Ticker

6/recent/ticker-posts

Rukunin Shahara Tsantsa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

Rukuni a cikin rukunnaiii,

Rukunin shahara fa tsantsa.

 

Rukuni na uku jawabi,

Lamarin shahara fa tsantsa.

 

Amshi

Shahara ce ussulibin,

Ilimi yas samu tsantsa.

 

Atafau godewa Allah,

Wajibi ne a gurina.

 

Haka komai za na fara,

Sai na ambaci Kaliƙina.

 

Hakaza in za ni kulle,

Na rufe da Mamallakina.

 

Shi ya sa ni ka sam ƙabuli,

Falala tai ta gudana.

 

Rukuni a cikin rukunnai,

Na uku zan yo bayana.

 

Fari kun ji su salsalata,

Da kaɗan a gwagwarmayana.

 

Yanzu za ni wuce bayani,

Shahara tsantsar bayana.

 

Bi ni sannu gami da lura,

Bisa tsinkayar batuna.

 

Na zamo tsuntsu bicilmi,

Damina ke ɓanna ƙwaina.

 

Na zamma dari a tsuntsu,

Dole sai fa a ƙyale ƙwaina.

 

Idan na hau keke na tuƙa,

Sai a ce ga wane rana.

 

In na hau mota da tsada,

Sai a ce alfahharina.

 

Ko’ina sai dai na ɓuya,

Sai ka ce cuta na auna.

 

Ko a mota sai da tintek,

Don in bad da kamannina.

 

Rabbu na gode Wahabu,

Yarda duk ka yi babu ɓarna.

 

Ni’ima ce wacce kab ban,

Ka taya ni riƙon abina.

 

Lokacin da kafar karatu,

Suka fara nazar a kaina.

 

Wasu na ta shirin asamen,

Da furojek duk a kaina.

 

Wasu na gayyar ziyara,

Makon Hausa da ni na.

 

Wasu na tsari na Ƙuestion,

And answer duk a kaina.

 

 

Su tsayar ni su tambaye ni,

Aikin da na yo da kaina.

 

Inda na burge su nuna,

Inda nay yi kure su nuna.

 

Makarantu na kwaleji,

Ka haɗa har jami’una.

 

Kuma sai suka tsirri ba ni,

Kwalaye da alluna.

 

Alami don karramawa,

Shaida aikin yabona.

 

Wasu katakon kafewa,

Wasu satifiket yabona.

 

A.T.C. can a Gumel,

Sun ba ni adon yabona.

 

Har Mamba sun ka sa ni,

Ƙungiyar nazari harshena.

 

A.T.C. ta Jigawa,

Sun karrama ayyukana.

 

Har Bahharu sun ka ba ni,

Baharin waƙa sunana.

 

F.C.E. ta Kanawa,

Sun ɗabbaƙa ayyukana.

 

Satifiket sun ka ba ni,

Da allo na gurina.

 

 

Ƙungiyar ulama’u jimla,

Na ƙasa karkaf! Garina.

 

Ulama’un F.C.E,

Sun bincika ayyukana.

 

Har shaida sun ka ba ni,

Don tallata addabina.

 

Kumbotso Kwalej Sa’ade,

Sun shaidar ayyukana.

 

Mako sun gayyace ni,

Sun karrama ayyukana.

 

Ligal Islam Studies,

Sun ban allo na kaina.

 

Kwalejin Zazzagawa,

Sun ba ni a kan yabona.

 

Science School ta mata,

Ta Garko suna yabona.

 

A Kawaji maza da mata,

Sun karrama ayyukana.

 

Jami’ar Usumanu Fodiy-

Yo jakada sun ka zana.

 

Jami’ar Bayero Kano,

Na sam shedar yabona.

 

ABU Zariya ma,

Sun ban kwalin yabona.

 

 

Ƙungiyoyin masu waƙa,

Sun ban kwalin yabona.

 

Ƙungiyoyin marrubuta,

Sun ban allon yabona.

 

Da ganin haka sai kalaman,

Suka suka taru kaina.

 

Aka ce biko nake yi,

Na a karrama ayyukana.

 

Cin hanci nikka baiwa,

Don a karramawa ayyukana.

 

Ga furofesas da doktos,

Na nunan so da ƙauna.

 

Haka waƙoƙin yabonsu,

Cin hanci ne da kaina.

 

Ga muƙaloli suna yi,

Don martaba kallamina.

 

Wasu har a cikin kitabu,

Suka masalan da batuna.

 

Wasu na saka a yi asament,

Da project duk batuna.

 

Ƙadiran ALA man yasha’u,

Masanin al’amarina.

 

Na gode ma Ilahu,

Masanin al’ammarina.

 

 

Na faɗi a jakadiyata,

Nai isharori da dama.

 

Wanda yan nufi birge kowa,

Ya zamo tamkar jununa.

 

Babu hauka sai ga wanda,

Zai game kowa da ƙauna.

 

In ka je wani yai du’a’i,

Gobe sai wani yai la’anna.

 

Wani har da kuɗi ya ba ka,

Har ya so ya kira ka ɗana.

 

Wani in ka yi ka ci duka,

Kuma kurkuku za ka kwana.

 

Komai nisa na jifa,

Za ya sauka ƙasa ya zauna.

 

Kwanci tashi a kwan a tashi,

Za a kwan wata rana fana.

 

Lamari na Ubanjinmu,

Yarda yai duka babu ɓarna.

 

Dukka yarda ya so ya gan ka,

Tahamida kai da gunna.

 

In ka gan ka da ‘yan adawa,

Da akwai manufa ka tona.

 

In ka gan ka cikin uƙuba,

Bincika da akwai bayana.

 

 

Dukkan lamarin da kay yo,

Nazari a ciki ka kwana.

 

Ka yi taf ka nutsu ka duba,

Kwan a tashi akwai bayana.

 

Sanadi na mu’amaloli,

Da yawa da ya faru kaina.

 

Ya saka ni zama fasihi,

Da fallasafa a kaina.

 

Na rabe kore da shuɗi,

Har zabibi da zabina.

 

Randa duk falala ta zo min,

Jama’a sai sui ta bi na.

 

Randa duk na shige bala’i,

Sai in rarrabe masu so na.

 

Na tuno da wata na Yuli,

Da a kurkuku ni na kwana.

 

Har ila yau mai karatu,

Shahara fa nake bayana.

 

Nasabarta da ɗan mabuɗin,

Ilimi na taho in tona.

 

Ka ji yarda a kai na je ni,

Kurkuku don ƙallamina.

 

Sanadin kaifi na harshe,

Aka kai ni kaso na kwana.

 

 

Sanadin baiti na waƙa,

Shara’a na yi da garina.

 

Aka ce ALA a Kotu,

Da state gwamnan garina.

 

Sanadin rigimar ga Malan,

Ilimi ya samu guna.

 

Ran da nas shiga ɗan akwaku,

Ga lauyoyi gabana.

 

Ga alƙali a girke,

Ga ‘yan kallo a baina.

 

Karo na biyu a guna,

Shiga kotu bayana.

 

Na san dai mai karatu,

Zai so sanadin zuwana.

 

Zai so ya ji me ya sa nai,

Waƙar da ta kai ni rana.

 

Farkon farin bayana,

Censoship ta garina.

 

Sabon director ya zo,

Zai garanbawul na ɓarna.

 

Rukunin adabi na Hausa,

Waƙa, fim, katibaina.

 

Aka ƙwalla kira na shela,

Da mawaƙa za a gana.

 

 

Censorship ta Kanawa,

Da mawaƙan zamanina.

 

Aka shirya zaman musamman,

Ga mawaƙa za a izna.

 

Aka rarraba inbateshan,

Aka kai ofis gurina.

 

Ƙarfe goma na safe,

Daidai na sammi kaina.

 

A muhallin tanadinmu,

Don za mu fahimci juna.

 

Taron ya sam halartar,

Manyanmu zuwa ƙanana.

 

Ƙarfe goma na safe,

Shi ne loton mu gana.

 

An fara tafi da taro,

Sha biyu daidai na rana.

 

Darakta da ya zo shi,

Sai kawai ya haye bayana.

 

Manufofi na matata,

Censorship duk ya zana.

 

Ya doshi kusan awa biyu,

Da bayani nazarina.

 

Kiran salla da an kai,

Shi yag gutsire bayana.

 

 

Da jin haka sai ya ce to!

Mu taƙaita da bayana.

 

A zatona za ya ce duk,

Kumu amsa kiran gwanina.

 

Kumu je izuwa ga sallah,

Farali don Khaliƙina.

 

Sai ya ce mu yi tambaya ɗai,

Biyu ko uku masu ji na.

 

Mawaƙa sun yi jangwam!

Sai na ɗaga hannuwana.

 

Alamu na a ba ni,

Izini domin bayana.

 

Ina da abin da zan ce,

Tambaya zoƙar a kaina.

 

Izinin biyu an ka ba ni,

In yi za a naɗe bayana.

 

Tambayata dai ta farko,

Ta’aliƙi nai na kaina.

 

Dokokin da ya zana,

Duka Allah ne ya zana.

 

Ɗamarar Censor a kanmu,

Gyara bisa addinina.

 

Kuma mu dukkan mawaƙa,

‘Ya’ya ne duk na sunna.

 

 

‘Ya’yan Hausa Fulani,

Tarbiyyar addinina.

 

Sai na ce duka mun ji mun bi,

Dokokin Khaliƙina.

 

Sai dai ƙarin su’ali,

Me ya sa ya shugabana.

Ka ce gyaranmu za kai,

Bisa tsarin addinina.

 

Kuma ka je kai sanarwa,

A kafofin radiyona.

 

Ka ja aya hadisi,

Bisa hujjar Khaliƙina.

 

Ka ce mana ‘yan baɗala,

Yaƙi za kai da ɓarna.

 

Kuma ka san kwai shari’a,

Guda biyu a garina.

 

Akwai Majistry Court,

Akwai shari’a tunana.

 

Wanne ya ci mu a kai mu,

Final ko sharri’ana.

 

Shari’a biyu ba ta zam ni,

Ƙwarya ɗaya a idona.

 

Da wuta da ruwa ka duba,

Ka gama ƙwarya guda na.

 

 

Me ya sa wai ba a kai mu,

Shari’a Court shugabana?

 

In da laifi a gare mu,

To a nan yake shugabana.

 

A final court ba mu laifi,

A human right za ka tona.

 

Ko ya zama gyara a ɗauka,

Ko a yo ƙarin bayana.

 

Ko ka ban hujja ta Allah,

Da kuke haka shugabana.

 

Ko ya zan tambaya ka amsa,

Ko nasiha daga guna.

 

Doka ta ƙasarmu ta ce,

Duka doka ko bayana.

 

Da ta saɓawa final court,

A aje ta kawai a ɓanna.

 

Haka dokar Issilama,

Dokar Allah Gwanina.

 

Ƙalallahu Tabarah,

Faman lan yahakun bayana.

 

Man lan yahakun bima an,

Zanallahu Khaliƙina.

 

Aka ce shi fasiƙi ne,

Da faɗin Allah Gwanina.

 

 

Aka ce ma kafiri ne,

Bisa hujjar Khaliƙina.

 

Wannan ita ce su’ali,

Da na yo farkon bayana.

 

Sai kallo da gyaɗa kai,

Jimamin hankalina.

 

Sai na ce saura su’ali,

Na biyu ya shugabana.

 

Kowanmu yana da lauya,

Bisa kundi na ƙasana.

 

Haka nan kuma Sanna’armu,

A buɗe take gudana.

 

Na ga masu fashi makami,

Shari’arsu a bayyane na.

 

Haka mai fyaɗe da sata,

A opon court sun ka zauna.

 

Haka mai juyi na mulki,

A opon court sun ka zauna.

 

A tafi da gidanmu mu ko,

Shari’armu ta ce ta zauna.

 

Me ya sa haka shugabana,

Neman ƙarin bayana.

 

Rukuni na uku su’ali,

Ko kuma neman bayana.

 

 

In hukuma ta yi doka,

Wajib ta sanar a baina.

 

Ko da ta yi hanin sana’a,

Sai ta kawo maddadina.

 

Haka gwamnan lokacinnan,

Ya yi kan sufurin garina.

 

Aka ce mata da mazza,

Na gwamayya a ɓarna.

 

Aka ce mata a ware,

Motar Safararsu kana.

 

Haka ma ta maza a ware,

Don kauce shiri na ɓarna.

 

Gwamna yas sa akay yo,

Odar mota da rana.

 

Aka yi masu tassawirar,

Mata da maza a baina.

 

Aka yanke uzzurin duk,

Mai suka ko hiyana.

 

Sai na ce mu ma a yanke,

Uzuri don sharraɗi na.

 

Masalan muka so a ba mu,

Waƙa daidai da ɗina.

 

Ko bita ce a ba mu,

Ko workshop baina-baina.

 

 

Domin mu rabe abawa,

Da zare kaɗa ganina.

 

In ka ce ban iya ba,

Sai ka koya min ganina.

 

A taƙaice in ɗan gajarce,

Maka dogon sharrihina.

 

Daga nan aka gincire mu,

Ba amsa ba bayana.

 

Aka ce an sallame mu,

Za mu sam ƙarin bayana.

 

Kwana biyu an ka bi mu,

Ga sana’o’i da rana.

 

Masana’antunga namu,

Aka kukkulle da rana.

 

Kamun kaza ta kuku,

A kai wa wasu da rana.

 

Wasu an ka yi masu tara,

Ko biya ko kurkuku na.

 

Wasu tara ce da ɗauri,

Kai watanni babu kana.

 

Da ganin haka sai mu ka yi ɗif!

Ta’ajibi kan sha’ana.

 

Sai mu kai taron musamman,

Da mawaƙa ‘yan uwana.

 

 

Daga nan sai munka tashi,

Muka kai ƙara fununa.

 

Farko shari’a kwamishan,

Muka kai kuka da rana.

 

Wani mai gemu ubanmu,

Shi ya ɗora faɗin bayana.

 

Da ya tattara uzurinmu,

Sai ya ce ga shawarina.

 

Haƙuri farko in ba ku,

Kuma kui nazarin batuna.

 

Wata shari’ar in akay yi,

Maku ita sai kun yi tsina.

 

Har sai kun gwamma ce da,

Ta final court a sanina.

 

Ustazu ya hau bayanin,

Ra’ayi son zuciya na.

 

A bayanin malaminnan,

Babu zancan Khaliƙina.

 

Ba faɗin Allah da Manzo,

Da madubin zamanina.

 

Babu hujjar assahabu,

Kulafa’u da tabi’ina.

 

Babu zancen attaba’u,

Ulamu’u majinginana.

 

 

Sai musaya kaɗai ta kallon,

Junanmu da ‘yan uwana.

 

Nan mu kai sallama da MalaM,

Ba hujjar dogarona.

 

Daga nan sai filgrim board,

Gun Sani abin Yabona.

 

Sani Ƙofar Mata nawa,

Oga ne a gurina.

 

Muka ce masa an tuƙe mu,

Tura ta kai ga zana.

 

Mun yo waƙa ta ƙara,

Gun Allah Khaliƙina.

 

Hasbinallahu Wani’imal,

Wakilu abin nufina.

 

Tura ta kai mu bango,

Koke sai Khaliƙina.

 

Almudabbiru mai isarwa,

A gurin bawa kamana.

 

Sai ya ce ALA in ji shi,

Na kirayi abokanaina.

 

Shi da mu za mui yi gani,

Nassara za ta gudana.

 

Sai na tarkata ‘yan Uwana,

Da mawaƙan lokacina.

 

 

Da Producers cikinsu,

Wasu aktocin garina.

 

Wasu ma alkatibai ne,

Mu ka tattara don a gana.

 

Kowa ya zube bayani,

Dabaƙa-dabaƙa fununa.

 

Sai Sani ya ce sawa’un,

Zan maku tanyo da kaina.

 

Zan je za mui yi gani,

Ba shamaki da gwamna.

 

Sunan Jabbaru Allah,

Na riƙe a madogarana.

 

Almudabbiru Khaliƙina,

Mai yaye baƙin cikina.

Rukuni a kashi na ukku,

A cikin Shahara batuna.

 

Zan tsahirta da zango,

A muhallin mun fa gana.

 

Da Sani Lawan Gwanina,

Yai alƙawari a baina.

 

Ku biyu ni a sannu-sannuuuuuu,

Da bayani a gabbana.

 

Rukunin a cikin rukunnaiiii,

Na uku ku ka ji bayana.

 

 

Rukuni a cikin rukunnai,

Na huɗu zan je bayana.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments