Ticker

6/recent/ticker-posts

Bargon Rufa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Um uhum wannan duniya rayuwa ba bargwon rufa,

Wohoho wannan duniya rayuwa ba bargwon rufa.

 

Rabbana Allah Rahimi rayuwa ba bargwon rufa,

Rabbana Allah Rahimi rayuwa ba bargwon rufa.

 

Rabbana mu bayinka ne,

Ka fa yi mu a don bautarka ne,

Mui sallah azumi domin ka ne,

Mun kaɗaita da bauta gun ka ne,

Rayuwa duk na gun Ka ne.

 

Ya Allah komai ƙudurarka ne,

Samu da rashi duk naka ne,

Rayuwar kowa na gun Ka ne,

Talakawa duk bayinka ne,

Mahukunta ma bayinka ne.

 

Nau a kan mulki duka baiɗaya,

Gurguzu har da mulukiya,

Kafitaliss Demokaraɗiya,

Hard a mulkin soja mazan jiya,

Ku biyo ni da tsinkaya.

 

Ko a zangon mulkin mallaka ilimi talakawa babu shi,

Lafiya jarin tallaka masu mulki na bautar da shi,

Yanzu kuma ƙarya ake ilimi hallau babu shi.

 

Rayuwa wannan ta isa masu mulki tabarman ƙashi,

Da fa kukan ‘yanci muke yanzu ma ‘yancin babu shi,

Demokraɗiya za a yi gurguzu anka haɗo da shi,

Demokraɗiya za mu yi har mulukiya a ciki da shi,

Demokraɗiya munka so mu yi mulkin soja da shi,

Mun aje mulkin mallaka gara kama karya da shi,

Ga Afrika yanki na mu ne koma baya mu aka san da shi,

Rabbana Sarki Rahimi magani Kai ke adda shi,

Ka sani mu bayinka ne ka cire tabarmun ƙashi,

Ba dabara mu bayinka ne gincire mana tabarmun ƙashi.

 

Wasu Shari’a za su yi a Demokraɗiya kuwa,

Sai fa ingausa za a yi ko kuma in ce yekuwa,

Sai badan-badama suke ta yi tarnaƙi ya gaza sintuwa,

Sai bugun taiki anka yi jakuna na yin sukkuwa,

Kwansutushin wai ita za ta ba da izini ai shari’a kuwa,

Ni a nawa sanina ko kuni sai na ce Allah ne kuwa,

In kwa har Allah ne ake ta bibiya karai kwa buwa,

A yi sakkarai bumbumi a bi sarki marasashin uba,

Tafi sak kar kai bumbumi ka bi sarki marasashin uwa,

Rabbana ba ya gyangyaɗi Kaliƙi ba Ya makkuwa,

Jama’a ban da gura-gura mu bi Sarki ba ya mantuwa,

Aminu ALA mai fa ƙulafuci shi yake shela da yakuwa,

Za ku ji bayani nan gaba sanda muka ƙara ɗiya kuwa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments