Amshi: Ga zaɓe na isowa,
Kar mu zaɓi tumun dare Nijeriyawa,
Mu fito ƙwai da ƙwarƙwatanmu,
Don mu bar ƙabilanci Nijeriyawa.
Allahu ga mu gareka,
Mai tasarrafin dukkan al’amuranmu,
Salli ALA annabinka,
Shugaban da ya zama jagora gare mu,
Bayi mun zo gareka ya Ilahu tallafi yan Nijeriyawa.
Ga ruwa yana cin yan Nijeriyawa,
Ga wuta tana bin yan Nijeriyawa,
Tallafe mu don kada a kassassara mu,
Kai gudunmawa don kada a hahhallakamu.
Rigima ba da bindiga ba ba faÉ—an takuba ne ko gariyo ba,
Rigima ba ashariya ba hankali da ilimi ne ba nuna zamba,
Bana ba za mu bari ba ba mu sai da ‘yancinmu Nijeriyawa,
Dukka shugaban da a yau Nijeriyawa yai nufin ya tauye haƙƙin Nijeriyawa,
Za ya gwammace shan ɗaci da alewa ba mu ba zaɓen gwarmai mai haɗawa.
Ku fito dukka mu yi rijista,
Dattijai zuwa ga matasa mu yi rijista,
Mu fito yan maza da mata,
Duk mu É—unguma mu je mu yi rijista,
Mu riƙe kishin ƙasata, kishin ƙasa zamu yi Nijeriyawa,
Don mu sam zama na lumana guna na kowa,
Mulkin adala dai Nijeriyawa,
Gaskiya riƙo na amana ba gazawa,
Kar mu zaɓi masu kasawa da hanawa.
Kada mu banbanta yare,
Ba mu son ƙabilanci Nijeriyawa,
Kar mui ƙyama ga yare,
Kar mu ƙirƙiro basasa mui kulawa,
Komai namu a tsare,
Tun firimiya na ƙasar Nijeriyawa,
Har zuwa rijin lidar Nijeriyawa,
Irin firimiya Ahmadu jigon arewa,
Irin dakta Nnamdi Azikiyawa,
Obafemi Awolowo na Yarbawa,
Yau an canza akala,
Falimantari system mun sashi bola,
Mulkin soja da hula,
Sun yi sun gama kowa dai nata ƙwalla,
Wai mene ne ya saura sai kuma muka raja’a mulkin mutane,
Mulki da harsashen taron mutane,
Mulki da rinjayen taron mutane,
DemokaraÉ—iya mulkin mutane,
DemokaraÉ—iya ‘yancin mutane.
Mulkin nan na siyasa ya zamo mulkin na masu yasa,
Mulkin nan na siyasa ‘yan uwa kar mu riÆ™e shi da wasa,
Ya zama mulki na gasa ya zama mulki na yasa,
Ya zama mulki na yasa kar mu bai wa masu ƙabilanci riƙonsa,
Kar mu yarda mu yi É“arin gagara kwasa mui riÆ™o da yaÆ™in kuri’a babu wasa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.