Ticker

6/recent/ticker-posts

Chiroma Nasiru Ado Bayero

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Chiroma Nasiru Ado Bayero zaɓina,

Jikan Dabo Allah ya ida muradin mai ƙauna

 

Rabbu Ubangiji Mabuwayi gagara mai koyo,

Agaji bawanka mai manufar koyi ko koyo,

Kai mani baiwarka kar ka bari ta yi man yoyo,

Za ni yabon saraki Nasiru Ado zaɓina.

 

Rabbu Ubangiji Masarauci ƙara amincinka,

Gunsa masoyinka annabi Ɗahiru bawanka,

Limamin ma'aika wanda ya ida risalarka,

Annabi manzona son sa ya zam mani tsanina.

 

Kan ilimin dama Nasiru ba shi ƙasar gwuiwa,

Yai ilimin Allah alfannanu jinin baiwa,

Kan ilimin hauni yai ilimin low ɗan baiwa

Mastas ya karke can a Amurka abin so na.

 

Ƙasar Sudanawa koko na ce Iffirikiyya,

Biladis Sudan kaf ban rage ko wacce alƙarya,

Ban ji ba ban gani ba kafatani na mulukiyya,

Hamshaƙin saraki tamkar Nasiru gagona.

 

Na yi baƙin ciki da rashi na madubin alƙaryu,

Dakta Ado Bayero na kira da madubin alkaryu,

Na yi farin ciki da gamo da magajin mai tanyu,

Chiroma garin Kano haji Nasiru Ado zaɓina.

 

In na kallaci Nasiru sai ƙwaƙwalwata ta yi kirdado,

Hotuna na uban gayya mai Kano shi taka kirdado,

Wani ga shi jikin turare Nasiru ya yi kama da Ado,

Taka sannu farin masoyi a kwana a tashi ishe haƙona.

 

 

Tafi da tafashen sarki ya yi tafi da Kanon Dabo,

Tiraki turakar sarki ya yi turaki Kanon Dabo,

Tangori uban ‘yan sarki ga shi chiroma Kanon Dabo,

Kira shi damin rumbu mai duka ida muradina.

 

Na ji wajen manya sunka faɗi da yana yaro,

Kamun kan chiroma da nutsuwarsa yana yaro,

Ya gwada waye shi an ga hakan fa yana yaro,

Kun ji damin rubbu angon Ilham jigona.

 

Nasiru alkunya ga yakana da badangalci,

Yana da kawaici kau ga ko tawali'u mai ‘yanci,

Mai haƙuri chiroma ba shi gwada maka ninanci,

Ga shi tsayayye kau Nasiru na da halin ƙauna.

 

Gashi amintacce an shaida da amincinsa,

Mai Kano ya shaida mu ma mun yaba halinsa,

Ga ko zaƙaƙurci ga nutsuwa da amanarsa,

Uba ga Muhammad Nasir ne chiroma gagona.

 

Mai nasara Nasir baban Nasiru mai gayya,

Tun daga sunanka Nasiru kaz zama ja gayya,

Ɗan Adam baba, baban Adamu mai gayya,

Ƙara taki saraki mai duka ya ji du'a'ina.

 

Allah ya hukkumu sa'a chiroma Allah ya dafa ma,

Alan waƙa ne naka na ajiya mai girma,

Ajiyan chiroma Alhaji Haruna mai himma,

Ga fa wulayarmu Nasiru don tsantsar ƙauna.

 

Sannu uwar maƙera Ilham Nasiru mai girma,

Alkyabbar mata kin yi abin a yaba ke ma,

Ga fa tukuicina don yaba kyautar alfarma,

Kan waƙar chiroma Nasiru mai komai ƙauna.

 

Rabbu Ubangiji Mawadaci kai baiwa jingim,

Kan harshe nawa da ta hanani zaman jingum,

Ƙarfafi baiwar nan kad da na zam kamar dinkim,

Na yi yabon masoyi Nasiru adon sarkina.

 

Tangori uban ‘yan sarki,

Turaki turakar sarki,

Tafida tafashen sarki.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments