Ticker

6/recent/ticker-posts

Fuju’a

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Fuju’a masoyi rabuwar fuju’a masoya,

Sai auren tunani rabuwar fuju’a masoyi.

 

Ciwon so da zogi,

Rarrashi nake yi,

Sai auren tunani rabuwar fuju’a masoyi.

 

Ya Sarki buwaji Allah ka tsare ni shayi,

A ciki kar in yi tsimayi,

Zan waƙar masoyi,

Ilahu ka sa kada in bulayi,  

Sai aikin tunani,

Rabuwar fuju’a masoyi.

 

Na ɗauki motata da niyyar za ni in tuƙa kaina,

Na saka ɗan mabuɗi na tayar sai in ji ɗas gabana,

Ina kallon maleji tamfirecar duba maina,

Sai in ga taswirar motan nan da na ce masoyi.

 

In maza in kawar da idona sashe na madubi,

A hannun dama domin in nazarin sashen madubi,

In ga taswirar masoyin nan a jikin madubi,

Haka ma a hannun hagu da madubin san ta duk masoyi.

 

Sai in kifad da kaina a kan sitiyarin motata,

Sai in rintse idona ina kaɗa kai don zuciyata,

Nan ma kiciɓus nai da hoton nan da na lasafta,

Karkataf na sa zuciyata don rabuwar masoyi.

 

Idan na ga gajimare ya tafi a sama a keɓe,

Sai in yi murmusa in samu guri na zama a keɓe,

In masa ƙyar da ido ina kallon tafiya a keɓe,

Sai hoto na baya ya dawo wanda na ce masoyi.

 

 

Ko da tsakar dare da taurari birjik samani,

Na yi rigingine a mashinfiɗina na yi rauni,

Ina kallon adon taurari sun cikashe samani,

Ɓaɓal-ɓaɓal nake ji motsin nan da na ce masoyi.

 

Sai ta ciko idona ƙwalla can kuma sai hawaye,

Tai ta zirarowa zuwa kunnena duk hawaye,

In sake murmushi idona shi kuma la hawaye,    

Allah ka kiyaye rabuwar fuju’ar masoyi.

 

Idan aka ce wata ya kama daren sha biyun nan,

Ko kuma sha huɗu ko goma sha biyar a ran nan,

Sulusin dare na farko ya haske garin nan,

Sai in zamo kamar warkakkeci don kewar masoyi.

 

Watan wataran in tashi na je ɗakin bitar karatu,

In tafi laburari da niyar yin nazarin karatu,

Na bincika na ɗauko littafin karatu,

Da na buɗa shi sai in ga taswirar da na ce masoyi.

 

In yi zuru idona ina kallon na matallaraye,

Ko kallon ƙuda da akan cewa kuma ga hawaye,

Rannan dai karatu ba shi yiwuwa sai dai hawaye,

Ina ta begen rabin rabuwa fuju’a masoyi.

 

In tafi daji ina kollon bishiya a ƙauye,

Ina ta safa da marwa ina kallon wasan tsuntsaye,

Ina annashuwa da sautun kukan tsuntsaye,

Iska na buga ni ina begen da na ce masoyi.

 

Sai da ya zamma lahaula walaƙuwata a guna,

Na yi alwala za ni yabon Sarki na kaina,

Ko a cikin ruwan alwala hoto ne da rana,

Taswira ta ran nan da na ce masoyi.


Da na fuskanci alƙiblata domin gai da Sarki,

Sarkina Buwayi zummar salla zan yi Sarki,

Sai wasiwasi ya mamaye ruhina da ɗoki,

Kokonto nake yi saboda ganin masoyi.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments