Ticker

6/recent/ticker-posts

Sakarkari

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa:

Eehhh, ya jama’ar Rasullla,

Ya ɗaukacin ibadulla,

Mu ƙanƙame ibadulla,

Mu riƙe ulamaulla,

Su za su zamanto fitila,

Tsanin zuwa wurin Alalh,

Da dausayin Rasulilla,

Mai sadarwa zuwa falala.

 

Amshi:

Irin riƙon sakainar kashi da ake wa malamai ibadulla,

Muke ta kira ga jama’a da su ƙaurace wa fushin Allah.

 

Na yi addu’a guns Sarki mai iko na busa numfashi,

Allah Ubangiji tsare Alan waƙa da ganin abin haushi,

In na yi gamo gamon baiwa Allah ka tsare ni ban kashi.

 

Salati sallu alaihi nabiyuna shugaban maja salla,

Muhammadu Hamidun Mahamudu Ahmadu umaidulla,

Mai tambarin yabo Muhammadu ɗan Amina da Abdulla.

 

 

 

Irin ginin sakarkarun da na ambata a fa baitukan baya,

Za ni warwar in tsefe inda ya zamma akwai hatsaniyya,

In since ɗaurin gwaurai da ya addabi masu son Ala.

 

Kalmar sakarkari fa kalma ce da ta zo a can baya,

Wanda take nufin banɗaki inda akan yi bahayya,

Yadda ake ginin banɗakin nay yi kwatanci walla.

 

Shi sakarkari ana gina shi a ƙauye guda ibadulla,

Sannan a tsuke babu rufin kirki balle daɗe walla,

Duk da fa fa’idodinsa an sani ba mai musu walla.

 

Idan da akwai mutum mai inkari ya taho ya saurara,

Shi sakarkari fa ɗaki ne tilo a cikin gida lura,

Dukkan jama’ar gidan nan kowa zai zo ya sauwaƙe wahala.

 

Idan ka ga mai gida ya fuɗɗuke domin lalurarsa,

To ba shi da inda zai je ya kintsa domin buƙatarsa,

Sai dai sakarkari banɗakin nan da nake faɗi walla.

 

Idan fa uwargida ta yi daƙal-daƙal malam in shaida ma,

Can za ta je tai adon hilatar miji don kar yai ƙyama,

Nan ne matattarar kintsi ko ya ka ce ibadulla.

 

Idan ka ga saurayi ya yi ado yana tafiya yana ƙobo,

Ko ka ga ‘yar budurwa tana layi rishi tana ƙwambo,

Sai da ta kai ziyara sakarkari ta fito ibadulla.

 

A ranar ban kwananka ga duniya ya bini abdulla,

Ɗakin shigar ka rannan sakarkari ka sani fa abdalla,

Nan za a maka wankan gawa ai suttura a ma salla.

 

Duk da dubun dubata na darraja da na wassafa walla,

Wacce sakarkari yai ɗarɗara wa ga ɗakuna walla,

Mun banzartar da shi ba alkintawa babu kula walla.

 

 

Idan haka nai kwatanci da malamai tsofaffi mu duk falala,

Komai da su muke tinƙaho in babu su akwai illa,

Mun mai da su kamar jujin shara kaico ibadulla.

 

Mu malamai a nan ƙasar Hausa ba a yarda da su su hau mota,

Koko su yi ginin nan na zamani ko su auri ‘yan mata,

Ka ji ana faɗin ba Allah ransu suna da wai illia.

 

Malami a nan ƙasar Hausa ko kari ba a so a wa hula,

Ka ji ana budurwar zuciya ce da shi ibadulla,

Kaico da wagga halayya mai cutar da mu ibadulla.

 

Su ya kamata su yi ado da shigar girma ibadulla,

Su ya kyautu su hau mota na ƙawa nazari ibadulla,

Sun gida na alfarma ba kai ba dalogaji gaula.

 

Duk janhuriyoyi nake ta ririka ka sha kallo,

Duk wata nayi nan ta duniya leƙa ka sha kallo,

Malamai ake regarding da kyautata da karrama walla.

 

Al’ulama’u wasatil ambiya’i fa ya ibadalla,

Malamai fa magada ga annabawa ku duba duk falala,

Amma muna riƙon sakarnar kashi gare su don illa.

 

Malamai na Islamic da zamani boko sanin Hausa,

Su na yi wa kuɗin goro ɗokacinsu na nahiyar Hausa,

Don Allah jama’a mu yi hankali kar mu mai da su bola.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments