Ticker

6/recent/ticker-posts

Gwamnan Jama’a Bindo

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Jinjina ta alkhairi gun gwamnan jama'a Bindo

Adamawa na murna bai,

Zo massu da illa ba.

 

Shimfiɗa

Shimfidar farar fuska,

Ta zarce wa ta tabarma,

Mai farin hali Malam,

Bai dace da ƙiyayya ba,

Ya Ubangiji Allah,

Mai baiwa ba ta ƙare ba,

Na yi durƙuso Allah,

Don baiwarka gwani Rabba,

Kai ka keɓu Sarkina,

Bautarka ba a taɓe ba,

Laluɓe nake Allah,

Ba zan zo da baɗala ba.

 

Ga yabo gurin annabi baban Faɗima mai haiba,

Ali wassahabati ban ɗauke masu kalma ba,

Nai riƙo da ƙaunarsu ba zan kai ga asara ba,

Rabbu ƙara ƙaunar su ba za tai mani oba ba.

 

Gayyatar gudu Malam ba a kyale batewa ba,

A bikin gudu Malam ba a gayyaci jaki ba,

Ga ƙudan zuma Malam wa zai zaɓi ƙudan zamba,

Kun sani ƙudan tsando ba zai zo da lumana ba.

 

Ga sugan zuma malam wa zai zaɓi maɗi baba,

Don sugan maɗi malam bai ko kai ta a daɗi ba,

Kana sha'anin waraka bai ko kai ta a da'iba,

Maggana nake malam kan hujja da ake duba.

 

 

Sarrari ƙure doki mai gajiyar da gwanin kallo,

Karɓi ba ni in baka tamkar masu bugun ƙwallo,

Hakka rayuwa duniya ke juyi fa kamarƙwallo,

Yau gare ka gobe kau ba ta tsallake wancan ba.

 

Na yaba wa alkyabbar gwamnoni na ƙasa karkaf,

Mai hali abin koyi mai kyautar karkaf kadagaf,

Mai nufi na alkhairi ba ka abokin burmi kaf,

Na taho yabon gwamna ba zai saren gwuiwa ba.

 

An ka ce da ni jifa ko an yo ƙasa zai yowa,

In ka jefa ɗan sharri ko ya je zai dawowa,

Hakka jefa alkhairi in ya je zai dawowa,

Shi ya sa farin gwamna ba zai shuka baɗala ba.


Tinjimi uban aiki hamshaƙi da ake nema,

Gagarau uban gayya darhamin da ake nema,

Allah raini dumfama aljanna kake sha nema,

In ka shuka alkhairi ba ka girbi asara ba.

 

Damisa maƙi sabo gun mai aikata ha'inci,

Ba sani fa ba sabo gun mai aikata zalunci,

Gagarau uban aiki ba ka yi da malalaci,

Shi ya sa nake waƙar ƙaimi ba da manuba ba.

 

Na ji tsallakar titi ba a yi sai an waiga,

Hakka mattsayin gwamna ba a yi sai an daga,

Lammarin na Allah ne ba jin kai da batun darga,

Mai rabo da insha'a ba masha'a ta aibi ba.

 

Hanzarinka banza ne in ka fito ba ka shirya ba,

In fa kai kumama ne za a wuce ba ka shirya ba,

Duniya budurwa ce gun wawan da yake zamba,

Godiya da sirdi ce ka san ko da batun zamba.

 

Yau Aminu ALA neke waƙa ta yabon Bindo,

Salihi abin ƙaunar salihhai gwamna Bindo,

A gurin mazalunta ko ya zamma kamar dodo,

Haka anka so gwamna ba zai ɗauki baɗala ba.

 

Za ni juya alƙalma in karramma masoyanka,

Sahibai na damanka abbokai da shaƙiƙanka,

In haɗa da gwamnoni abokanka masoyanka,

Masu addu'ar nasara ba ‘yan bita da ƙulli ba.

 

Ga yabo na first lady Maryama matar gwamna,

Jinjinarki Maryama ga sauti na yabon ƙauna,

Allah ƙara soyayya ke da abin ƙauna gwamna,

Allah ƙara maimaici zango nab biyu burina.

 

 

 

Ga yabo na ‘ya’yayen gwamna mai jama'a Bindo,

Auwalu Hudallahi Farouk duk ‘ya’yan Bindo,

Ga Khadija ga Sani 'ya'yan Umar J. Bindo,

Ga Khadija ga Jibirillah ‘ya’yan gwamna Bindo.

 

Gaisuwa da jinjina gun babanmu abin ƙauna,

Babanmu Ummaru ɗan Jibirilla abin ƙauna,

Baba gurin gwamna kau a gaishe shi abin ƙauna,

Allah ja da kwananka kau ya haɗa mu a aljanna.

 

Gaisuwa gurin Adda na gaishe ki da alfarma,

Ɗanki ya yi cara yau alfarma kuma mai girma,

Addu'ar uwa iyaye ce mai ƙwace na cikin koma,

Ba kamar uban kowa kai sa'a daga al'uma.

 

Dagga gaisuwar manya na fara janar nawa,

Gaisheka GMB ba ka rawa da bazar kowa,

Janaral Buhari ne alfaharin ga talakkawa,

Allah ida burinka ai ta rawa a gidan kowa.

 

Gaisuwa ga Barkindo Lamiɗon Adamawa ne,

Daraja sahun farko Lamiɗon Adamawa ne,

Gaisuwa ga mai mulki guna wannan lazim ne,

Lamiɗo fombina mai daraja ta gajin aune.

 

Gaisuwar Abubakar Isa Mubi uban kowa,

Daraja da alfarma na ga abin ƙaunar kowa,

Sarkin ƙasar Mubi ga fa yabonka ina yowa,

Alan Kanawa ne ke ta yabonka gwanin kowa.

 

Sai turaki Adamawa gogarma da halin baiwa,

Gangaran uban kishin Naja har da Arewa,

Ga maraya birni nan alfaharin ‘yan Yolawa,

Gaisuwar farin gwamna na ƙare da gwanin kowa.

 

Jikar bara Nana jikar Dogo uban naira,

Ta wajen furofesa Gaji Fulani mai naira,

'Yar ɗiya ta gwaddabe mai tsinkaya mai lura,

Yau Aminu ALA ne ke baitinki cikin lura.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments