Ticker

6/recent/ticker-posts

Bubukuwa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Gudun da ba kuɓuta a shi,

Ya zama samkon Bubukuwa.

 

Allahu kai mana magani,

Abin da naj ji da nag gani,

Mugun ji mugun gani,

Rayuwarmu da hautsini,

Abin fa ba shi da kyan gani,

Abin a ƙyama da tsantsani,

Yana saka ni tuntuntuni,

A yanzu ko ya sarayar da ni,

Na rasa inda za ni ni, Allah kuwa, bubukuwa.

 

Muna ta samkon Bubukuwa,

Muna gudu ba gurin zuwa.

 

Ɓarayi a ban ƙasa atifishiyal muka ƙirƙiro,

Su ke addabarmu a ko'ina atifishiyal muka ƙirƙiro,

Masu fo wan nayin Arewa na ƙirƙira aka ƙarƙaro,

Wahalar da muke ciki ita ta sakka suka bijjiro,

Da rashin shuwagabanni adalai da rashin tsaro,

Rayukanmu kamar kiyashi, fagen kulawa ba tsaro,

Rabbi kai ne Rahimi, tsare ƙasar Najeriya.

 

Gudun da ba kuɓuta a shi - a shi,

Gudun da ba tsira a shi - a shi,

Gudun da kwai halaka a shi - a shi,

Gudun da ba nasara a shi - a shi,

Gwara nai kwanciya da shi - da shi,

Gwara nai birgima da shi - da shi,

Gwara nai barci da shi - da shi,

Gwara ma mutuwa da shi - da shi,

Indai da dace da ƙaruwa, bubukuwa, bubukuwa.

 

Ba ku da kwanciyar hankali,

Ba mu da kwanciyar hankali,

Ba su da kwanciyar hankali,

Babu zama lau kan hankali,

Kun yi rashi na adali,

Kuna ta samkon bubukuwa.

 

Abin da yas sa ni tunzuri,

Ina ta tsuwwa cikin dare,

Na kasa barci cikin dare,

Na waswasin na fanɗare

 

Masu mulki daga Kansila,

Ɗanmajalisa sun kantare.

 

Kwamishinoni, Ciyamomi,

Da Gwamnoni sun fanɗare.

 

Su suka saci haƙƙin jama'a,

Babu hukunci garai-gare.

 

Lallai ɓarayi suna suka tara,

An yi gudu ba gurin zuwa.

 

Sittin a cikin ɗari, larura ta sa su bin dare,

Ashirin ta cikin ɗari, talauci ya sa su bin dare,

Talatin ta cikin ɗari, son zuciya ya sa su bin dare,

Lidas sun kantare, malamai sun ɗare-ɗare,

Dukiya ta ƙasa da haƙƙoƙinta sun kanainaye,

Ga isa da cikar isa da alfarma sun tattare,

Shi ya haddasa sace-sace da a ko'ina tamkar ruwa.


Shumagabanni na zamani,

Masu hali na zamani,

Malamai 'yan zamani,

'Yan siyasar zamani,

Talakawan zamani,

Katankatanar zamani,

Ta samu samkon bubukuwa.

 

Ba ku da kwanciyar hankali,

Ba mu da kwanciyar hankali,

Ba su da kwanciyar hankali,

Babu zama lau kan hankali,

Kun yi rashi na adali,

Kuna ta samkon bubukuwa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments