Amshi
Gwamna Bindo gwamnan Adamawa,
Fatan khairi kowa yake yi ma.
ShimfiÉ—a
Samji mai sa sawu su raunata,
Kunya mai sa bayi su ƙuntata,
Ramin ƙarya mai sa a kunyata,
Gaugawa mai sawa a yunwata,
Raunin gata mai sa a jikkata,
Alkhairi mai sawa a karkata,
Dogon buri mai sa a dokata,
Talala hanyar kai mutum wuta,
Wauta mai sa bayi su haukata,
Adalci mai sa wa a tabbata.
Sardaunan mubi ka ƙara karkata,
Kan adalci domin a yalwata.
Mai badawa Allahu Rabbana Sarkin kyauta rani da damina,
Kulliyata Allahu Rabbana na miƙata gunka da dangana,
Bawa ne ni rauni ta ko’ina Æ™alban jasadan ko ma ta ko’ina,
Ga kasawa Allah Ubangiji na gode ma Allahu Rabbana.
Manzon tsira manzo Muhammadu baban Nana haske na zuciya,
Tsanin bayi mai kai ga matsera sirrin É“oye hanya ta shirriya,
Nurul hudda ango na A’isha dodon arna 'ya'yan jagaliya.
Ga baitina don so da bibiyar Allah Rabbi mai ba ni kariya.
Samji mai sa bayi su raunata, kunya mai sa bawa ya kintata,
Ramin ƙarya mai sa a kunyata gaugawa mai sawa a ƙuntata,
Alkhairi mai sawa a karkata, dogon buri mai sa a jikkata,
Adalci mai sawa a tabbata, wauta mai sa bayi su haukata.
Jagoranmu gwamna na jamma'a, kowa nai ma fata da jinjina,
Manya nai ma fata da addu'a, malumma na Allahu Rabbana,
Allah kare gwamna na jamma'a, mai kyan hali Allahu Rabbana,
Yara na so mata suna yabo, gwamna Bindo nai makka jinjina.
Iccen dashi sare shi kad dasa yai ma toho rani da damina,
Jirgin kago ka ya da masu shi, bai ma nauyi balle ka tsugguna,
Babban ganbu ga mai abin yabo gwamna Bindo ga tawa jinjina,
Danki ne kai ƙofar shiga gari sai an taru kafin a mirgina.
Gwamnan aiki Allah riƙa maka, mai kyan haiba zaɓi na al'uma,
Zaɓin kowa gwamnan Adamawa sanata Bindo in ka yi kak kuma,
Linzaminmu kai ke tasarrafi in ka motsa ka motsa al'uma,
Mun miƙa ma ka kama raggama, ba ma bore mai gyara al'uma.
Mamman Jibirin Umar abin yabo, ka tattake sawu na maƙƙiya,
Mai kushe ka sai dai ya gajjiya, ka kekkere tsara da maƙƙiya,
Fatan khairi mu dai muke ta yi kan hanyarka sai kai ta taffiya,
Ba gantsarwa hanya ta gaskiya salin alin kuma ba ƙarangiya.
Sai an jure sara na maƙƙiya sai an daure cizo da dariya,
Dukkan duka da akai wa auraki, bai gocewa a kan tabon jiya,
Marka-marka mai kyau da ƙyalƙyali mai kyan niyya layar a rataya,
Ga sautina Sardauna ka jiya sai in na zo barka da godiya.
Baban Auwal murna nake maka auren Auwal sai nuna godiya,
Malam Auwal ga tawa jinjinar angon Samira taka gimbiya,
Fatan khairi Allah dado rabo karo yalwa ƙari na godiya,
Sardaunan Mubi zai yi zai kuma yardar Allah sarki abin biya.
Yabon girma zan yo da jinjina,
Ga hamshaƙai bango na jingina,
Ga Barkindo LamiÉ—o Fonbina,
Mai martabba nai makka jinjina,
Ga gaisuwar turaki jinjina,
Turaki Atiku ka ci jinjina.
Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.