Ticker

6/recent/ticker-posts

Budaddiyar Wasika

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Buɗaɗɗiyar wasiƙata ga shugaban ƙasarmu ‘yan Nijeriya.

Buɗaɗɗiyar wasiƙa ce ga shugaban ƙasarmu ‘yan Nijeriya.

 

Nai dogaro da Sarkina mai warware dukkan sarƙaƙiya,

Kamun ƙafa da Sarkina mai maganin dukan ƙullalliya,

Komai daren daɗewa ƙarya za ta tashi domin gaskiya,

Allahu ga ƙasata ta Uwa da Uba ƙasar Nijeriya.

 

Ofen leta nake yi a gurin shugaban ƙasar Nijeriya,

Buɗaɗɗiyar wasiƙa a gurin shugaban ƙasar Nijeriya,

Bayan dubun dubatar gaisuwa a gunka shugaban Nijeriya,

Zan ma bugun misalai daga shuwagabannin ƙasashen duniya.

 

Mulki na al’umma ne sannan daga al’ummar duka duniya,

Demokaraɗiya ne mulki daga al’umar duk duniya,

Ku zaɓi shugabanku zaɓin jama’a ta hanyar gaskiya,

Da yai kure ya sauƙa in ya kuskurewa tsarin gaskiya.

 

A rukunin misalai farko na sako maduban duniya,

Waɗan da dan nagarta suka sauka saboda mulkin danniya,

Masalahar mutane ta saka su su sauka ba ko tankiya,

Dan kishin jama’arsu domin kar a ce da su ‘yan murɗiya.

 

Amerikan firesident Jonson yai gwadi na halin gaskiya,

A shekara ta etin sisti et ya zamo abin ai kwaikwaya,

An yunƙurin cire shi wai a saɓa halinsa nan na mazan jiya,

Jonson kawai ya sauka dan masalaha ta al’uma jiya.

 

Sai Jamani firesident Kiristan Wofena mazan jiya,

A shekara ta tu sauzan tuwelf Fabarairu in yi matashiya,

Rikicin siyasa ya saka shi ya sauka ba wata turjiya,

Masalahar mutane da gudu na zargin mulkin danniya.

 

US Firesdent Richard Neɗon abin ai fariya,

A shekara ta nayintin sabinti fo dan in ɗan baka matashiya,

Gunagunin siyasa ya saka shi ya sauka ba wata tankiya,

Masalahar mutane ba a zub da jini ba ko fa na tinkiya.

 

Zic Firayin minista Fitnikas a zubi na ba ka matashiya,

Tu sauzan satin ya aje ragamarsa babu hatsaniya,

Rashawa da hanci ya saka shi ya sauka babu hatsaniya,

Masalahar mutane ba a zub da jini ko fa na gaffiya.

 

Hungry firesident tu sauzan tuwelf in ba ka matashiya,

Sunan sa Folek Chamik Ekzam malfuraktis ya yo fa a tin jiya,

Ya yi a kan furojet da ake da zato kamar ya yo wankiya,

Shi ya saka ya sauka dan ƙarfafa ai matakan gaskiya.

 

A shekara ta tu sauzan fotin mun ji Sauzan Koriya,

Shugaban ƙasarsu yai murabus saboda jin kunya jiya,

Jirgin ruwa da kaya da mutane ya nutse fa a Maliya,

Masalahar mutane sai ya sauka saboda jin kunya jiya.

 

Ya shugan ƙasa ta mai girmama demokaraɗiya,

Har fisful demostirashin mun yi a baya kan hanya jiya,

Mun nuna kar a janye sufsidi baya ka yi jayayya jiya,

Wasunmu sun mace a cikin rana kai ko ka ƙi dubayya jiya.

 

An yi shirin a haɗu Kaduna a je birni na tarayya,

Rana ta ashirin ga wata na Janairu ka ɗan yi dubayya jiya,

A shekarar dubu biyu da sha biyu in yi ma ka tariya,

Mun wartsake da tashin bama-bamai sai ka ce gari na Somaliya.

Daga nan fa yajin aiki aka bar shi babu hatsaniya,

Aka sanya dokar ta-ɓaci ko’ina a kan hanya jiya,

Jami’an tsaro suka yo tsinke ko ina ka duba hanya,

Ya isar dalili na murabus mulkin siyasar gaskiya.

 

 

 

Yuwa ekselensi mai girma lamba wan Nijeriya,

A jaha ta Yobe a Potiskum an yo fa hatsaniya,

A jahar ta Yobe Buni Yadi ankaron ƙullalliya,

A unguwa ta Shanu jinin jama’a fa ya bi ta rariya.

 

Yuwa ekselensi sa mai girma lokacin jamhuriya,

Ka tuno da Borno a Bama fa an biki na hatsaniya,

A Sambisa fores a nan ma fa an shirin sarƙaƙiya,

Batu gami da mata na Cibok ya zamo kamar tatsuniya.

 

Yuwa ekselensi sa Afirka kamar ƙasar Nijeriya,

A ce a sace mata ɗari biyu har da ma ‘yan ɗoriya,

Wata biyu da motsi har iyau kwanaki fa ba wata ɗuriya,

Kai ko kana zaune matsayin shugaba na ‘yan Nijeriya.

 

Yuwa ekselensi sa Kaduna zan ko ɗan dawaya,

Kafancen Kaduna gwanin goro sun buga sun turjiya,

Kaduna santaral ma an tashi bama-bamai ba ƙirgiya,

Kana Abuja zaune matsayinka na shugaban Nijeriya.

 

Yuwa ekselensi sa Filato a Taminos an gauraya,

Haka Dogo Nahauwa da Barikin Ladi duk an gauraya,

Kuru-kuru gada biyu an zub da jini bare ma karaya,

Kai ko kana Abuja a kan karagar ƙasar Nijeriya.

 

Yuwa ekselensi sa Abuja hedikwatar Nijeriya,

Hedikwata ta polis an tashi bama-bamai ba ƙarya,

An sanya bom a Nyanya an zub da jini na ‘yan Nijeriya,

Kana Abuja zaune bisa kan karagar Uban Nijeriya.

 

Mulki ake wa rumfa koko mulkin mutane,

Wal wayis ni ma ko kuma tsarin mutane,

Militiri ka ke yi ko kuma mulkiya ne,

Falimantari ne ko demokaraɗiya ne.

 

 

 

Falimantari ne,

Ya kyautu ka sauka Nijeriya.

 

Ko minisanci ne,

Ya dace ka sauka Nijeriya.

 

Gurguzu ka ke yi,

Ya kyautu ka sauka Nijeriya.

 

In mulukiya ne,

Ya kyautu ka sauka Nijeriya.

 

Militiri kake yi,

Ya kyautu ka sauka Nijeriya.

 

Demokaraɗiya ne,

Tintini sai ka sauka Nijeriya.

 

Mulki na al’umma ne,

Kuma zaɓin na al’umma ne.

 

Zaɓi na al’umma ne,

In kana so ka ce kana kan gaskiya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments