Ticker

6/recent/ticker-posts

Marainiya

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Duniya mai yayi mai abin ban tsoro,

Haihuwar guzuma ɗa uwa a kwance,

Habawa ai idan yau mu ne gobe ba mu ne ba,

Gobe ba mu ne ba,

Gobe ba mu ne ba.

 

Duba duba Aminu,

Alan waƙa,

Abin ban tausai,

Gidan marayun yara.

 

Kaliƙin talikkai,

Rabbi sarkin tausai,

Sarki na sarakai,

Rabbu sarkin jin ƙai,

Wanda jiji da kai,

Yake a gunsa maji ƙai,

Nai nufin waƙa tallafe ni kar nai kwaɓa.

 

Rabbana yi salati addadi su fi dubbai,

Gun mai girman al’umma da ke da sahabbai,

Sayyadin gwanin karkato mabauta baibai,

Ɗan Amina abin ambato da ba aibi ba.

 

Yau akala na karkata ga rainon yara,

Lokacinda na je ni ziyara domin yara,

Da abin ban tausai jiki ya kama kyarkyara,

Tsarraba zan ko za a tausaya wa yara.

 

Abin ban tausai gidan marayun yara,

Abin ai kaico hawaye sui ta darara,

Abin tsuma rai dagwai-dagwai ‘yan yara,

Wasu haɗarin mota akay yi suka zama rara,

Wasu ko tsinto su a kai a cikkin shara,

Wasu ko masu taɓin hankali ka haifa yara,

Sababi na haɗakarsu ba shi irgo yara,

Wasu ‘yan jarirai a kan gadonsu na yara,

Wasu na tatata da rarrafe ‘yan yara,

Wasu na makarantar karatun firamara,

Wasu an kakkai can sakandare don kara,

Ba uwa babu uba haɗin gamayyar yara,

Komi ɗaya amma kamarsu bamban yara,

Wani na zaluntar na ƙasa da shi dan ƙwara,

Wani jarumta wanni shaggwaɓa ‘yan yara,

Wani ba ƙoshin lafiya cikin ‘yan yara,

Wasu ko ƙoshin lafiya kamar tattabara,

Abinci idan za a ba su tamkar fara,

Jerin gwano suke kamar masu bara,

Gidansu matsattse sai ka ce tattabara,

Gidansu guda ɗaya jal ku je ku yi duba.

 

Sai naj ji hawaye yana ɗosowa dodo,

Da irin maƙudan kuɗinda ba kirdado,

Na ji raina ya tirniƙe ina fargaba.

 

Na tino filin ƙwallon ƙafa na tamola,

Na tino maƙudan kuɗinda anka malala,

Na tuno kuɗaɗen jama’a da ke zuba wa tamola,

Zuciyata ta harziƙe kamar ba ni ba.

 

Na tuno makaranta ta nakkasassun bayi,

Inda kurma ko gurgu a can duka kan yi,

Gaɓo har masu tawwaya duka kan yi,

Ilimin zamani a gun fa sai ka duba.

 

Makaranta tilo guda ɗaya jal duba,

Sai naj ji takaici na kama duba-duba,

Sai nay yi aniyar za ni in yi duba-duba,

Da wainar toya waɗansu ya saba ba.

 

 

 

Tun da na je ni gidan marayu an yo duba,

Kuma na je ni gidan mahaukata na duba,

Na je assibitin Kaduna duba,

Kuma za ni gidan ‘yan siyasa in yo duba.

 

Yau tsarabar duk abinda ni na nazarta,

Ku yo nazarin hankali ku zo a kwatanta,

Sa’an nan ma san abinda zai zam mafita,

Allahu ka ban izzini na yo ba zamba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)


Post a Comment

0 Comments