙe na ji wa an ka ba Marafan Kano,

Domin na yi binciken hujjar naɗin Marafan Kano.

 

Habu Sule Minjibir ta faɗa kan Marafan Kano,

Da naj ji batun haka sai nai caffa ga uban Kano,

Sara ya yi kan gaɓa Habu Sule Marafan Kano,

Dukkan rukunai cicif sun hau Habu Marafan Kano.

 

Sai ɗan babban gida ake yi wa Marafan Kano,

Sai mai tsarkin hali ake yi wa Marafan Kano,

Sannan ƙasurgumi ake bai wa Marafan Kano,

Mai tausan jamma'a yake zama Marafan Kano,

 

Mai tanyon jamma’a ake saka Marafan Kano,

Jajirtaccen maza yake zama Marafan Kano.

Gawurtaccen maza ake yiwa Marafan Kano,

Habu Sule Minjibir ka cancanta Marafan Kano.

 

 

 

Farko daga assali Habu ka kai maƙurar yabo,

Jini na sarautakar sarkin Fulani abin yabo,

Ayuba uban maza kakan Abu Sule sha yabo,

Sarki Sulemanu ne ya ba shi kun ji abin yabo.

 

Marafa Abubakar fannin sanin ilimi kuma,

Jaɓɓama Abubakar harɗo ka zarci fa gardama,

Harɓard uniɓasity ka je ka sami wajen zama,

Dakta aka ba ka can fannin sanin sana'u kuma.

 

Landon da su Jamani ka je ƙarin ilimi kuma,

Ka sam gindin zama gogayya ka yi ta haƙƙima,

Oil, and gass a can ka san makamarsu kuma,

Harkar inɓestment hada-hadar jalli kuma.

 

Kafin haka nan a Rimi City yay yi furamare,

Barewa Kwaleji can Habu ya yi ta ya ƙarƙare,

BUK nan Kano Habu ya yi ta ya ƙarƙare,

Sannan uniɓersity Abuja ya yi ya ƙarƙare.

 

School of Managment Kellogg Habu ya yi ya dire,

Chikago America Habu ya je shi fa ya ƙware,

Oɗford Uniɓasity London Marafa ya ƙarƙare,

Ya san ilimin hagun ya san na dama badagire.

 

Fagen hidimar ƙasa Abu Marafa fa ya ƙure,

Zango na mu'amilla Habu Marafa ba tsambare,

Aikinsa fa bai faɗo yawan ya kai na ruwan dare,

San nan gaba za ni zo da ayyukansa a yo kure.

 

Allah ya jiƙan maza Sule Marafa na gun Habu,

Allah ya jiƙan maza wakili Abba na gun Habu,

Yaya a gurin Habu wakili Abba maso Habu,

Allah daɗa rahhama a kabbarinsu jinin Habu.

 

 

Na gai da uban ƙasa limami mai malafar Kano,

Sarkin mai taguwa sanusi na biyu mai Kano,

Naɗin da ka wa Habu wannan naɗi Marafan Kano,

Allah ya daɗo maku ƙauna da son jama'ar Kano.

 

Zan gai da shaƙiƙanai na gu Habu Marafan Kano,

Baaba darman sahu na fari ni fa na zayyano,

Baaba darman a yau Habu shi ne Marafan Kano,

Murna na taya ku ni Aminu ALA garin Kano.

 

Da ɗan Isan Kano cikin sahu Marafan Kano,

Cikinsu abokanai nasa ɗan Isa na nan Kano,

Murna na taho maku Habu shi ne Marafan Kano,

Allah ya riƙa masa Allah ya armasa ɗanɗano.

 

Captain Ado na sa Ado karaye a yabo,

Captain pilot ina taya ku murna da yo yabo,

Malam Nasir Gumel ALA ne ke baitin yabo,

Murna ta Abubakar Abu Marafa abin yabo.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments