Amshi
Jikan toro mai martaba,
Attahiru Abdurrazak,
Bunun Bargu mai darraja,
Allah ma dubun É—aukaka.
ShimfiÉ—a
Rana mai rabon ayyuka,
Gulbi sha da kowa duka,
Bango maganin É“arraka,
Turmi sha luguden daka,
Gamji nawa sha sassaƙa,
Jikan toro sha baituka,
Taka sannu ba fuffuka,
Kwana a tashi gun mai duka,
Buri zai cika har É—aka,
Tauraronka na haskaka,
Ala ke yi maka baituka,
Bunun Bargu mai É—aukaka,
Ya Sattaru gode muke kai baiwa cikin duniya,
Mai darajar halittu duka É—an Adam cikin duniya,
Mai falalar halittu duka annabi shugaban duniya,
Ai ni'imarmu ta bayyana albarkar mijin Mariya,
Da na zamo cikin al'umar annabi shugaban duniya.
Annabi khatimul anbiya mai matsayin da ba shamaka,
Mai tsarki jiki annabi mai nasabar da ba É“arraka,
Tsira har aminci duka yi su ga mai dubun É—aukaka,
Ali sahabihi su duka masu biyarsa 'yan É—aukaka,
Rabbu da su na kamun ƙafa ƙarfafi hikkima haɓɓaka.
In ba ka san gari ba na ce saurari amon mai daka,
In ba ka san masoyi ba kau kallaci wanda ke 'yammaka,
Rana mai rabon ayyuka ba na waje ki ba na É—aka.
Bi ni a sannu kan sussuka da rairayo amon baituka.
Da izinin maƙagin duka mai sama ne nake baituka.
Waƙa sai da hujja ake, shi sanadi da ƙarfi yake,
Wasu yabon masoya suke, wasu yabon siyasu suke,
Wasu yabon su roƙo suke, wasu a nasu horo suke,
Kowa yabon muradi yake, yanzu yabon sarakai nake,
Wajen da mallakarmu take,
Gargajiyar ta'adu suke.
A yau yabo na bunu nake, bunu na Bargu waƙa nake,
Yabon jinin sarakai nake, mai asalin da har ya tuke,
Mai nasaba da kyawu take, mai darajar da yau zan sake,
Bunun na Bargu shauƙi nake, da zarafin yabawa nake,
Mai É—amara ta horo nake - yabon da baitukana suke.
Toro mai kiwo shi É—aya, ko a cikin mazajen dawa,
In ko batun sarauta ake, zaki ne uba mai dawa,
Tashi a bi ki uwar zuma, inda ta rankaya ko dawa,
Masu maÉ—i gusa ban guri, mai sukari jiki na rawa,
Na ajiye fa kwangin zuma, za ni in aika mai isuwa.
Bunun Bargu mai darraja ka kai ay yi ma tambura,
Ka kai ay yi ma jinjina ai busa da ma tambura,
Domin É—an saraki kake yanzu a zaune zauren jira,
ÆŠan sarki fa sarki yake a kwana a tashi sai kabbara,
Rabbu Wahabu ka san nufin masu kira da ƙoƙon bara.
Jikan toro mai illimi dama da hauni duk masani,
Ga ilimin sani sharri’a ga ilimin sanin addini,
Kana sanin hadisai a ka kana sanin na Al-ƙur'ani,
Sashen illimin zamani kai digiri da mastas sani,
Bunun Bargu kai godiya ka É—ara tsarakinka sani.
Yai degree sociology, kan ilimin zaman duniya,
Yai masters fa a scurity and strategy Maliya,
Fannin illimi kan tsaro nan ya ƙware fa ba tankiya,
Yanzu protocol officer ne a ciɓil defence kun jiya,
PO na commander genar ciɓil defence a nan tarayya.
Jikan Garba É—an Balki ne yayan Dije da Zahara,
Da gun Dije wan Dije ne baban Dije da Zahara,
Wanda akan kira gantamau sashen hikkima fikkira,
Bunun Bargu kai kabbara don na share filin dara,
Rabbu Wahabu dafa mana amsa kira na mai yin bara.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.