Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Ilimi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Ku nemi illimi fitilar haskawa,

Illimi fitilar ƙyallawa,

Illimi gwadaɓen haurewa,

Hanyar ɓullewa.

 

Ku nemi illimi gwadabɓen ɗorewa,

Ku nemi illimi alfaharin kowa,

Illimi dan kowa.

 

Ku nemi illimi fitilar haskwa,

Ko wanda bai gani ma na hangowa.

 

Haske na illimi ba ya nashewa,

Ko wanda bai gani ma na hangowa.

 

Hasken da ko’ina shi ke ƙyallawa,

Ko wanda bai gani ma na hangowa.

Ko wanda bai gani na fuskantowa,

 

Duhun rashin sani ya zarce faɗowa,

Wane duhun dare gun siffantawa.

 

Kife adon batu ƙul haƙƙu nawa,

Ciki da gaskiya ba ya hujewa.

 

Wadatuwa ta zuci babbar yalwa,

Ku nemi illimi suturar sanyawa.

 

Kwaɗai da zuciya shi ke hallakarwa,

Ku nemi illimi suturar sanyawa.

 

Ado na mumini tsoron mai kowa,

Ku nemi illimi suturar sanyawa.

 

 

Tsoron buwayi sutura ce mai yalwa.

Aiki da hankali hanyar ɓullewa,

Aiki da ra’ayi lallai shi ka ɓoluwa,

Komai tsawon dare za shi yi wayewa,

Komai tsawon gari sai an yi iskewa.

 

Ga yau da gobe karya mai cin kowa,

A kwan a tashi mai kai ƙarshen kowa.

 

A kwan a tashi sai ta isko kowa,

A kwan a tashi mai kai ƙarshen kowa.

 

Gudu da waiwaye ba ya tsirarwa,

A kwan a tashi mai kai ƙarshen kowa.

 

Waƙar gatsai anai fa da nanatawa.

 

Allah mun riƙe ka linzaminmu,

Mai tasarrafin lamurran kowa,

Allah kaz zamo fa gatan kowa,

Rami ko koke-koken kowa.

 

Ga yau da gobe karya mai iya cin kowa,

A kwan a tashi sai ta isko kowa.

 

Gudu da waiwaye ba ya tsirarwa,

Waƙar gatse anai fa da nanatawa.

 

Aya abin ƙasa dutsen tawa,

Abinda anka shuka ke girbewa.

 

Na gai da ɗan Adam sarkin mantawa,

Abinda anka shuka ke girbewa.

 

Don me ake zubindashen tarawa?

Abinda anka shuka ke girbewa.

 

Ran biyan buƙata ai gamsarwa,

 

Hassada ga mai rabo takin shukawa,

Ɗaukaka abar yabo Allah ke baiwa,

Gaskiya abar yabo tsanin haurewa,

Ƙarya mahallakar mai ita ganewa.

 

Da rai da rayuwa aka fafatawa,

Ɗayan biyun ga in ba ku ba kowa,

 

Baki na rayuwa bakin aunawa,

Yau ga mu nan muna nunnunfasawa.

 

Na shirya baituka ga ni da rerawa,

Alan Kano fa mai waƙar faɗakarwa.

 

A kwan a tashi sai sautin nan nawa,

Alan Kano fa mai waƙar faɗakarwa.

 

Ni daɗa na tafi na zam gawa,

Alan Kano fa mai waƙar faɗakarwa.

 

Sai ni fa sai abinda na aikatawa.

 

Kaico!

Tuba nake wurin wanda na saɓawa,

Kui affuwa garen wanda na cutarwa,

Ga shi ni nake labarun kowa,

Kuma gobe ni ake iya labartawa.

 

Alanku ne da ke waƙar faɗɗakarwa,

Alan Kano fa mai waƙar faɗakarwa.

 

Bulaliyarsa na duka kan kowa,

Alan Kano fa mai waƙar faɗakarwa.

 

 

Harshe da kansa ma ba ta ƙyalewa,

Alan Kano fa mai waƙar faɗakarwa.

 

Fatanmu kattari ranar dacewa.

 

Ya Rabbana ka dube mu,

Ya Rabbana ka dube mu.

 

Ya Rabbana ka cece mu,

Ya Rabbana ka cece mu.

 

Ya Allahu Rabbana Allah mun tuba,

Allahu Rabbana Allah mun tuba.

 

Ya Allahu Rabbana Allah mun tuba,

Allahu Rabbana Allah mun tuba.

 

Allah na tuba,

Mu ma mun tuba,

Sarki na tuba,

Mai duka mun tuba.

3.5 Waƙar Ilimi- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 50)


Post a Comment

0 Comments