Ticker

6/recent/ticker-posts

Maɗaci

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amashi:

Wani ya sha zuma wani ya sha maɗaci,

Daɗa wai me ya faru ne akan harshe na?

Na ji ɗaci na maɗaciyar dake a cikina.

 

Mabuwayi dake ta sarrafin ruhina,

Rabbi ka san abin cikin ruhina,

Mallaka min zuciya ta bar ruɗina,

Sarrafa min ita ta daina min karakaina.

 

Babu ƙwari cikin jiki da gaɓɓoɓina

Ga ƙafata ta gagara ta ɗauki jikina,

Ga jiri na galauniya da dukka jikina,

Sai hawaye yake ta bibiyar kuncina.

 

Babu daɗi idan na ba ku labarana,

Ba ni fatar gari ya wartsake ni kaina,

Na fi burin shigar dare cikin ruhina,

Duk da barci fa ba shi samu a idona.

 

Na fi burin ana ruwa cikindamina,

In tsaya a ruwan sama yana duka na,

Ya jiƙa ni ta ko’ina jikin jasadina,

Babu mai gane ko akwai hawaye idona.

 

Nai gamo wanda ya rugurguzan lamurana,

Da maɗaci da ma zuma duka ɗaya guna,

Ba nishaɗi a kan zuciya da fuskana,

Wasiwasi ya auri zuciya a gurina.

 

Na ɗauko abinci za ni in ci da kaina,

Sai tunani ya baibaye mini duka kaina,

Tuni kallon ƙuda ya birkice wa idona,

Sai hawaye yake ɗisa yana karakaina.

 

Haka nan in ya jijjiga in karkaɗa kaina,

Kuma sai in yi ajjiya ta numfashina,

Daɗa sai in yi shashshaƙa da numfashina,

Kuma sai ɓulɓular hawaye duk a idona.

 

Nai rashin ɗanɗano dukansa kan harshena,

Zuciyata dulum-dulum gami da idona,

Gashi barci ya ƙaurace tuni a idona,

Ga abinci ba ɗanɗano a kan harshena.

 

Ga karatu na zamani a zanƙama guna,

Ga ababen hawa kal- kala a gurina,

Ga gidajen ƙawa na zamani nan guna,

Ga kuɗi ga dala da fam stalin guna.

 

Inda duk na wuce ana ta duddubi na,

Jama’a na ta sha’awa a kan lamurana,

A cikin zuci sai tafarfasa zucina,

Ba sukuni dulu- dulum cikin ruhina.

 

Ko’ina taku har nakan jiyo sautina,

Ko’ina tafiya ina ta sanbatuna,

Ɗan uwa kar na je na ba ku labarina,

Wani zai zautu in na bada labarina.

 

Ɗan uwa na rufe ku dukka labarina,

Wata tsoka guda cikin jiki dangina,

In ta gyaru dukkan jiki fa zai amfana,

In ta ɓaci jiki da gaɓɓuna sun ƙuna.

3.6 Maɗaci- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 53)


Post a Comment

0 Comments