Waiwaye adon tafiya ne,
Siyasar ƙasarmu nufi na ƙiblarmu ina muka dosa?
Nineteen siɗty ne muka sami ‘yancin kai ba bone,
Abin murna ne ga ɗan ƙasa da ya san ‘yanci ne,
Abin fahari ne ga ɗan ƙasa da yake kishi ne,
Da India ɗin ne muka sami ‘yancin kai ba aune,
Abin kunya ne yau Hindu su zama gagari gasa.
Fagen kimiyya mu tuntuni aka bar mu a baya,
Mu yo tsinkaya har takanolaji mun zama baya,
Ba ma jin kunya da ‘yan siyasarmu zakkar ƙarya,
Ku yo tsinkaya da laturun fa da aikin hanya,
Ake mana ƙarya in za su kamfen suna sa’insa.
Mu ba ilimi ba ba ƙere-ƙere na zamani ba,
Ba lantarki ba ba ko wadatar ruwayen sha ba,
Mu ba hanya ba ba kasuwanci na zamani ba,
Ba jin daɗi ba ba kwanciyar raid a hankulla ba,
A yi duban duba Allah Ka sauya siiyasar yasa.
Abin dubawa ba arziƙi na ƙasa ka rasa ba,
Abin canzawa ba mineral resoses fa ba babu ba,
Mu ƙara tunawa in mun yi noma fa ba illa ba,
Abin a yi tsiwa sun taru kan fetur ba wai ba,
Haƙin talakawa ba za ya bar ku ba sai kun kasa.
Batun mulki ma dawurwura fa yake al’umma,
A kansu kawai ma ya zam resakilin mulki ma,
Kai mai jar koma kifi fa ya hango ka da koma,
Mai gutsiri tsoma ka bar kaso na haƙin al’uma,
A Ya mai girma da ba inuwa Ka lasa.
Ƙasar babata ƙasar uwa da uba babata,
Ƙasar mata ƙasar ɗiyana mazansu da mata,
Idan na tuna ta sai zuciya ta daka har hanta,
Kuma sai fuskata ta yamutse ta duhunta kamata,
Ƙasar haifata tana cikin garari ba wasa.
Manyan gobe an bi mu anai mana ladan gabe,
Ku bi ni a keɓe ya ‘yan ƙasata da Rimin Keɓe,
Mu ɗauko kube mu yaƙi jahilcinmu a keɓe,
A ranar zaɓe mu kada azzalimi ran zaɓe,
Zan ba ku a keɓe suffer mutum-mutumin kwarkwasa.
Manyan gobe ina mawaƙa na baka masaƙa,
Masoyan keɓe makirkira marubuta dukka,
Madubin keɓe ‘yan fim da masu dirama barka,
Ku ji ni a keɓe wai shin ina mafita kan harka,
Duk kun rarrabe kun bar su kowa yana ingausa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.