Ticker

6/recent/ticker-posts

Dan Bello Yahaya Gwamna Mai Jihar Kogi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Ɗan Bello Yahaya gwamna, Adoza mai jihar Kogi,

Muggan madambatan bayi ba za su maka illa ba,

Mai dogaro da Jallallah ba zai gamon akuba ba.

 

Shimfiɗa

Tama masarrafin ƙarfe,

Dutsin fashin tama ne kai.

 

Danki maƙare alƙarya,

Ƙofar shiga gari ne kai.

 

Rani da damina toho,

Icce na ceɗiya ne kai.

 

Sara da sassaƙa mai yi,

Bai sa ka waiwaye da kai.

 

Adoza ka zamo gawo,

Mai tambarin yabo ne kai.

 

Cin duddugen magautanka,

Bai riskuwa ya tadda kai.

 

Allah ka sa gaba Bello,

Ba dai ta mahasudi ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments