Ticker

6/recent/ticker-posts

Usman Kogunan Gamawa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi 

Ku ba ni tambura za ni yabon abin yabawa,

Jinjina na ke Usman kogunan Gamawa.

 

Shimfiɗa

Ƙashin bugun ƙashi dogara ka ji tamburana,

Ruwan kashe wuta gagara ka ji bambamina,

Yabon abin yabo ne take na baitukana,

Hali ake yabo jajira aka san sanina,

Dubu jiran guda tokara kalli kallumana,

Ganau nake jiyau ne ni kansa kogunana,

Don ka yi na gani kai fi ɗai a kan idona,

Allah ya ƙara ƙarfin nema jinin Gamawa.

 

Kira nake ga Alhayyu abin riƙo a bauta,

Cikin kiran maƙagina ma ishin halitta,

Ina kira da tattausan laffazin bajinta,

Ubangiji ka lamunce min fagen tsayawa.

 

Ina riƙo da jigon ƙauna gurin halitta,

Madogarar mu Amadu shuma gaban halitta,

Riƙo nake da tsanin ƙaunar ubansu Binta,

Haɗa da darrajar ahalin ɗan Larabawa.

 

A ƙarƙashin dalilai biyu nai nufin yabon ka,

Da fari alƙawar in har ka yi kai da kanka,

Da son Ubangiji za ka cika shi babu shakka,

Na biyu ko zumunci na shaidi ɗan Gamawa.

 

Wadan su na biki da zumunci gwanin Gamawa,

Da an yi sai su rama in an ƙi su kirewa,

Waɗansu na zumuncin aisabis Gamawa,

Kawai ganin ido ke sanya su sabbahawa.

 

 

Waɗansu ko da maigirma dai suke Gamawa,

Da mai kuɗi da masu muƙami suke ƙwamawa,

Dodon uwar masaƙa Usumanu ɗan Gamawa,

Da mai kuɗi da mai mulki duk yake Gamawa.

 

Idan da mai kiɗan kurya mu yi wa ɗan Gamawa,

Idan da mai kiɗan taushi mu yi wa ɗan Gamawa,

Badujala sarewa busa wa ɗan Gamawa,

Ko da da tambari zan doka wa ɗan Gamawa.

 

A kan kawai halayyar nan kogunan Gamawa,

Na na hakkake da in tsara baitukan Gamawa,

Cikin dubu a halayya alkwar makwarwa,

Kana zumuntaka wannan babu ma ta cewa.

 

Taka da lafiya Usman kogunan Gamawa,

Rimi adon gani daga nesa tsimin isowa,

Farin hali farar suffa Shehu ɗan Gamawa,

Na san hakikatul amri za mu je Gamawa.

 

Da ma a ce cikin al'umar jihar Arewa,

Ina nufin a hausa fulanin ƙasar Arewa,

Idan da mai halayyar Usumanu ɗan Gamawa,

Guda bakwai kacal da sun kare tallakwa.

 

Halin ka ya yi min Usman kogunan Gamawa,

Adon ka ya yi min usman kogunan Gamawa,

Kamarka ta yi min usman kogunan Gamawa,

Ba ka san baƙin ciki ba burinka ai wa kowa.

 

Yayan Habibu yayan Garba da Nana Hauwa,

Ubangidansu zakin zakzaki ɗan Kanawa,

Kura mabi dare mai cirani don sanarwa,

Mai tambari kanin kalmarsa yake yabawa.

 

 

Irin zubin da nai ba da kuɗi akan zuba ba,

Da na ji walwala da nishadi da ba matsi ba,

Kamar zubar ruwan marka za ka ji su baba,

Jerangiya kamar rauhanai suna tayawa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments