Amshi:
Rayuwa a duniya tana ban tsoro,
Lamarin duniya rawan ‘yanmata,
Da farko ka tashi ne kana ɗan yaro,
Duk wani motsinka za ta yi masa wairo,
Sai a yi maka tarbiya cikakken gwauro,
Ka gane abinda duk da kai da kyau dana tsoro,
Ka tashi da ƙarfin ƙuriciya ɗan yaro,
Ba aikin ƙwarai bare ka wahalta.
Larurarka gaba ɗaya ake ɗaukar ta,
Ba ka abinci da sutura ka tufata,
A ɗora ka a turbar sani makaranta,
In ba ka da lafiya a kai ka ga likita,
Muhallin kwancinka ya zamo mai tsabta,
A ba ka kulawa mafi nagartar tsabta.
Watan watara a tashi bakai ne ba,
An sami waninka yanzu shi aka duba,
Ba a mararinka yanzu sai ɗan baba,
Ka kama tudun hawa uba ɗan baba,
Ka zama mai yunƙurin zamowa baba,
Sha’anin duniya rawar ‘yan mata.
Da ka taka munzali na isa aure,
A ɗan ƙuƙuta da ‘yan uwanka a daure,
A sama maka ‘yar budurwarka ta aure,
Aure fa sha’aninsa sai an daddaure,
Sai an jure riƙe amanar aure,
A bar ka da yau da gobe ɗan tatata.
Daga nan sai tsufa ta fara shiga ba ciwo,
Abinda da kake yi a yanzu bashi yiwo,
Baka tafiya ta nesa balle yawo,
Da kai tafiya ‘yar kaɗan jiki yai ciwo,
Babu kataɓus a gunka ka zama wauro,
Ka zama sai dai ka ci abinci ka kwanta.
Fuskarka buzu-buzu da gashin girma,
Kana nan sai furfura ta bayyana ita ma,
Ko tsayuwa in ka yo jiki na kyarma,
Zama kwance tsayuwarka duk ba dama,
Fata ta jikinka ta sake ga rama,
Ruwan ɓargon jikinka ya nakasata.
Anan lafiya yau ta gobe da dama,
A yau ciwo a hagun ka gobe a dama,
Kallon nesa gunka yanzu ba dama,
Zance in an yi sai a maimaita ma,
Abinci cikin hikima ka ɗan laluma,
Sannan ka haɗiye ka ɗan kikkifta.
A sannu zuwa hankali komai sai an ma,
Abinda ke wa jinjiri yanzu ake ma,
Ya zam ko kashi ka yi sai an wankema,
Jimɓintar lamuranka har su da zama,
Mai ƙarfi da ƙuriciya ya koma,
Rarrauna mar rashin lago na buƙata.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.