Ticker

6/recent/ticker-posts

Gimbiya Mero Tanko Almakura

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Gimbiya Mero Tanko Almakura uwa,

Garkuwar matan Nassarawa ce gimbiya.

 

Shimfiɗa

Ga sakainar ruwa ishe ta sai an iya,

Kin zamo kainuwa dashenki Allah ɗaya,

Mai nagarta ake wa tamburan lafiya,

Gimbiya Mairo kya gama daram lafiya,

Manufarki a samu wanzuwar lafiya,

Ƙudurinki mata su zam cikin lafiya,

Ragamar dukka mai nufin zaman lafiya,

Na gurin Rabbu Khaliƙinmu ƙwalli ɗaya,

Bisa yardarsa ne kika zamo gimbiya,

Garkuwa a wajen dukan matan lafiya.

 

Masarauci Ubangijinmu Allah ɗaya,

Mabuwayin da shi ake wa bauta ɗaya,

Ƙarfafe ni abin da nai nufin zan biya,

In bayani a kan ta Mairamu gimbiya.

 

 

 

 

Masarauci ka yo tagomashin kariya,

Ga Aminu Muhammadu khairul anbiya,

Mahabubu abin yabon mu kau bai ɗaya,

Ɗan Amina mijin Khadija har Mariya.

 

Zan yi waƙa gurin uwar marayun ƙasa,

Gajiyayyu suna uwarmu ba cinkisa,

Naƙasassu suna muke da maman ƙasa,

Garkuwa a wajen dukkan mata kulliya.

 

Hajiya mai halin yabo akan wa yabo,

Hajiya mai halin faɗi akan wa yabo,

Hajiya Mairo Tanko Almakuran yabo,

Nasarawa dukkansu na yabon Shaksiya.

 

A halinki maza da mata duka na yabo,

Na ji har ma Sadauki Lafiya na yabo,

Aka ce wai saninki na a babban rabo,

Da nagartar halinki ga riƙon gaskiya.

 

Daga Keana suna kiran ki sarauniya,

Ga sarauta ta garkuwa gurin gimbiya,

Ga sarauta ta Keana ki ce sarauniya,

Duka mata suna ƙasan ki ba na riya.

 

Dukanin ɗaukaka tana ga mai kyan hali,

Da halinki kike ta ƙyalƙyalin walwali,

Duka aure bayan sadaki sai alwali,

Taka sannu ta Almakura sarauniya.

 

A kamala kamarki za a sha ‘yar wuya,

Haka hali a sam kamarki a sha wuya,

A dabi'a ko nan wajen ake turjiya,

A karaɗe ƙasa a sam kamar gimbiya.

 

 

 

Ko a mata irinki ban da ban ban suke,

Duka motsinki in da duk kikai ke ake,

Allah sambarka inda duk kikai ce ake,

Ta daban ce uwar marayu sarauniya.

 

Gantamau ne uban su Zara har A’isha,

Ga mawaƙi na ɗauri har na yanzu su sha,

Lafazina fa ba hululi kuma ba assha,

A yabon garkuwa ta Tanko ko gimbiya.

 

A yabo gun uwa mabada mama a sha,

Godiya gun Abubakar Sadauki na sha,

Da yabawa uwa ma sha da kowa ya sha,

Gimbiyar Tanko Almakura sarauniya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments