Ticker

6/recent/ticker-posts

Tallafi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Shekara nawa kenan batu na tallafin fetur Nijeriya?

Ga tuni a gare u shuwagabannin ƙasar yankin Nijeriya,

Shekara nawa kenan batu na tallafin fetur Nijeriya.

 

Ɗan mabuɗin waƙar a yau ya zo da istigfari,

Astagfurullah lillahi wahidun ƙahhari,

Wa atubu ilaika mai sanya ƙaddarar alkairi,

Share kukanmu an tsunduma mu halin wayyo bai ɗaya.

 

Mulki na mutane kuma fa ƙirƙira ta mutane,

Don wasu mutane taken da muka rataya ne,

Sai ga shi mutanen waɗanda an ka wa mulkin ne,

Sun fito har ƙwansu suna ta ɗuga tutar na-ƙi da na-ƙiya.

 

Ko ana ɗaya an kai zuwa bakwai da ba sauyawa,

Kuma an yi asarar rayuka da ba mai gawa,

Kuma an yi asarar lokaci da ba zai zo ba,

Ba ta sake zani ba sai ɗan karen wuya da aka sha tin jiya.

 

Ashirin ga Janairu Juma’a da ban manta ba,

Shekara ta dubu biyu da sha biyu da ban yi kure ba,

Da gari fa ya waye sai Kaduna ban manta ba,

In da za mu Abuja da zang- zanga dai ta lumanar gaskiya.

 

Wai ina da wakilai da mun ka dangwalan kuri’armu,

Wai ina da wakilai da mun ka ce su je madadinmu,

Wai ina sanatoci cikinmu har da dattijanmu,

Yan support on motion sun sai da martabarmu idanun duniya.

 

Muna ta’ajibi muna taraddadi kan haka,

Ashirin fa ga wata Juma’a da yamma i haka,

Ina harama ta in je Kaduna babu mushakka,

Sai na ga hayaƙi garin Kano ya koma duk ya gauraya.

 

 

Da na dubi sama’i yanayinta ya sauyawa,

Hargitsi ya gudana ta ko’ina da ka zagawa,

Go silo ya yawaita kowa yana nufin tserewa,

Sai na kaɗa kaina garin Kano cikin yanayi na Somaliya.

 

Daga wannan rana sai tattalinmu dukka ya karye,

Daga wannan rana sai lamarinmu duk suka karye,

Kasuwa a garinmu middle clerk duka suka karye,

Tsoro ya shige mu sai fargaba ta aure mu ga tirjiya.

 

Ko’ina a arewa an kewaye tsaro na tsarewa,

In ka fito tun safe kafin ka kai gari sai fawa,

In ka fito ba tabbas ba tabbaci na ka komawa,

Sallama da iyali muke a yau idan har za mu zagaya.

 

Sai idan ka dawo cikin gida a yi maka barka,

Dokar ta-ɓaci ta baibaye mu ta mana sarƙa,

Mu ko ba mu da ‘yanci maza kama da matan ɗaka,

Ɗimuwa a jikinmu Allah ka kare yankin Nijeriya.

 

To ashe arziki muke ciki zama na salama,

Ka fito in ka so ka so a sa’ilin da ka koma,

Ka yi sabgoginka ka wataya cikin al’umma,

Yanzu ba mu da yarda ba mu da izinin shewa sharholiya.

 

Ga bajet da akan yi na jami’ai dake ta tsaronmu,

Mafi yawa na kuɗinmu ana kashe su ne ga tsaronmu,

Babu kayan aiki da za su taimaka a tsaronmu,

Dubi matan Cibok an kwakwashe su bana ɓoyen tsinkaya.

 

Ya Mudabbiru Allah Ubangiji ka kare ƙasarmu,

Ya Musawwiru Allah ka sauya masu zaluntar mu,

Yau ruwa ya ci mu ba ma kamar arewa garinmu,

Addu’a fa nake yi Allah arziƙi namu zauna lafiya.

 

 

 

Duk abin da ake yi kai ne mafi sanin sirrinsu,

Zahiri da fakenmu Allahu kai ka san motsinsu,

Dukka masu nufaƙa kai ne mafi sanin kaidinsu,

Ya masharin kuka ka share dukka matsalar Nijeriya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments