Ticker

6/recent/ticker-posts

Rukunin Gwagwarmaya

Shimfiɗa

Wanga zango ne na biyuuuu,

A ciki na gwagwarmayana.

 

Godiya ga Ubangijinmuuu,

Godiya ga Ubangijinaaaa

 

Amshi

Shahara sanadin ilimmai,

Sanadin ilimi na Ala.

 

Godiya ga Ubangijinmu,

Da ya faɗaɗa saddarina.

 

Ya armasa fussuhata,

Ya tausasa laffuzana.

 

Mai Karatu kar ka manta,

Shahara na taho bayana.

 

Wanga zango ne na biyyu.

A ciki na Gwagwarmayana.

 

Kan batun waƙar siyasa,

Nai zango a batuna.

 

Nan na san jari na kaina,

Na jiɓintar lammurana.

 

Yau ina buga cidikana,

In sayar maku ‘yan uwana.

 

A iyaye na siyasa,

Ba ni manta abin yabona.

 

Sani Ƙofar Mata shi ne,

Gangaran na gaban gabana.

 

Sani har abada fa ALA,

Ba ni mantawa da ƙauna.

 

Sani ka yi abin yabawa,

Talifi ne yau na zana.

 

Na yi album na na fari,

Angara, Bubukuwana.

 

Ya fito da farin jininsa,

Har akan ce na yi ɓarna.

 

Na tuke ƙarfi a waƙa,

Na zube duka illimina.

 

Aka ce wawan mawaƙi,

Na tuke ƙarshen sanina.

 

Daga nan sai nay yi album,

Na uku Fulfulde ɗina.

 

Masu harsashe a kaina,

Sai shiru kuma ba bayana.

 

Na gaji da tunanikansu,

Da Bakan Dabon garina.

 

Sun ji ƙofofin Kanawa,

Da sarakunna na kaina.

 

Daga baya a kwan a tashi,

Na yi Lu’u-lu’u da kaina.

 

 

Fuju’a ma na sake shi,

Rayuwata ce na nuna.

 

Na yi Album Gwaddabena,

Na yabo gun ɗan Amina.

 

Shugaban farko da ƙarshen-

Mu Imamul-Mursalina.

 

Shugaban farko da ƙarshe-

Imamul Muttaƙina.

 

Shugaban farko da ƙarshe,

Imamul Raki’ina.

 

Shugaban farkon da ƙarshe,

Imamul Ɗa’i’ina.

 

Na kumo Album fa Kamfa,

Faɗakarwa ‘yan Uwana.

 

Sai na sakki Jakadiyata,

Gaisuwa ga masoyana.

 

Baya na saki Kamayye,

San Kano ya yi Sardauna.

 

Ga Mulukiyyarmu Album,

Da haɗakar baitukuna.

 

Ma’anata da Gamayyar,

Littafin baitukana.

 

In da raina za ku ji ni,

Da wasunsu anan gabana.

 

 

Allah ja nisa na kwana,

Ku ji waƙoƙi da gunna.

 

Kwanci tashi ina bayani,

Maƙasudin shuhurana.

 

Sababin ilimi na ALA,

Shuhura ku biyo bayana.

 

Za ni karkata kan bayanin,

Sanda ranta ta nuna.

 

Ku biyo ni a sannu dangi,

A gaba fa akwai bayana.

 

Waiwaye aka ce ado ne,

A fagen tafiya tunana.

 

Kun ji zangon fari dai ko,

Tarihin haihuwana.

 

Zango na biyu bayana,

Shahara da Gwagwarmayana.

 

Da ina alkatibi na,

Marubucin so da ƙauna.

 

In na wallafa ɗabba’ina,

Sai in sanya wayar kirana.

 

A jikin bangon kitabu,

Manufata ai kirana.

 

In da mai gyara ya ba ni,

Ko ko sukar ƙallamina.

 

 

In da mai ƙarin bayani,

Ko ganina ko yabona.

 

Ko ko aiki ne a ba ni,

Ga wayar tarhon gidana.

 

Haka ma a jiki na alban,

Na rubuta wayar gidana.

 

Da kwatancin dandalina,

Shabbabu kwana ta Ghana.

 

Ni buƙata ta kira ni,

In ji suka ko yabona.

 

Sannu ba ta hanna kaiwa,

Da waya ɗai ƙwal a guna.

 

Sai da yazzamto salula,

Ta fi ƙirgawa gurina.

 

Haka ma layin salula,

Duka ko wanne gurina.

 

Da ina karɓar waya ne,

Sau guda kowacce rana.

 

Ko biyu ko ukku dai duk,

Bai wuce haka dukka rana.

 

Sai ya zam dukkan ta sa’a,

A kira ni da son ganina.

 

Ya zamo dukkansa minti,

A kira ni da son ganina.

 

 

Ya zamo dukkan daƙiƙa,

Ka jiyo sautin wayana.

 

Ko a taro in na je ni,

Sai ace na kashe na zauna.

 

Ba protocol gare ni,

Babu P.A. mai biyana.

 

Ni nake karɓar bayani,

Ni nake waƙa da kaina.

 

Ni nake nazari da kaina,

Ni nake waƙar da kaina.

 

Ko saye da sayar da waƙa,

Ni nake jele da kaina.

 

Lamura sun kai jimurɗa,

Cikumurɗa lammurana.

 

Sai ƙwaƙwalwata ta kulle,

Ko da daddare ko da rana.

 

Na gaza da rubuta waƙa,

Na gaza wa masu so na.

 

Ba ni jure kira na tarho,

Ba ni jure fita da rana.

 

Hotuna fasta da kaset,

Sun karaɗe ƙasar ubana.

 

Ko a moto sai da tintek,

Don gudun neman bayana.

 

 

Babu Kura da Siyaki,

Gaba Zaki baya Ɓauna.

 

Ga kuɗi a gida da banki,

Ga masoya na biyana.

 

Kullu-yaumin babu hutu,

Ko a daji ko gidana.

 

Ba sukunin cin abinci,

Har na kan manta da kaina.

 

Sai in yini zubur da safe,

Ba kumallo ba na rana.

 

Likita yai min bushara,

Cutar yunwa jikina.

 

Wata ran sai in ta kaki,

In ta gurnani da kaina.

 

Ƙai-ƙayin kunne ya sani,

Yin hakan zan cuci kaina.

 

Da naje gun likkitana,

Don biɗar ƙarin bayana.

 

Sai ya ce na rage salula,

Kansar kunne ka bina.

 

Babu hutu a gurina,

Ko gida ko ofishina.

 

In da na tsuguna na zauna,

Jama’a na kewayona.

 

 

 

Haka sashen ‘yan uwana.

Ka haɗa da abokanaina.

 

Wasu burinsu su gan ni,

Mu yi hirar so da ƙauna.

 

Wasu ko in sun gane ni,

Sun ga samun darhamaina.

 

Makaranta nai abokai,

Da ba su faɗo a guna.

 

Haka makarantar kwaleji,

Ina da abokanaina.

 

Na yi wasa na tamaula,

Da abokaina na suna.

 

A fagen matanin hikaya,

Ina da abokanaina.

 

Na shigo harka ta waƙa,

Na shigo ta da sahibaina.

 

Ga masoya na safotas,

Masu sona ba kiyana.

 

Na gaza da biyan haƙƙinsu,

Rabbu ya san ƙuddurina.

 

Kun ji wasa fara girki,

A cikin al’ammurana.

 

Babbar matsalar gurina,

Na kusanci Mamallakana.

 

Na kusanci shuwagabanni,

Ma su mulkin duk garina.

 

Na zamo dangin Sarauta,

Masarauta na yabona.

 

Kowansu idan ya tashi,

Ya buƙata da son ganina.

 

Sa’i ɗaya za ya aika,

Ko me ni ka yi in daina.

 

Ba ruwansu da me ni ke yi,

Ko da alƙawari a kaina.

 

Babu halin in bayani,

Ko in ce ga uzzurina.

 

I remain loyal gare su,

Babu ja sai bi da ƙauna.

 

Babu damar in yi tsari,

Ko in zana jadauwalina.

 

Daga an ce ya ka ALA,

Na ji na amsa da kaina.

 

Ko mai ni ka yi a sannan,

Za ni bar shi in miƙa kaina.

 

Ba ni son saɓawa kowa,

Ba ni son aga kuskurena.

 

Kuma ba ni iyawa kowa,

Talaka da shugabana.

 

 

Ko ina in an ka gan ni,

Tambaya za ai gurina.

 

Wata ma in an ka yi ta,

Sai ta shafi mutan gidana.

 

Na zamo bawan mutane,

Babu ‘yanci ni a guna.

 

Ko ina tafe da iyali,

A tsare ni tsaka na rana.

 

Wani hoto za mu ɗauka,

Ko ko amsoshin bayana.

 

Ku biyo ni cikin jawabin,

Shuhura kogin iyona.

 

Za ku ƙaru da illimomi,

Da yawa a cikin batuna.

 

Nai karo da dubun jafa’i,

Sanadin handset ta guna.

 

Sanadin matan soyayya,

Da suke son mallakana.

 

Wasu ƙaunarsu gare ni,

Don aiki mai gudana.

 

Sanadiyyar baitukana,

Shi ya sa su suke kirana.

 

Wasu burinsu su gan ni,

Su ga mun saba da juna.

 

 

Ko’ina in sun kira ni,

Aji mun saba da juna.

 

Wasu ko mu zamo ƙawaye,

Don shawarta ga juna.

 

Wasu ko fatansu guna,

Ya zamo mun auri juna.

 

Wasu ko domin nifaƙa,

Ta su karyan ƙaddarina.

 

Burinsu kawai su gan ni,

Tumɓur tinkis! A rana.

 

Wasu ‘yan yara ƙanana,

Wasu mattasa irina.

 

Wasu mata ne na aure,

Da mazansu gida na sunna.

 

Za su zo da sufa ta aiki,

Za su ba ka kana ta murna.

 

Wasu bokaye gare su,

Daga kun arba da juna.

 

Wasu ma tsafi su ke yi,

Kuɓutarka mamallakina.

 

Wasu ibilisan zamani,

Dukiya da kuɗi da ƙauna.

 

In ka tsallake wanga tarko,

Gobe sabo za a jona.

 

 

Addu’a ita ce makamin,

Mumini mai son lumana.

 

Ba tsumi babu dabara,

Kuɓuta ta Khaliƙina.

 

Tambayata gun mutane,

Ko da mai amsan batuna.

 

Da akwai jinsin mutane,

Keɓaɓɓu ba su ɓarna.

 

Ɓarayi nasu ba su laifi,

Ba su yin sharri a tona.

 

Ba a yin wa’azi gare su,

In ka ji su kawai yabona.

 

Jama’a in babu amsa,

Sai ku ba ni gari da kaina.

 

Rukunin aikin jarida,

Na ƙasar Hausa garina.

 

Labarin ɗan jarida,

In ka gan shi yabo ka zana.

 

Ko takardar girmamawa,

Ya yi aure ko ko suna.

 

Ba ka jin ɓaci na suna,

Ko kaɗan ko ƙyas! Gani na.

 

Malami ko Bassarake,

Sun buga shi a ya yi ɓarna.

 

 

Shugaba ko jami’i ne,

An ga laifi nai a tona.

 

Mashahurin ɗan siyasa,

Bibiyarsa ake da ɓarna.

 

Ko mawaƙi ko sananne,

Bibiyarsa ake da ɓarna.

 

Mai karatu kar ka mance,

Ƙibular alƙallamina.

 

Wanda yai shuhura kaɗai ne,

Za ya san ilimin batuna.

 

Ilimin ga faratikal ne,

Ba tiyori sahibaina.

 

A nishaɗin nan na waƙa,

Za ku ƙaru a baitukana.

 

Za ku gane falassafata,

Da kirdado na kaina.

 

Ba hadisi babu aya,

Masalan aiki na zana.

 

Aikin da ya faru kaina,

Ra’al aini da kaina.

 

Simfil arissimetik,

Ɗaya ga ɗaya ai biyuna.

 

Za ni ƙara taƙin bayanin,

Shahara da na sami kaina.

 

 

 

Tsakure fa nake wa dangi,

Ko ciki a sam amfana.

 

Kar ku ƙosa da biya ta,

Da bayani a gabana.

 

Da akwai tufka da saƙa,

Da warewar ‘yan uwana.

 

Ku biyo ni bisa nutsuwa,

Da kula da nazar a kaina.

 

Tafiyar da maza su kay yi,

A cikin shekara da rana.

 

Wasu babu dare da rana,

Ba su tsayye bare su zauna.

 

Burinsu kawai su zamto,

Mashahuran zamanina.

 

Sai kawai suka ji dirina,

Ba zato da tsaka ta rana.

 

Ba zato ko ko tsumina,

Suka ji ni ina bayana.

 

Ƙanƙanin loto na karɓu,

Ƙauye, birnin garina.

 

Da kafofin Sadarwa,

Radiyo, T.Ɓ. ka kunna.

 

Da mujallu har Jarida,

Internet, fezbuk ka tona.

 

Daga nan kuma sai a kai ca!

Sara-suka a kaina.

 

Zahiri dukkan ni’imma,

Za ta sha hasada da ƙuna.

 

Kowa ka gani a inwa,

Tambayo ya sha fa rana.

 

Wanda yai barci na rana,

Ba shi cara ko a inna.

 

Masu munshari saleɓa,

Ba su zamtowa kamana.

 

Masu hikima sun bayani,

Mai biɗar shahara da suna.

 

Ba shi barci ko ya huta,

Ɗokaci na dare da rana.

 

An ka ce yaro gulamu,

Ɓata darre kay yi suna.

 

In ko ka ƙi kuwa ka zamto,

Mai kamar kumfa sanina.

 

Ko kamar gishiri na Andir,

Ya yi fuu! Haka sai ya kwana.

 

Ka zamo tamka da iska,

Mai kaɗawa ko a inna.

 

Ko’ina duka dai ta faɗi,

Sha ta zamto a wajena.

 

 

Radiyo aka je da suka,

Aka ɓata hali na guna.

 

Wasu na suka gare ni,

Wasu na yaƙi a kaina.

 

Wasu ma suka ce a goge,

Baitukan da aka adana.

 

Sanadin harkar siyasa,

Da ake ciki a garina.

 

Nan na fara ganin adawa,

Da idona da sanina.

 

Aka sa ɗanbar ƙiyayya,

Har ana gori a kaina.

 

Na ga samfur da misalai,

Na ƙiyayya ‘yan uwana.

 

Na ga hali na shirinya,

Ka kafa a kifarka rana.

 

Wanda duk ka gina ya taso,

Sai ya ɗora yima hiyana.

 

Inuwa ka gina a huta,

Sai a maishe ka a rana.

 

Na ga bibiko idona,

Masu saran duddugena.

 

In yi tirgaɗa a rushe,

Ai gada ta zare a kaina.

 

 

In yi tufka sai na wucce,

Sai a zo a ware shirina.

 

Na ga tarkon masu haƙƙo,

In yi ɗan tari su tona.

 

Na yi ban yi ba duk guda ne,

Za a ƙaga minni ɓarna.

 

Na ga masu duhun basira,

Ba ta aiki sai a kaina.

 

Na ga masu baƙar fasaha,

Ba ta motsi sai a kaina.

 

Na ga masu ragon azanci,

Ni suke biko su ƙona.

 

Jinginarsu da shinfiɗarsu,

Duk gadon baina su kwana.

 

Ba su buri ko muradi,

Da ya zarci a gan ni rana.

 

Shahara dai ga ni ga ta,

Ko dare safe da rana.

 

Ba ni iko don na huta,

Babu sirri cikin gidana.

 

Babu dama in yi sabga,

Ta irin tasu ‘yan uwana.

 

Tafiyar ƙasa ko da na so,

In na yi ta fa sai a nuna.

 

 

Kar ku ƙagara masu bi naaaaaaaa,

Masu bi na.

 

Mai Sauraro,

Har kai mai karatu.

 

A gaba fa akwai bayana,

Can gabba akwai bayana.

 

Rukuni a cikin rukunnai,

Na biyu na gamo bayana.

 

Mu tara fa akwai bayana,

Ka tara fa akwai bayana.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Post a Comment

0 Comments