Ticker

6/recent/ticker-posts

Baba Ina Za Ka Ne?

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Baba ina za ka ne

Mulki an yi an gama yanzu,

Yanzu gida za ni in zauna da ‘yan uwa.

 

Na tuna sanda muka kammala mulki a tenuwa,

Mu kai handing oɓer fuskoki ba bu damuwa,

Babu kwatankwacinmu tsaf a jiki namu nutsuwa,

Ko ƙyas ko ƙyaras zukatanmu fa babu damuwa.

 

Lotan nan idan ka gan ni fa zan ba ka sha’awa,

Komai na a can a can sutura ta ganin ƙawa,

Ga kadara a ko’ina filaye kwa day yawa,

Sannan ga gida na kwanci na ya yi unguwa.

 

Ga tsirrai cikin furanni sa ba ka sha’awa,

Sannan ga ma’aikatan hidima sun yi min yawa,

Ga mai ar ruwa na shuka ga mai dahuwa,

Ga mai wanke suttura ga mai tuƙa tsohuwa.

 

Sannan ga direba nawa na kai na a nutsuwa,

Sannan ga direba mai kai yara school tuwa,

Sannan ga direba mai kai mata fa unguwa,

Motoci kala-kala har da ta haura sakuwa.

 

Kowanne mako uku mai fanti yana zuwa,

Ya sabunta fante-tante a waje da ɗakukuwa,

Sannan masu ɗammara na bi na da zaƙƙuwa,

Ko tsuntsu ya wulkita zai baƙunci muttuwa.

 

Sannan shekaru fa sun ja tsufa yana zuwa,

Boko ya hana ni auren wuri dan ɗimuwa,

‘Yan yara dagwai-dagwai babu guda na garkuwa,

Ga saƙo na mutuwa tsufa ya yi garkuwa.

 

 

Ban kula ba da dukka eɗpensiɓe ya yi min yawa,

Albashi na ma’aikata da yawa ya yi min yawa,

Sannan ga kuɗin school fees yara yana yawa,

Na manta a yanzu income kuma ba sa zuwa.

 

Sannu a kan a hankali tunani yana yawa,

Sannan ga yawan larurori sun yi min yawa,

Sanda na je gwajin jini aka ce ya hauhawa,

Ga tari ina ta yi sannu yana ta daɗɗuwa.

 

Nai maza nai yi firgigit naddawo da nutsuwa,

Nai farga irin ta fargar jaji da makkuwa,

Ɗan sauran kuɗinda kadarori sun yi ragguwa,

Sai nan nemi yin sana’a na kama tsasuwa.

 

Duk sana’ar da nai yi ba riba ba batun uwa,

Inda na sa ƙafa duka ba sa a yi beguwa,

Kai kafin in ankara komai nau ya bi ruwa,

Kwance a tashi masu aikin masa zuwa.

 

Sannu a hankali furanni sai bubbushewa,

Ga fantin jikin gidana na ɓaɓɓarowa,

Gidan ya yi min yawa hidima tai akwai yawa,

Ga bidi okshoniya nai gwanjan abubuwa.

 

An ce maluwal ba nuni a duniya yake ƙawa,

Ga ya yi da dukiya yau sun zam baƙar ƙawa,

Cuta ci take kuɗi kullum na rage yawa,

Har na fara sai da kadarorin nan fa mai yawa.

 

Raina ya dugunzuma in na je ni wucewa,

Zunɗena kawai ake wasu ma na mini shewa,

Ga ni ina ta taffiya ba comboy na garkuwa,

Sannan babu jiniya taken gani nan zuwa.

 

 

 

Da inna wuce a titi ka ga ɗaga hannuwa,

Ba mai damuwa da amsawa ta da kulawa,

Yanzu ko babu mai kula wa wane yake zuwa,

Sai ma in an kula ganewa ga tahowa.

 

Ko tafiya nake ta yi wayige ya yi min yawa,

Waige ne na tsarguwa ya hana mini nutsuwa,

Dukkanin majalissa na wuce zan yi tsarguwa,

Zunɗena kawai suke su nai mini daƙƙuwa.

 

Bayan shekara takwas sauka ta da mulkawa,

Ba sauran abokanan gaba sai a ‘yan’uwa,

‘Ya’yana da masu aurena na ta zaƙƙuwa,

Kullum ba ni lafiya gara a kai ni kushewa.

 

Cuttata kala uku ba waraka ba muttuwa,

Ga cutar hawan jini ta saka sashe muttuwa,

Sannan ga dayabitis ga tibi yana zuwa,

In na sai da kaddara kan sati fa ba uwa.

 

Ƙarshe dai in ba ku labari kun ji ‘yan uwa,

An hana kai ni hospital an girke ni ƙoƙuwa,

Kullum magani na Hausawa anka jiƙawa,

Dan alkinta ƙaddara kar na mace su yi kuwa.

 

Wannan shi ya sa na ɗau waraka ta nake yi wa,

Dangi ‘yan uwa nasiha kan wagga rayuwa,

Saƙon nan a kai wa Alan Waƙa na Kanawa,

Ga saƙo ya issuwa masoya da ‘yan uwa.

 

Mai aure da duniya kai aniyar shirin hawa,

Hawa goɗiya da siddi fili na sukkuwa,

Ba ta gwani a sukkuwa ko kai ne gwanin hawa,

Sanda ta tashi yar da kai sai ta kai ka ƙoluwa.

3.4 Baba Ina Za Ka Ne?- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 47)


Post a Comment

0 Comments