Ticker

6/recent/ticker-posts

So

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:

So sarƙaƙƙen zance mai sarƙaƙe masoya,

So so so na kanka mai sussulle masoya.

 

Allah kai muke so so mai sadar da da sawaba,

Ya Sarki salama mai son ka ba zai sane ba,

So fa halitta ne ba harsashe bane ba,

Zaɓin zuciya ne ba tilas shi ake ba,

So alƙawari ne e ba hilatta ake ba,

So fa gamon jini ne ba gamo na gambiza ba,

Kamar sartse ka soka a ba sukar mashi ba,

Kamar mai ƙoya kana so ba dila ta ungula ba,

Linzami so ilimi ne ba tarin jahilci ba,

Turkar sohankali ne ba ɗiyar rashin rayi ba,

Komai zafi laƙaninsa ai haƙuri ba zai gaza ba,

Idan so ya zama cuta haƙuri fa ba illa ba,

Mu Ankara dai matasa ba sunbatu nake ba,

Ba sunbatu nake ba jinini nake ba.

 

So ba ƙwarmato ba,

So ba kwakwazo ba,

So ba kwallagwazo ba,

So ba banbaɗo ba,

So ba kankanbaa ba,

Ai nazari ai nazari samari so ba bambaɗo ba.

 

So ba kwarkwasa ba,

So ba zirgilli ba,

So ba tsugudidi ba,

Ba da giringiɗishi ba,

So ba shishshigi ba,

Albishirinku masoya albishirinku masoya,

So ba kinibibi ba.

 

Ga gutsiri tsoma ba,

Ba tsegumi ba,

Ba surkulle ne ba,

So ba tsafi ba,

Ba yin tsatsuba,

Ai nazari ai nazari masoya,

So babin bokaye ba.

 

Ba bin bango ne ba,

Ba shan minti ba,

Ba nanaye ba,

Ba cika lubaye ba,

Ba gwalli bane ba,

Albishiri albishiri masoya,

Ba zuƙi ta malle ne ba.

 

Kar ki sake kar ki sake tai miki nanaye,

Kar ki sake kar ka sake tai maka lubaye,

Da kin gan shi ki dube shi ki nazarin ɓoye,

Da ka gan ta ka dube ta kai nazarin waye,

So ba cin fuska ba kuma ba cin zarafi ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments