Ticker

6/recent/ticker-posts

Dashen Mai Shukan Kainuwa Hawa Mulkin Lamaran Yaro

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Dashen Mai Shukan Kainuwa Hawa Mulkin Lamaran Yaro


Gwamna na Kaduna abin yabo abin son kowa bai ɗaya,

Da suna na mai tasarrafi nake farawa ƙwal ɗaya,

Abin bauta mai tajarrabi muna gode maka bai ɗaya,

Mai kumfa yakunu mamallaki muna godewa ka biya,

Cikin ƙudura taka ne ka sa mulki ya zamo riƙar aro.


Mai yadda ya so kan lamamri ba mai sauyawa kun jiya,

Allah Rahamani Arrahimu mai juyawa shi ɗaya,

Mai ba da muƙami duniya ya ba baubawa mulkiya,

A san da ya so kuma wahidi ya karɓi abin da ya bai aro.


Tsira da aminci ɗaukaka ka bai wa masoyin gaskiya,

Ahali da sahabu su duka da ba su da shayi ko ɗaya,

Ka sa da waliyai malamai waɗanda suke yin tarbiya,

Kira abu Allah shi kaɗai a kan hanya ba tasgaro.


Ina zamanina a Kano sai naj ji wayata,

Na sa ta a kunne nai halo da baki na furta,

Bushara an ka min da Rabbi ya juya ta,

Tutar mulki Ƙadiran ya juya abin da ya bai aro.


Sai na tuna loton da akai tsumi na ji rana,

Ana ta tsumina in yi yabo da baitocina,

Aljihun baya ban yiwa yabon waƙena,

Ashe baitina zai ishe ka ɗan Sambo Lamaran Yero.


Me cim ma muradi yi haƙuri da ke dafa dutse,

Ka zammana dutse a ruwa kai ƙassa ka nitse,

A yau haƙurinka ya zamo kadarko na ratse,

Ka zamana gwamnan arewa abin alfahharo.


Waƙar da nake ba jam’iya nake yi wa ba,

Waƙar da nake ba fahar nake yi ma ba,

Na daɗa miƙo godiya ga Allah Rabba,

Da yai zaɓinka Lamarana ɗan Sambo take Yero.
An sha ƙuna ag gurin abokan gaba,

Rana kuma ƙuna innuwar ba ah huta ba,

Ka sha kuɗa izgili ba za a kwata ba,

A ƙarshe Sarki mai daɗa ku yag gwada shi ke warwaro.


Mai ɗaga muƙami yai sama da ya so yanzu ya gangaro,

Mai ba bawa riƙar aro a kwana a tashi ya tuntsuro,

Mai talalar mai izgili da yai gaba sai ko ya ɗinkiro,

Ka lura da aya, shugaba abin fahari Lamaran Yero.


Mawaƙa sun kai ayari ka nuna ta ɗauka ba jira,

Kowa kibaunsa ya ciro giwa ta faɗi a kakara,

An ce mini an maka baituka da sun fi ɗari da ɗigo tara,

Ni tawa nasiha zan maka don ka saka riga ta aro.


Cikin tafiyarka shugaba ina miƙo ƙoƙon bara,

Suka na magauta waiwaye kar ka yi bare kay yo jira,

Ka sanya gabanka, kai gaba muna nan mu sai kabbara,

Kar ka yi nufaka ka riƙe abin da Ilahu ya ƙaddaro.


Ka kau da ƙabilancin zama da bambancin yare duka,

Faɗan addini ka kawar mu zauna lau mu mu duka,

Arewa ƙasarmu an shigo ana raba kanmu haɗin ɗaka,

Mu zauna lami lafiya Musulmi Kirista ku tattaro.


Mulki na ɗorewa idan da adalci mai bai ɗaya,

Yana rushewa in da so fa na zalunci ƙwar ɗaya,

Ka harhaɗa kanmu Rabaren da Ustazanmu gaba ɗaya,

Da kai haka zama lafiya ya samu wuri ba tazgaro.


Mulki na ɗorewa idan da adalci mai bai ɗaya,

Yana rushewa in da so fa naz zalunci ƙwar ɗaya,

Ka harhaɗa kanmu Rabaren da Ustazanmu gaba ɗaya,

Da kai haka zama lafiya ya samu wuri ba tasgaro.


Turakin dawakin Zazzau ina godewa,

Dalilin waƙar kai ka ce in tsattsarawa,

Albarkar gwamna ga yabo ina sherowa,

Ina rerowa gun sa gwamnatin Malam Lamaran Yero.Idan ka ji an ce ɗan ƙwarai ka lura ka duba,

Ya samu uba ne naƙ ƙwarai ko ba ka sani ba,

Turakin dawakin Zazzau baba mara aiba,

Ina baitocin godiya gurin Allah mara tasgaro.


Hajiya Fati ga yabo ina miƙowa,

Albarkar ɗanki ni nake ta baiti yabawa,

Albarkar ɗanki ni nake miki fa yabawa,

Allah sa alkairi a ciki na mulki nai Lamaran Yero.


Ɗa gun Fati ga yabo ina miƙowa,

Baban Fati ga yabo ina aikowa,

Angon Fati,

Ɗa gun Fati,

Baban fati ga yabo ina yi tamkar warwaro.


Baban Usmanu ina yabo,

Baban Zara’u ina yabo,

Baban Fatima in ayabo,

Baban Saddiƙu ina yabo,

Baban Ahamadu ga yabo,

Baban Muhammadu ga yabo,

Uban A’isha nake yabo,

Ga yabo.


Angon Faɗima uwar gidan sarautar mata,

Angon Faɗima uwar gida daban fa a mata,

Sannu Faɗima na kira ki zakkar mata,

Matar gwamnanmu, matar gwamna Lamaran Yero.


Kada in yi tuya ban sako da albassa ba,

Uban tafiyarmu in wuce shi ban wasa ba,

Namadi Sambo Deputy President,

Namadi Sambo shugaba fa jagoran Lamaran Yero.
‘Yan uwan iyayensa nake yabon wasawa,

Hajiya Gambo da Abdulkadir,

Abdulkadir Sambo,

Da Sani Yero,

Da Ahmadu Sambo,

Sai Ibrahim Mamman Sago.


Ƙanne na jininsa nat taho in ɗan wasawa,

Da Abdullahi,

Da Nura da Zara,

Sagir da Yassir,

Kalid da Idi,

Da Amar cikinsu nat taho in wawwasa su in kankaro.


Shaƙiƙan gwamna zan wuce in jejjero su in kambamo,

Muhammadu Sani Sadik ciki,

Dijine ma a ciki,

Malam Sadin Polytechnic na sako ka ciki,

Zakari E.E.S na saka a ciki.


Aliyu Makama na sako,

Baba Idi na sako,

Abokan aiki za na je in wawwaso su in wassako,

SSG ma na sako,

Hamza Ishak ma na sako,

Ɗan Mahawayi nas sako,

Sama’ila PPS ciki.


DG midiya Ahamad mai yaƙima,

Yahaya Amini cif of citaf da Madami,

DE Madami ad Dubai za politics ma,

Abokansa Abdullahi manaja Mu’azu akawu kuma.


Madakin tsafta a ciki,

Atiku Turaki a ciki,

Turakin ondora ciki,

Kabir lema a ciki,

Tanimu Sa’ad a ciki,

Makama na sanyo ciki,

Albarkar Mamman ɗan Yero.


Magaji Bos ma a ciki,

Galadima ma a ciki,

Sulemanu Jumare ciki,

Lawan soja ma a ciki,

Da sani Umar a ciki.


Ibirahim Umar da Garba ido a ciki,

Muhammadu Sani da Adam Isiyaku a a ciki.


Masoyan gwamna Falulu Umar a cikinsu,

Sa da Umar Yakubu Lere cikinsu,

Umar Jakada jama’a ina ta yabawa,

Sai Yakubu Lere ga yabo yabon gwamna Lamaran Yero.


Makaren gwamna ga yabo ina sherowa,

Makaran gwamna ga yabo su ADC ina ta yabawa,

ADC Tafida,

Chief Security ma,

DSP ne,

Jamilu ina yabo ba tasgaro.
Haɗa Manniru a ciki haɗa har Gimba a ciki,

Da Abbas shi ma a ciki,

Haɗa har Abbas Odili nake ta yabawa,

Albarkar gwamna,

Albarkar gwamna ga yabo ina ta zubowa.


Muhammadu Sani Ladan Ahmad Isiyaku,

Ina ta yabawa, 

Abin da ku kai min,

Ina godewa,

Mai sunan baba ga yabo ina ta fa yi wa.

4.3 Dashen Mai Shukan Kainuwa Hawa Mulkin Lamaran Yaro- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 124)


Post a Comment

0 Comments