Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarakunan Fulani

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Ta dabo garin baiwa saraki ba ay ya Kanawa ba,

Sarakunan fulani za na ƙidaya su ba da wai-wai ba.

 

Shimfiɗa

Kano gari na masu albarka,

Cibiya ta masu yin harka,

Ko dame ka zo fa an fi ka,

Sarauta ka zo a nushe ka,

Mulki ka zo a nushe ka,

Taho ka ga garin waliyanka,

Taho Kano garin sharifanka,

Gari na malamai na son barka,

Kai wannan gari da albarka,

Tadabo garin baiwa, saraki ba ai ya Kanawa ba.

 

Allah huwallazi rahamanu mai mulkimmu ba da cuta ba,

Gun Ka na roƙi ilhama zan waƙe Kano garin daba,

Kai mun gudunmawar ƙarko ya zamma in yi bada rauni ba.

 

Allah daɗo salati dubu-dubun da ba ka yi wa ƙaidi ba,

Ga mursalin mutum da ba kay yi kammarsa a gun adala ba,

Muhammadur Rasulullah nai tsani da son ka ɗan babba.

 

Zan tattago bayanin sarakunan Fulani ba da wai-wai ba,

Tun daga zamanin sarki Sulaimanu ba da nuna ƙwauro ba,

Har zuwa gurin Ado sarki mai halinka ba ay yi ba.

 

Farko mujaddadad dina Usmanu Fodiyo maƙi gaba,

Shi ya tura sarakai gari-gari irinsu mai hali babba,

Sarkin Kano Sulaiman aka ba mu ku ji ba da ƙarya ba.

Sarkin da ke zama bisa karagar mulkinsa ba da wasa ba,

Sai zai yi shari’a ko kwatankwacinta ba da nuna girma ba,

Haziƙin sarki taƙiyi fa ba shaƙiyi ba.

 

Na biyu sarki Dabo mai sa maza gudu mazan gaba,

Shi ya raraki Ɗambatta Ɗantunku har ya kai su can gabba,

Lokacinsa sarautar Kano ta tsayu ba ta sake rauni ba.

 

Lokacin da akai naɗin sarki Dabo anka mai bai’a,

Wani yardajjen Allah yaz zo gare shi don ya mai bai’a,

Daga nan ne busharar fallalarsa ba da nuna ƙwauro ba.

 

Na uku Usmanu mai tausayi ɗa a gurin Dabo,

Mai laƙabi Maje-Ringim mai jin ƙan jinin Kanon Dabo,

Ranar da yai wafatinsa Kano ba wanda bai yi kuka ba.

 

Na huɗu Abdullahi mai arziƙi da kwarjinin girma,

Lokacinsa hukunci an yanke wa fajirai da ‘yan nema,

Albarkacinsa ne fa ake cewa Ado mai Kanon daba.

 

Sarki Bello karimi ne haziƙ mai ilim na addini,

Mai yawan roƙon Allah mai taƙƙawa kishi na addini,

Shi a kaiwa ishara tun bai hau ba don isa gurin daba.

 

Sarki Tukur fa jarunta tas sa aka naɗa shi sarkinmu,

Lokacin da ya taushi mutan argungu sai yaz zama linjamu,

A karo na artabu argungu sun ji ba da daɗi ba.

Ga jinjina ga gumbar dutse,

Mai horo da dunƙulen dantse,

Kauce maza kar a yi ma sartse,

Mutun guda jiran dubun dantse,

Kauce wa sababi maza ratse,

Idan Tukur ya cika ya batse,

Arnaku za fa su sha rotse,

Awartaki masassaƙin dantse,

Gashin ƙuma ka fi gaban rotse,

Ta dabo garin baiwa saraki ba ai ya kanawa ba.

 

Sarki Alu mazam fama namijin duniya fa mai sango,

Mai takubba mai masu mai bindiga riƙonki ya fi rago,

Mai ɗamara ta fama a lokacinsa ba ai mana wargi ba.

Sarkin Kanonmu Abbasu sarki na takwas fagen ƙirga,

Makamin yankan bidi'a mai zabgawa fasiƙai tsabga,

Lokacin da akai basasa karon batta ba da daɗi ba.

 

Shi ya dinga biyan diyar rayukkan da anka rassa su,

Da masu raunika mata waɗanda suka rassa mazzansu,

Sabaucin alkairi mai tausai ba za ya taɓe ba.

 

Sarkin Kanonmu Usmanu na biyu datti mai halin girma,

Lokacinsa akai famfo assibiti abin nema,

Ɗan Datti uban Datti ba kac ci amanar Kanawa ba.

 

Sarki Bayero mai alfarma gangaran a sarakoki,

Shi ya yalwata majalisar fada wacce ke a gaban sarki,

An samu ci gaba da yawan da ba zai yiwu in kwatanto ba.

 

Sarki Sunusi mai shajja’a hadari ba a yi ma shinge,

Basaraken sarki mai haiba da kwarjini maƙi shege,

Cida ratsa kunnuwan kurma mai sukarka bai ji daɗi ba.

 

Sarki Innuwa mai alkunya mai haƙuri irin baiwa,

Sari mai tawari'u mai yakana ɗa’a a halin baiwa,

Mushtahidin sarki abin so da soyuwa baba.

 

Hadari malafar sarari gwanki mai fasa ka zai kuje,

Dare mahutar bayi mayanki haƙuƙuwa lauje,

Uwa ma ba ɗiya mama mai ƙaunarka bai asara ba.

 

Ado Bayaro sarki a zamanin ga ba a yi kama tai ba,

Arewa da kudancin ƙasarmu kaf ban ga mai kama tai ba,

Ado da kwarjinin mulki a nahiyar ga ba kamar shi ba.

Majingina madogarar bayi,

Allah ya zo da guguwar sauyi,

Ya ba mu wanda ba shi yin shayi,

Mai ilimi wanda ake yayi,

Mai mulki cikin ruwan sanyi,

Ado mafi sani na fannoni,

Mai yin gudunmawa ga addini,

Mai ƙin ka na kira shi shaiɗani,

Koko in ambatai da majnuni,

Ta dabo garin baiwa saraki ba ai ya Kanawa ba.

 

Zan dakata nasa aya wataran sai sarakunan Haɓe,

Za ku ji ni da tarihin ƙofofin Kano a kekkeɓe,

Almajirinku ne ALA na Tudun Murtala gari babba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments