Ticker

6/recent/ticker-posts

Nasiru Dan Dano

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Nasiru ɗan Dano dubu jiran ɗai a gayya,

Ɗan amana na Dutse yau kake ba hamayya.

 

Shimfiɗa

Mai bugun ramli ya bugo dariki da rayya,

Mai dariki farin ciki ya harbo da gayya,

Shi ko rayya ka san ka na gidan 'yan hamayya,

Mutuwa ko baƙin ciki gidajen su rayya,

Nasara na gidan Dano uban tara gayya,

Ɗan amanar uban ƙasa janar masu gayya,

Na gurin Buratai uban maza watsa gayya,

Ɗan gaban goshi gun uban ƙasar Dutse hayya,

Mai asarki akiza mai gadawur da gayya,

Ga yabon Nasiru inai ciki ba hamayya.

 

Nasara dai nake biɗa gurin mai rabawa,

Wanda shi ke rabo na rahama babu kwarwa,

Gyangyaɗi ba shi riskuwar maƙagi na kowa,

Ko bare cinkisa da gajjiyawar gazawa.

 

Khaliƙi godiyarka na yi na jaddawa,

Falala wacce kay yi min ka zamto daɗawa,

Nasarori suna zuwa a huce da baiwa,

Ba barin martaba da tumbuɗi na kwakwalwa.

 

Gaisuwa gun Muhammadul Aminu na kowa,

Shugaban mursalai da annabawa na baiwa,

Mai sahabbai kwatankwacinsu ba a kumawa,

A nagarta zuwa riƙon amana da baiwa.

 

Yau yabon godiya na gurguso don yabawa,

Ga ubanmu majingina madafar fakewa,

Masani akili cikin sarkan Arewa,

Nuhu Mamman Sanusi Allah kareka yalwa.

 

A sarautu na hakimai da dama Arewa,

Daga jin ɗan amana an riga an ƙurewa,

Daga ji ɗan halaliya ake bai wa baiwa,

Daga ji ai sarautakar ga 'ya'ya akewa.

 

Wanda duk an ka ce wa ɗan amana ƙurewa,

A aminci kusan ya kai magaryar tuƙewa,

A kusanci kusan ya kai makwarwar kusurwa,

Da aminci ake amintuwa ai daɗewa.

 

Nasiru Haladu Dano ina sabbahawa,

Ɗan amana na dutse tamburan sallamawa,

Mai nagarta na gun janar na gwamnan Jigawa,

Eɗcelency badar riƙon amanar Jigawa.

 

Jinjimi ƙwai da damina ake karkaɗowa,

Gamji sara da sassaƙa na mai sassaƙowa,

Bai kisanka kana ba shi hana ka fitowa,

Taka sannu ubangida da halin yabawa.

 

Duniya an yi makka godewa tai ragewa,

Arzikin duniya gida da mota akewa,

Kana sannan da lafiya da masu rakawa,

'Yan baranda gida da dawwa na tuttuɗowa.

 

Sanadan nan uku da kan saka ai naɗawa,

Jarumta da assali da gadon naɗawa,

Ko hidimtawa jamma'a da halin yabawa,

A rukunnen ga babu wanda ka ɗungushewa.

 

Yau uban Dije ɗan Khadija ke baitukan nan,

Tambarina tsakar dare nake walwalar nan,

Saƙe-saƙe da ƙulle-ƙulle har warwarar nan,

Da kaɗaici nake rawar bazata a sannan.

 

 

Ko ka ce min Alan mutan Kano ɗan Kanawa,

Gungurun gagarau ga masu son mirginawa,

Goɗiya ta wajabta gun maƙagi na kowa,

A yabon Nasiru Dano fa na kammalawa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments