Ticker

6/recent/ticker-posts

Takawa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Mai Martaba ɗan Bayero farin gani,

San Kano takawa sannu-sannu dai,

Lafiya ɗan Abdallah adon gani.

 

Ubangiji Ahadun Assamadun ɗaya,

Abin yiwa bauta shi shi ɗaya,

Wahidun da ya yo mu a gari ɗaya,

Mu ke bikin al'adarmu fa baiɗaya,

Bikin sallah, ta Kano ba ta da kishiya,

Godiya muka fito yi maka baiɗaya,

Kasa mu sake riskar baɗi baiɗaya,

Ka amsa addu’o’inmu tamkar walƙiya,

Wahidun Assamadun Sarki ɗaya.

 

Jajiberi na zuwan sallah 'yan uwa,

Taho Kano ka ga ɗoki gun 'yan uwa,

Ɗinkunan alfarma ga mafi yawa,

Raguna, ga kaji don soyuwa,

Yara mata na ƙunshi don karɓuwa,

Yara-yara na tsalle don ɗimuwa,

Gobe za su su gano sarki zai hawa,

San Kano ɗan Bayero uban ƙawa,

San Kano ɗan Bayero uban ƙawa.

 

Gari ba Kano ba, dajin Allah buwayi ne,

Sallar Kano za ni furta ku ji yanzu ne,

Da bikin sallar sarki ku ji yanzu ne,

Da hawan sallar sarki ku ji yanzu ne,

Da adon alfarmar sarki ku ji yanzu ne,

Da zubin mulkin sarki ku ji yanzu ne,

Tsarin tafiyar sarki ku ji yanzu ne,

Dakaru na gaban sarki ku ji yanzu ne,

Dakarun bayan sarki ku ji yanzu ne,

Babbar giwar sarki ku ji yanzu ne,

Duk duniya ALA na yanyane,

Ba mai irin sautar sarkinmu ne.

 

Ɗan Bayero Kanawa tafi sannu dai,

Ɗaukawa a hankali sannu-sannu dai.

 

Ranar ɗaya ga sallah, nac ci adon ƙawa,

Ina ta rawar jikin zuwa bautar mai kowa,

Ana ta hada-hada kowa na kai komowa,

Kano ta yi cikar kwari ta cika ta batsewa,

Ina tafiya ina hailala zikiri kuwa,

Ina azamar in risko, kuɗuba 'yan uwa,

Akai sallah da ni zukatanmu da nuttsuwa,

Da anka idar na garzaya don na yi gaisuwa,

Ga San Kano ɗan Bayero uban kowa.

 

Daga can na ji tambari na harbawar bindiga,

Sai na ji tambura na sarki mai bindiga,

Sannu dodo maganin 'yar bakar daga,

Hakimi na sarki guda in har ka ga,

Ya yiwo shigar fitar sallah ba batun ziga,

Daidai yake da sarkin wata nahiya ka ga,

Rundunarsa rundunar sarki goma ga,

Ka gano sarakuna sun koma ya diddiga,

Ɗan Bayero yana gun babu batun ziga.

 

Hakimai na tsarin hawan sarki Maikano,

Na gaban gaba a sahun tafiyarsa Maikano,

Makaman Kano,

Dallatun Kano,

Sarkin Dawaki mai tuta, walin Kano,

Matawallen Kano,

Makaman gado da masu, sarkin Bankano,

Ga fagacin Kano,

Madakin Kano,

Ɗan Majen Kano,

Ɗan kaden Kano, Magajin Malam Kano,

Magajin Rafin Kano,

Ɗan Madamin Kano,

Ga Falaƙin Kano,

Ga Sa'in Kano,

Ga Sarkin Rano, Sarkin Gaya ta jihar Kano,

Sarkin Fadar Ja'idanawa na jihar Kano,

Mai Unguwa ta Mundubawa ta Jihar Kano,

Marafa na Kano,

Ga Durbin Kano,

Sarkin Fadan Kano,

Sarkin Yaƙin Kano,

Bunun Kano,

Katuƙan Kano,

Jarman Kano,

Ɓarayan Kano,

Talban Kano,

Uban Doman Kano,

Ga Ajiyan Kano,

Maji Daɗin Kano,

Zannan Kano, Ma'ajin Watarin Kano,

'Yan Dakan Kano,

Kaigaman Kano,

Kacallan Kano,

Barden Kano,

Ga Ɗan Iyan Kano.

 

Sansanin tafiyar sarki a gaban gaba,

Kowa ya yi shigar alfarma yai gaba,

La Haula wala ƙuwata na ce a gaba,

Na gano sansanin giwar sarki a gaba,

Na gano giwar sarkin Kano uba,

Na hango rumfar masun mai martaba,

Ɗan Bayero da al'ummar mai martaba,

Mai tambura mai tagwayen masu uba,

Ɗan sarki Alhaji Allah dai ya ja gaba.

 

 

Jama'a suna ta hanƙoro ambaliya,

Wasu na faɗin Allah ƙara maka lafiya,

Ga 'yan lufudi a jere suna ta tafiya,

Ga ‘yan sulke a jere suna ta taffiya,

Ga dogarawa na doki na taffiya,

Mai tafari da 'yan baka sun yiwo aniya,

Sai taguwa da ɗa na gabanta na tsinkaya,

Ga alfadari na sarki mara turjiya,

Sannan zagage na sarki babu nokiya.

 

Zagagen tsakiya dozin sha biyu ne,

Hagunsa dama 'yan kagira dogarai ne,

Sai uban tafiya takawa sannu ne,

Damansa Shamaki da Ciroman Shamaki ne,

Da Turaki Shamaki Madakin Shamaki ne,

Ƙarshe na sa jakadan garko cikinsu ne,

Hannun hagu makaman ɗan riminmu ne,

Sarkin hatsi madawakin ɗan rimi ne,

Sannan turaki na ɗan rimi ku gagga ne.

 

Bayansa sallama da kilishi adon gani,

Da galadima na sallama mai adon gani,

Ƙarƙashin dawaki na zage sha biyu na gani,

Na gano majasiddi, malafa mai kyan gani,

Ga 'ya'yansa da jikoki armashin gani,

Duk duniya ban ga sarki na azo a gani,

Mai ɗammara da tsari mai isa da kwarjini,

Da ya kai kwatankwacin takawa farin jini,

Da zubi da tsaruwar mulki na a zo a gani,

Sansanin bayan giwarsa za ni wassafa.

 

Wazirin Kano,

Galadiman Kano,

Haɗa Wamban Kano,

Chiroma na Kano,

Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Turakin Kano,

Sarkin Shanun Kano,

Da Tafidan Kano,

Da Ɗanburan Kano,

Da Ɗan Isan Kano, da Ɗan Lawan ɗin Kano,

Barde Kerarriya, Magajin Garin Kano,

Ɗan Amar ɗin Kano,

Da Ɗan Makwayon Kano,

Dokajin Kano,

Ɗan Darman Kano, ɗan Ruwatan Kano,

Haɗa Ɓauran Kano,

Da Yariman Kano,

San Turakin Kano,

Ɗan Malikin Kano,

Sarkin Ƙarayen Kano.

 

Ado ka zama garkuwa, bakan dabo abin yabo,

Ubangijin Shamaki, da Ɗanrimi abin yabo,

Ubangijin sallama da kilishi abin yabo,

Ubangiji na sarkin dogarai ka sam rabo,

Ubangijin makaman ɗan rimi abin yabo,

Ubangijin maja siddi babban zagi mai rabo,

Ubangijin ciroman shamaki babban rabo,

Ubangijin na sarkin mota abin ai yabo,

Ubangijin na ɗan mori nake yiwa yabo.

 

Hawan Nassarawa ba za ku ji yanzu ba,

Hawan Daushen Sarki ba za ku ji yanzu ba,

Hawan Fanisau fa ba za a ji yanzu ba,

Hawanmu na Ɗorayi ba zan sheƙo yanzu ba,

Dalilin yin su zan karanto ba yanzu ba,

Asalin yinsu zan karanto ba yanzu ba,

Alan Kano na Kano ba baƙonku ba,

Ɗan jiha ta Kano ba alfahari ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments