Ticker

6/recent/ticker-posts

Rukunin Kalubale

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

Rukuni na cikin rukunnaiiiiii,

Rukunin ƙalubalena.

 

Rukuni na huɗu bayani,

Rukunin ƙalubalena.

 

Amshi

Shahara ce ɗan mabuɗin,

Ilimi a ƙasan sanina.

 

Mai amsa kiran maraya,

Da talakka da shugabana.

 

Barci ko gyangyaɗawa,

Sun koru ga Khaliƙina.

 

Matsaya ta munfa gana,

Da Sani Lawan gwanina.

 

Da yac ce zai yi gani,

Da gwamna shugabana.

 

Zai nemi a ba shi iko,

Da wakilcinmu a gana.

 

Ku je ku tsumai kirana,

Ko da almuru da rana.

 

Daga nan sai munka koma,

Zama na jira tsammana.

 

Na tafi gari na Bauchi,

Aka doka wayar kirana.

 

Aka ce mata ta gwamna,

Tana so za mu gana.

 

Ta hanyar Missibahu,

Ta sam ikon kirana.

 

Daga nan sai gun Halima,

Matar gwamnan garina.

 

ALA aka ce da shi da,

Misbahu mai danana.

 

Muka je gommen hawus,

Bayan issha sanina.

 

Halima ta sa a kai mu,

Falon baƙi mu gana.

 

Ta fito ta marabce mu,

Muka hau tattauna kana.

 

Muka ce mun ɗau mataki,

Sai ta ce kar kui hakanna.

 

Ku tsumayi zuwa na Malan,

Ya tafi Lagos da rana.

 

In ya zo zan mai jawabi,

Kar ku sau waƙa ganina.

Sai muka taso da murna,

Lamura za su gudana.

 

Sasari da akai na ɗauri,

Za a kwance ‘yan uwana.

 

 

Kowa zai sami ‘yanci,

Za a sam sauƙi lumana.

 

Daga nan wasu ‘yan uwanmu,

Suka tattara sukka zauna.

 

Zargi na su za a ba mu,

Kuɗaɗe gun sa gwamna.

 

Suka je suka yanki waƙar,

Hasbinallahu da rana.

 

Suka kai gun ‘yan wayoyi,

Aka watsa ko a inna.

 

Suka ɓata shirin da mun kai,

Suka ƙulla shirin hiyana.

 

Suka je Censor da sharri,

Wai munyo soja gona.

 

Wai mun yi infasineshan,

Mun cuci Halima gwamna.

 

A can ɓarayin Halima,

Ta ci alwashi da ƙuna.

 

Mun baɗeta ƙasa a iddo,

Mun yi sulhu irin na arna.

 

Mun yi alƙawari da kanmu,

Sidi da mu kai mu ɓanna.

 

Sai ta harsala tai nifaƙa,

Ta kirayi rabo na gwamna.

 

 

Ɓarayin Sani Lawan ma,

Aka kai masa tsegumina.

 

Sai ya ce ya zan yi hakka,

Baya mun sharaɗin amana.

 

Babu halin yin bayani,

Ko in je don kare kaina.

 

An ɓata ma’alarmu,

Da Halima amarya gwamna.

 

An ɓata mu’amalata,

Da Sani ubangidana.

 

Hasbinallahu na sake,

Faɗi bisa harsunana.

 

Kan kwabo fa gari ya ɗauka,

Baituka na karrakaina.

 

Ko ina ka bi ka ji sautin,

Hasbinallahu a baina.

 

Sharri na munafukanmu,

Gungun maciya amana.

 

Sai suka koma a gefe,

Sun saƙa shiri na ɓarna.

 

Ganin haka nai tawasul,

Da sunan Khaliƙina.

 

Na sake na yo tawassul,

Da waƙar da na zana.

 

 

Kafin haka sai rahoto,

Ya ishe ni ina gidana.

 

Aka ce wai an yi bandin,

Waƙoƙi an ka zana.

 

Ciki da su Hasbinallah,

Da mu kay yi da ‘yan uwana.

 

Aka ce wai an haramta,

Ji ko a sayar a baina.

 

An ka kawo min jarida,

Na karanta ni da kaina.

 

Ni ma sai nay yi ƙuduri,

In fito don kare kaina.

 

Na yi hira da ‘yan jarida,

Na gaya masu ra’ayina.

 

Na yi hira garin kaduna,

Da kafofin radiyonna.

 

Haka Raypower ta F.M,

Mun hira ta ra’ayina.

 

Wannan ya fusata Censor,

Suka lashi takobi kaina.

 

Suka hau nema na ALA,

Za ai shara’a a kaina.

 

Wata ran Jum’a da darre,

Na ga gardawa a kaina.

 

 

Na je Oasis da ni da,

Adam Kirfi na guna.

 

Suka ce mu an ka turo,

Ƙararka akai bayana.

 

Suka ce noma salan yau,

A Siteshan za ka kwana.

 

Sai na ce ku ɗin su waye?

Suka ce mu jami’aina.

 

Sai sukai nuni da kati,

Na shaidar jami’aina.

Na ce masu na ga wannan,

Saura shaidar tsarona.

 

Na ce masu ba waranti,

Ba halin ai tsarona.

 

Ɗayansu ya je shi mota,

Nan take ya je ya zana.

 

Suka ba ni waranti arestin,

Sai na duba da idona.

 

Sai na ce da abokina,

Ga motata amana.

 

Adam Kirfi a sannan,

Muna tare da juna.

 

Sai ya ce duk inda za ku,

Da ni za a a gana.

 

 

In laifi ne da kay yi,

Ai tare mu kai da juna.

 

Hasbinallahu wa’ni’imal,

Wakilu da laffazina.

 

Sai na taushe shi da kalma,

Da ƙyar muka rabu da juna.

 

Da zuwa police station,

Bayan kanta na zauna.

 

Da zama ɗan lokacinnan,

Sai ga ‘yan kar ta kwana.

 

Fulanin nan na talla,

‘Yan jarida na garina.

 

Yau ga ALA a hannu,

Amma ba mai tsarona.

 

Don Police Commisioner,

Ya ce bai case a kaina.

 

D.P.O. sai ya tsure,

Ya ce shi bai tsarona.

 

A kai yi waya a Censor,

Sun kulle waya da rana.

 

Kare ya kama zaki,

Ƙoshi ga kuma yunwa.

 

Kan dole aka sake ni,

Wai na kai kaina da rana.

 

 

Rana ta tara ga wata,

Na Yuli a lisafina.

 

Tu Tausan nayin a sannan,

Shekaru fa biyar da kwana.

 

Aka ce ran sha uku ne,

Zaman kotu da rana.

 

Sha uku ga wata na Yuli,

Na kai kaina da rana.

 

Na iske ɗarin masoya,

Abokai ‘yan uwana.

 

Ku ji ba masaka ta tsinke,

Cika ta kwari ganina.

 

Da a kai izini a zauna,

Alƙali ya zo ya zauna.

 

Tuni kowa sai ya miƙe,

Aka ce Kot! Aka zauna.

 

Nan take magatakarda,

Ya aje fayel na guna.

 

Muhiti ya karanta ƙara,

Ya kira sunan ubana.

 

Na gabata a ɗan akwaku,

Ya kira lauyan gurina.

 

Ya gabata da lauyana,

Murtala lauya a guna.

 

 

Bayan fa karanta caji,

Aka nemi fa ra’ayina.

 

Guilty or not Guilty,

I am not guilty bayana.

 

Ɗan shiru ya gita tsakani,

Sai rubuce-rubuce kana.

 

Daga nan lauya na Gwamna,

Ya nemi a ƙara kwana.

Baristan ɓarayina,

Ya aminta da ƙara kwana.

 

Daga nan aka ɗagga ƙara,

Zuwa kashegarina.

 

Ran sha uku ne ga Yuli,

Na kai kaina da kaina.

 

Bisa alƙawari da mun kai,

Na je kotu da kaina.

 

Jama’a sun kay yi tsinke,

Ba gurin tsuguno ka zauna.

 

Sai Lauyan gwamnatina,

Ya bugo tarho da rana.

 

Na ɓidar izini a mai da,

Shari’ar washegarina.

 

Cewarsa yana da shara’a,

Wata kotu a can dabanna.

 

 

Sanadin haka anka mai da,

Shari’ar gobe a zauna.

 

Jama’a na gun-guni,

Ra’ayoyi na gudana.

 

Marubuta ‘yan uwana,

Wasu ‘yan fim sahibaina.

 

Na ga Nura da ‘yan jarida,

Yana ta batu a kaina.

 

Rana ta zama na uku,

Tun safe na je na zauna.

 

Jama’a duk sun jigata,

‘Yan tsiraru ne a guna.

 

Ƙarfe biyu cif! Na rana,

Jama’a sun bar gurina.

 

Sai ga mota ta prison,

Da ma’aikata da rana.

 

Sai ga alƙali ya zo,

Sai ga lauya ya zauna.

 

A cikin minti ƙalilan,

Aka ce mu shige mu zauna.

 

Aka sake karanta ƙara,

Aka sake ɗaga zamana.

 

Amma kuma wanga loto,

Ba beli wai a kaina.

 

 

Lauya ya buƙaci beli,

Aka ce ba shi a kaina.

 

Jami’ai suka sa ni mota,

Sai kurkuku za ni kwana.

 

Abin al’ajabi da,

Ya ɗumama minni kaina.

 

Da isar mu gida na jarum,

Jama’a na ta tsumina.

 

Aka buɗe minni ƙofa,

Da shiga naɗ ɗagga kaina.

 

Na ji ihu ya karaɗe,

Ya juyan hankalina.

 

Ihun da a kai a loton,

Ya ruɗan kunnuwana.

 

Take sai suka fara waƙar,

Bakan Dabon garina.

 

Yin hakan da su kai gare ni,

Sai ya juyan hankalina.

 

Sai na ma rasa in da za ni,

Sai na nemi guri na zauna.

 

Jami’an doka na furzin,

Suka harhana tsokanana.

 

Suka ce zo nan cikinmu,

Mu yi sallah sai mu zauna.

 

 

Da muka gama alwalarmu,

Ni na yi liman da kaina.

 

Na idar kuma na yi du’a’in,

Jarabawa yau a kaina.

 

Sai tunani yag game ni,

Na abin da ya faru kaina.

 

Laifin da ake zato na,

Bai kai sata ba kana.

 

Laifin da ake zato na,

Bai kai fyaɗe ba kana.

 

Laifin da ya kai ni jarum,

Bai kai yin ku ba kana.

 

Laifin da ya sa ni tasku,

Ba kisan kai ba ku tona.

 

Me ya sa aka ƙi a ba ni,

Beli na in fanshi kaina?

 

Kuma sanda a kai kirana,

Kotu na je da kaina.

 

Zuciyata ke ta saƙa,

Amsawa ma da kaina.

 

Ya a kai wai fursunoni,

Suka san da zuwa na kwana.

 

Suka taru suna tsimina,

Da shiga suka zolayo na.

 

 

Daga baya na gane komai,

An shirya zuwa na kwana.

 

Tun ran farko na kamu,

Aka shirya a kai na kwana.

 

Lamarin da ya kiɗɗima ni,

Ya daɗan al’ajjabina.

 

Kotu cewa tai a kai ni,

Gobe a dawo a zauna.

 

A gaban lauyan jihata,

A gaban lauya na kaina.

 

A gaban kowa da kowa,

‘Yan kallon shari’ana.

 

Da zuwa sai anka sauya,

Labarin sharri’ana.

 

Aka ce ga shi rubuce,

Sati biyu anka zana.

 

Sai na sake kiran wahabu,

Hasbiyallahu gwanina.

 

Sai nay yi shiru a zuci,

Lahaula ta zam batuna.

 

Jama’a ne ke shigowa,

Sun zo jaje gurina.

 

Na ga Nura a sahibaina,

Nura Agin nan na guna.

 

 

Na ga Auwalu Ɗan Barno,

Shi da Coach Sani na guna.

 

Na ga Kirfi da shi da Maryam,

Duka sun jigila gurina.

 

Ga Bashiru na Ɗandagona,

Yai ziyara a gurina.

 

Na ga Fati Binta Niger,

A mawaƙa ‘yan gurina.

 

Na ga Maimuna Birniwa,

Ta yi kuka ma a kaina.

 

Na ga Inspector fa Binta,

Har tsaraba tai gurina.

 

Na ga M.G. nawa Zico,

Ya kai ziyara gurina.

 

Har wasu mata maƙotan,

Furzin sun zo gurina.

 

Suka ce sun ji a taskar-

Labarai ne na rana.

 

Suka zo domin su gan ni,

Sun gode Khaliƙina.

 

Sun sami cika ta buri,

Yau sun ganni da rana.

 

Wasu na kuka a kaina,

Su suna murnar ganina.

 

 

Na ga Dije da Allawiyya,

Na hawaye duk a kaina.

 

Su ne suka so su sani,

Yin hawaye da idona.

 

Ran nan na rabe masoya,

Da kiyoshina su ƙauna.

 

Masu waƙa na ta murna,

Allah ƙara wai a kaina.

 

Wasu na ai ga irinta,

Taurin kai ya yi rana.

 

Ga ɗan lelen Sarauta,

Ga ɗan lele na Gwamna.

 

Yau ina ƙaryar sanayya,

Ga shi bursuna za a kwana.

 

Yau ina ƙarya ta lele,

Ga shi jarum za a kwana.

 

Na tuno da gari ya waye,

Aka ce an zo ganina.

 

Wani Jami’i na aikin,

Firzim yaz zo gurina.

 

Ibrahimu fa Tola,

Yaz zo da tuni a guna.

 

Da ganina sai ya ce min,

Ya zo da tuni a guna.

 

 

Tola da ya kallace ni,

Sai ya ce ko za ka tunna.

 

Daga jin haka sai tunani,

Nan take ya zo a kaina.

 

Wataran na je gurinsa,

Na same shi mu gana.

 

Sai na ce masa na amince,

Bisa yardar izzinina.

 

Ni a kai ni gida na yari,

In yi sati can da kwana.

 

Duk abin da ake a jarum,

A yi min bisa lamunina.

 

A yi min aski a ba ni,

Yunifom in saka jikina.

 

A ba ni irin abincin,

Da ake ba ‘yan uwana.

 

Manufata lokacin can,

In yi ilimi ni a kaina.

 

In nazarci gida na jarum,

Da halayyar ‘yan uwana.

 

In ji laifi ban da ban dai,

Da fa nau’ukka na ɓarna.

 

Marubuci nakkasance,

A wancan lokacina.

 

 

In gano yarda hukuma,

Taka rainon ‘yan uwana.

 

In karanci zamantakewa,

Makarantar kurkukuna.

 

In yi littafi ƙadimi,

In sayarwa ‘yan uwana.

 

Sai Tola ofisan nan,

Ya ce ga shawarina.

 

Farko ba watta doka,

Da ta ce haka a sanina.

 

Kuma in har babu doka,

Babu halin ya wakana.

 

Sai dai in za ka yarda,

Bisa harsashe na kaina.

 

Ka je ka ka karya doka,

Ka yi laifi a ganina.

 

In kai haka babu shakka,

Za a kai ka kaso ka kwana.

 

Da ka yi kana da ‘yanci,

Tarihi ko a inna.

 

Dokar prison sanina,

Komai sirri hakanna.

 

Komai ka gani ka bar shi,

Sirri ne kar ka tona.

 

 

Wanga zango ne na huɗuuuuuu,

Rukunin ƙalubalena.

 

Zan yi zango da bayani,

Rukunin ƙalubalena.

 

Ku tara gaba kwai bayani,

Rukunin nasara a guna.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments