Ticker

6/recent/ticker-posts

Kira ga Gwamnoni

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Kira nake gare ku gwamnoni,

Ku bar mana naɗin ciyamomi

Naɗi a ƙananan hukumomi,

Bai nuna adalcin siyasa ba.


Allah na ambata na kai kuka,

Kukan wanda an ka wa duka,

Allahu kai ka ƙirƙiro doka,

Kai sannadi na shugaban doka,

Ka ce a bi shi ƙarƙashin doka,

Zalunci kai hani a kan kanka,

Sannan ka ce haram ga bayinka,

Ƙara na zo gare ka bayinka,

Waɗanda sun ka zamma sa doka,

Sun bar mu a ƙasa muna kuka,

Ba mai wakiltakar mu don barka,

Zaɓi muke biɗa a kan doka,

A kan doka,

Ba shugaba na je ka na yo ba.


Allah na ambata a waƙena,

Duk sanda nar riƙe kaumbana,

Sai nai riƙo kuma da so ƙauna,

Ƙaunar Muhammadu madubina,

Da na yi ban ƙasa a guiwa ba.


Wanshekare na ɗauki kayana,

Na je ga Nalge in yi kukana,

Nalge fa ƙungiya makarina,

Mai kare haƙƙuna tunanina,

Ƙalubale na ce da su babba.





Nan take shugaban ya dube ni,

Kafin ka ce kwabo ya shaida ni,

Barkanka da zuwa ya karɓe ni,

Zauna ka sha ruwa ruwan rani,

Na ce da shi fa ban ga zamma ba.


To Alan mutan Kano ya ce man ni,

Me ke tafe da kai? Ya tambai ni,

Na ce da shi da ku da gwamnoni,

Kun haɗa bakuna da mizani,

Ba maffita kuka kai ma kowa ba.


Naɗi da kun ka yi hukumomi,

Naɗin da kan cewa kantomomi,

Ya tattara mu ya shigar rami,

Ka ba ni sannadi in sam ƙaimi,

Ban zo na mannufar siyasa ba.


Yai haka ɗan kaɗan a haggunsa,

Ya mai da hankali a damansa,

Sai dariya ta sauka fuskarsa,

Su kay yi da shi da sakatarensa,

Bai sake ce da ni fa komai ba.


Walet a dunƙule ya miƙo min,

Da na aza kuɗi ya miƙo min,

Sai nai biris da kyar ya turo min,

Na buɗe abin da ya turo min,

Sai niy yi al’ajab cikin haiba.


Har shugaban ƙasa ya shaidawa,

Nai tambaya yana ta amsawa,

Ya ce da ni suna ta zagawa,

Kamfen gari-gari na wayarwa,

Na ce da shi ban ga ta zamma ba.



Ba za ni sayar da haƙƙi ba,

Ba za ni in sayar da ‘yanci ba,

Haƙƙinmu ne ba zan ƙi furci ba,

Demokaraɗiya fa ba riba,

In ba an zaɓi shugabana ba.


Abin da na gani fa dangina,

Ya sa ni binciken karan kaina,

Yau ga shi na riƙe kalummana,

Na shirya baituka ga dangina,

Ba za mu zam kamar kumama ba.


Dokar ƙasa da konsitushin ma,

Ta ce a zaɓi shugaban umma,

Zaɓi na ra’ayi na al’umma,

A zaɓi shugaba na al’umma,

Ba wai naɗi na jeka na yo ba.


Yau gwamnati a yanzu tai nisa,

Ga al’umma suna ta sa-in-sa,

Ba wanda za su kai garin karsa,

Su ce da shi ya kai wakilcinsu,

Ba in da za mu bam mu dawo ba.


Ka so waɗanda anka aikowa,

Na gwamnatin jaha yana zowa,

Na ƙarramar hukuma bai zowa,

Ina yake shiga yana shewa,

Alƙawar an ka yo da su ku yo duba.


Noto na shugaban hukumomi,

Sauƙi yana zuwa al’ummomi,

Birni da ƙauyuka suna ƙaimi,

Don ga su ga wakili limami,

Ba sa rasa guri na kuka ba.



Shiyar Arewa kaf ku yo duba,

Jigawa ce kaɗai abar duba,

A North West nake fa tambaba,

Su ne su kay yi zaɓuka duba,

Ba sui naɗi na jeka na yo ba.


Najeriya ƙasa uwa babba,

Jaha talatin da shida duba,

Amma cikinsu goma ne duba,

Su kay yi zaɓuka da ba wai ba,

Sauran na je ka na yi ɗan baba.


Najeriya akwai hukumomi,

Ɗari bakwai yawan hukumomi,

Da ɗoriyar seɓenty four nemi,

Amma cikin yawan hukumomi,

Seɓenty ne su kay yi ba giba.


Sannan asusu don haɗin guiwa,

Bai warware zare da abbawa,

Joint account da ake yo wa,

Nan ne abin yake kwaranyewa,

Ba zai iso ga talakkawa ba.


Ina kira gare ku gwamnoni,

Ku sakki ƙananan hukumomi,

Ku sau musu mara su yo ƙaimi,

Zaɓi na al’umma muke nuni,

Ba tubalin dashe na ƙarya ba.


Idan fa ba biɗar husuma ba,

Idan fa ba nufi na bauta ba,

Ba wai kashi ake na romo ba,

Kai dankali ka sauka ba riba,

Ba dauwama kake tsumayi ba.

4.2 Kira ga Gwamnoni- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 121)


Post a Comment

0 Comments