Bargu Kingdom

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi 1

    A rukunin tarihi zan yabi Bargu Kingdom,

    Ga masarautar Bargu mai asalin tarihi,

     

    Amshi 2

    Yau masarautar Bargu ta naÉ—a jikan toro,

    Attahiru Abdulrazak anka wa bunun Bargu.

     

    Ya Ahadun mai iko ban fikira Jallallah,

    Kai mini ƙaimin fusuha da hikima ya Allah,

    Kan sha'ani na hikima kar ka yi man talala,

    Kar ka shikan linzami in biye ruÉ—un daula,

    Duk rikicin zamani kar na bi zaukin daula.

     

    Na yi yabon manzonka annabi mai kishin ka,

    Mai haƙuri ɗan Abdu wanda ya kai saƙonka,

    Mai nasara Ahamadu jagoran bayinka,

    Mai daraja mai falala wanda yake begen ka,

    Ali da sahbu na sanya wanda suke kishin ka.

     

    Zan yi adon mai tafiya kan sha'anin tarihi,

    Mai tafiya adon tafiya dakaci waiwayi tarihi,

    Mai asali shi ka faÉ—i shi ka tsumin tarihi,

    Yau masarautar Bargu za ni biyo tarihi,

    Zo ka ji tarihi mai sa nutsuwar arwahi.

     

    Tun a sabintin tati za ni na zano Bargu,

    Tun Kisira sarkin nan ne sanadiyyar Bargu,

    Wanda zuwan Islama ce sanadiyyar Bargu,

    Da rugujewar Kisira daular Sham sai Bargu,

    Kisiru Burodin nan za ni na kawo Bargu.

     

     

    Sanda ma'aikin Allah yai masu saƙon zance,

    Kan Islam addinin Allah babban zance,

    Sanda matsi yay yi matsi sai Kisiru ya arce,

    Yab bi ruwan Africa don Islam ta yi fice,

    Kun ji silar ‘yan Bargu za ku ji sauran zance.

     

    Da ya gudu sai aka ce annabi yai mai zance,

    Ka gudu don ƙin Allah za ka ji ƙarshen zance,

    Duk zuri'a ta Kisiru za su shigo a huce,

    Don Musulunci za sui ba wanda zai kafurce,

    Don haka dukkan Bargu babu guda kafirce.

     

    Za ni zubo tarihi na masarautar Bargu,

    Daga sabintin tati masu sarautar Bargu,

    Kawo zuwa tu'osabin tin masarautun Bargu,

    Daga sabintin tati sarkin mazajen Bargu,

    Kiseru Burodi ne a karagar mai Bargu,

     

    Har ya sabintin fifti yake sarautar Bargu,

    Daga sabintin fifti ne masarautar Bargu,

    Yarima busa sarki É—an Kisero mai Bargu,

    Daga sabintin siÉ— siÉ— ne Kigera mai Bargu,

    Ɗan Kiseru ne na biyu ya riƙe mulkin Bargu,

     

    Daga sabintin nine one ne Jibirin mai Bargu,

    ÆŠan gun yarima Jibirin Busa sarakin Bargu,

    Sai a sabintin nine two yarima IB Bargu.

    Yarima Ibrahimu É—an Jibirin mai Bargu,

    Shi ya riƙe tun daga nan Kitoro Garil mai Bargu,

     

    Shi ya yi gado na yarima a karagar mai Bargu,

    A eating tati fayib ya zama sarkin Bargu,

    Beraki Eating Fofo É—an Jibirin mai Bargu,

    Waruko É—an mai kuka Eating siÉ— two Bargu,

    Kigera na biyu É—an Jibirin É—an toro É—an Bargu,

     

     

    Shi ko a eighteen nine fiÉ“e ya zama sarkin Bargu,

    Ya kai ninetin o tree a ragama ta Bargu,

    Sai Wuru yaro Kisaru, kisan dogo, É—an Kitoro,

    Shi ya É—are kan ragama ninetin o tree Bargu,

    Har ya zuwa ninetin fiftin a karagar ‘yan Bargu.

     

    Kitoro gani kilishi yarima ne É—an toro,

    Shi ya haye kan karagar yai sarkin ‘yan Bargu,

    Tun daga ninetin fiftin yai sha tara mai Bargu,

    Sai Jibrin É—an toro, ninetin twenty four Bargu,

    Sha huÉ—u yai kan karaga yana ta sarautar Bargu.

     

    Ninetin thirty fiÉ“e Mamman Kitoro Gani Kilishi,

    Kitoro Gani Kilishi yarima sarkin Bargu,

    Ninetin fifty four Wuru Babaki ÆŠantoro mai Bargu,

    Ninetin siÉ—ty eaght Muhammadu Sani a sarkin Bargu,

    Two thounsand Musa Muh’d Kigera na uku mai Bargu,

     

    Sai kuma two thausand fiftin Halliru ne ÆŠantoro,

    Kitoro na III yai sarki a karaga ta Bargu,

    To daga nan sai Mamman Sani Kitoro na II,

    ÆŠan Halliru Dantoro shi ka sarautar Bargu,

    Mai daraja mai nasaba,

    Allah riƙa Bargu.

     

    A falalar 'yan Bargu duk a ƙasar 'yan Bargu,

    Sai Musulunci tsantsa kafurci ko ƙwaya,

    Babu ɗigon kafirci daga ƙabilar Bargu,

    Allah riƙa Allah tsare rai ya daɗe mai Bargu,

    Aminu Alan waƙe ke biya talifin Bargu.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.