Ticker

6/recent/ticker-posts

Rukunin Tarihi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

Godiya ga Ubangijinaaa-

Da ya tsarma dare a ranaa,

Dare a rana.

 

Amshi

Shahara sanadin sanina,

Sababin ilimi na Ala.

 

Godiya ga Ubangijina,

Da ya tsarma dare a Rana.

 

Hikima ta Ubangijina,

Ta buwayi alam su zana.

 

Baiwarka Ubangijina,

Ta wuce ƙalami su tona.

 

Za ni bayyana ra’ayina,

Kan batun rayuwa ta kaina.

 

Ɗan Malan Sani Ala,

Ladan Baba a guna.

 

Sani Ladan Habu ne,

Bakari kaka a guna.

 

Shi ko Bakari kwa ɗa ne,

Ga mijin Yawa bincikena.

 

Mijin Yawa Kura Jarmai,

Baba a gurin kakana.

 

Ɗan Sarki Dambuwa ne,

Gobir tsibiri garina.

 

Dambuwa ɗa ne Gwamki,

Gwamkawa assalina.

Masarautar Bawa Gwarzo,

Kuji salsalar Ubana.

 

Sunana Al’Aminu,

Da shi aka raɗɗa suna.

 

Alhaji Ladan Ubana,

Da Abubakari kakana.

Sunan da na sa wa kaina,

ALAN WAƘAR yabona.

 

Saƙandamai na sunayena,

Na cire ciki laƙƙabina.

Asali na garin ubana,

Jega, Kebbi State ka tona.

 

 

Asali na garin uwata,

Dabo ta Kano garina.

 

Gari ko na haihuwata,

Birni na Kano garina.

 

Shekarar ran haihuwata,

Ƙirgen shara’ar Nabina.

 

Hijira ta alif dubu ɗai,

Da ɗari uku da ɗigonna.

 

Ma’ana manufar ɗigonna,

Casa’in da huɗu nufina.

 

Ƙirge kuma na Nasara,

Nineteen seɓenty-three na.

 

A Munisifal Kanawa,

Yakasai ta garina.

 

Nan ne aka haihuwata,

Labarin assalina.

 

Nai ilmin issilama,

Matayassara gwargwadona.

 

Nai ilmin zamanina,

Boko don zamanina.

 

Gwargwado dai diploma,

Na yi domin kare kaina.

 

 

Na yi kan Art and Design,

Ƙirƙira zane fununa.

 

Duka dangogin Fusaha,

Na fi ƙarfi lammurana.

 

Nai rubutu na hikaya,

Fikshin ƙarin bayana.

 

Waƙar baka ko ta zubbe,

Ita ce babban fagena.

 

Zan matsa kan maudu’in,

Da ya jaddada in bayana.

 

Kan Shuhura ma su bina,

Da na ce tsanin sanina.

 

Shuhura sanadin ƙwarewa,

Sababin na fahimci kaina.

 

A mu’amilla da dama,

Mai wuyar ta a ra’ayina.

 

Nazarin halin mutane,

Ammafi girma ku tona.

 

In ka shahhara ka buwaya,

Da halin ɗan Adamuna.

 

Wanda yai shuhura ku gane,

Doki da kare da tana.

 

Duka ɗai suke a gurinsa,

Ɓigiren so har da ƙauna.

 

Kowansu ya zo gurina,

Za ni tarbe shi da murna.

 

 

Marhaban baƙo na kaina,

Har in ce masa sahibina.

 

Wani al’adarmu ɗai ne,

Wani Baubawa a guna.

 

Wani yare namu ɗai ne,

Wani saɓanin na guna.

 

Wani addininmu ɗai ne,

Wani ko akasin na guna.

 

Wasu jinsiyya ta mata,

Wasu jinsiyyar gidana.

 

Wasu ilmin Arabiyya,

Wasu ilmin zamanina.

 

Wasu sashe na firaƙu,

Ahalul sunnar Nabina.

 

Wasu shi’a mazhabinsu,

‘Yan Aliyul Abidina.

 

Wasu ko Ahmad Gulamu,

Wasu Isa Annabina.

 

Wasu ko bautar siyasa,

Da ake ciki zamani na.

 

Wasu ma su gado na mulki,

Rawani ko gwamnatina.

 

Wasu Alƙalan Shari’a,

Wasu Final kot gani na.

 

 

Wasu yara ‘yan ƙanana,

Wasu mattasa kamana.

 

Wasu tsofaffi a suffa,

Burinsu su zo guri na.

 

Babu ƙwari a jikinsu,

Kyarmarsu dare da rana.

 

Wasu zafin kai gare su,

Wasu sauƙin kai lumana.

 

Wani ba’abore cikinsu,

Wani sauƙin kai gani na.

 

Wani ilmi za ya ba ka,

Wani ko ya zo ku gana.

 

Wani alkhairi gare ka,

Wani cuta ce hiyana.

 

Wani ɗan adam kamarka,

Wani aljan ko rauhana.

 

Wani Boka ne matsafi,

Wani masanin Khaliƙina.

 

Wani arzurta ka za yai,

Wani four one nine ganina.

 

Wani ɗan daudu a suffa,

Wata yawon karrakaina.

 

Ku biyo ku ji al’ajubba,

Da ya sa nai tsokacina.

 

 

Za ni tsakuri ɗan ƙalilan,

Da a kaina sun wakana.

 

Wani jami’i na aikin,

Radiyo ta Kano garina.

 

Malan Abdallah Sani,

Sunansa ubangidana.

 

Ya ishe ni ina a zaune,

Muka gaisa sai ya zauna.

 

Sai ya ce ALA na waƙa,

Lamarinka azim gurina.

 

Girman al’ammarinka,

Ya gaji da sani na kaina.

 

Yarana an ka yiwa,

Ruƙiyar Ahalu sunna.

 

Aljani ya fito jikinsu,

Sai ya ɗora faɗin bayana.

 

Aka ce masa me dalili-

Na shigarka jikin ɗiyana.

 

Sai ya ce kullum ɗiyanka,

Ko maraice dare da Rana.

 

Waƙar ALA gwaninmu,

Suka ji a dare da rana.

 

Mu ko in har za su kunna,

Da’iman kuma za mu zauna.

 

 

Mutumin ya tambaye su,

Laifin ALA su tona.

 

Suka ce masa ba shi laifi,

A gare shi da so da ƙauna.

 

Sai ya dube ni da shakka,

Rantsuwa ya yi da gwanina.

 

Sai ya ce shawara in ba ka,

Dafa’i ka riƙe shi ɗana.

 

Suratul Kursiyyu aya,

Ka riƙe ta dare da Rana.

 

Wataran a watan Nuwanba,

Tutauzan sis batuna.

 

Wata tsohuwwa ta zo ta,

Ta galabaita ganina.

 

Rauni linkib jikinta,

Ya yi tamoji ganina.

 

In tana tafe sai ta huta,

Sai ta yunƙura sai ta zauna.

 

Da kaɗan-da-kaɗan tazo ta,

Har shigifa ta ubana.

 

Da shiga ta fashe da kuka,

Muka hau tausa da rana.

 

Ko da tan nutsu ko ta huta,

Sai ta hau yi mana bayana.

 

 

‘Yar ɗiyata ce na wanke,

Sanadin aure na Sunna.

 

Mun yi mun yi ta zauna,

Sai ta ce sharaɗin ta zauna.

 

Sai an kai matta kaset,

Wanda nai Ummi Momina.

 

Kuma an ce ba a saida,

Kaset ɗin ko a ina.

 

In gidan radiyo ta kunna,

Daga nan ta jiyo bayana.

 

Ban shirya fitar da shi ba,

Ba shiri na ciro na guna.

 

Sai na ba ta gami da kari,

Don zaman aure ya nuna.

 

Tsohuwa ta ruƙƙume ni,

Tai hawaye na lumana.

 

Ta kira yi Ubangijinmu,

Tai du’a’i a gurina.

 

A kwana a tashi baba,

Mai yawan rai zai bayana.

 

Wata tsohuwwar Ilaila,

Tai maya biyu don mu gana.

 

Ni ko saɓani gare ni,

Ta wuyata kafin mu gana.

 

 

Tai maya biyu ukku guna,

Daga ƙarshe mukka gana.

 

Da mu kai arba da juna,

Sai hawaye ke gudana.

 

Sai ta ce ko yanzu Allah,

In ka so ɗauki raina.

 

Ka cikan buri muradi,

Da ganin Alan ga ɗana.

 

Ta riƙe ni ta hau jawabi,

Sonka zai lahani a guna.

 

Lafazinka idan na ji shi,

Sai hawaye ke gudana.

 

Goɓilla gari da nisa,

Gwadabawa ne garina.

 

Illaila kusa da boda,

Duk a can na baro ɗiyana.

 

Na taho domin biɗarka,

Don tsantsar so da ƙauna.

 

Na yi kalmomi gareta,

Masu sanyaya rai da ƙauna.

 

Na yi kyautukka gare ta,

Na kaset na gani da jina.

 

Da atamfofi na sawa,

Da kalandun hotunana.

 

 

Muka ɗau hoto a tare,

Da busharar ni da kaina.

 

Za ni yo ramko gare ta,

In ziyarce ta da kaina.

 

Haka ko an kai umarni,

Bisa yardar Khaliƙina.

 

Na ziyarci Ilaila haƙƙan,

Ni da yarana da Rana.

 

Muka kwana gidan Khadija,

Tsohuwa mai so da ƙauna.

 

Na yi waƙoƙin yabawa,

Na yi baitoci na ƙauna.

 

Aka min tarbar bajinta,

Wai gidan Sarki in kwana.

 

Sai na ce ni gun Khadija,

Nan na zo nan za ni kwana.

 

A cikin rinkar Khadija,

A ƙasan Darni na kwana.

 

A cikin rinkar Khadija,

A ƙasan shifci na kwana.

 

Sai labarin Sa’ade,

Shekarunta bakwai na rana.

 

Wata Jikanya ta Sarki,

Wayonta wuce sanina.

 

 

In ana so tai karatu,

Sai a sa mata faifayena.

 

Waƙa ta haddace su,

Bitar su dare da rana.

 

In kana son kui zumunta,

Ce mata angonta nina.

 

In ko kuka za ka sa ta,

Ka yi furucin ƙi a guna.

 

Lokacin hutun Sa’ada,

Dole sai an kaita guna.

 

Har waya maman Sa’ada,

Ta sayo mata don ta kunna.

 

Ta bugo mini sai mu gaisa,

Ko da almuru da rana.

 

Kullum lamarin Sa’ade,

Sai gaba kan so da ƙauna.

 

Yarinya ce Sa’ada,

Mai nunin so da ƙauna.

 

Wani loton sai a ganni,

Ko a aiki ko gidana.

 

Ni da fagal, za mu zauna,

Har muna taɗi da juna.

 

In da ‘yan canji a guna,

Sai in ba su saboda ƙauna.

 

 

Nakasassu ma ku jini,

Na ziyartar ofishina.

 

Da makafi har guragu,

Na riƙe su a ‘yan uwana.

 

Wata ran in kai ziyara,

Ga taɓaɓɓu ni da kaina.

 

Ko in je ni gidan Marayu,

Don sanin ilimin idona.

 

In ga halin wai ni ‘yasu,

In yi ragiretin da kaina.

 

Wani sa’in in yi kotu,

Don ganin zahir idona.

 

In yi kallon sharri’o’i,

Da ɗabi’u ban daban na.

 

In yi al’ajab da kaina,

Har in gode Khaliƙina.

 

Nai mu’amilla da dama,

Da mawaƙa sa’annina.

 

Na yi hulɗoɗi da dama,

Ciki har shuwagabana.

 

Wasu sojoji da kaki,

Wasu ‘yansandan ƙasana.

 

Wasu Emagrate da Custom,

Wasu ko a ciɓilian na.

 

 

Za ni dawayya a baya,

Kan bayanin lammarina.

 

Mai karatu dakace ni,

Shuhura farkon batuna.

 

Na kirata da ɗan mabuɗin,

Ilimi bisa kan sanina.

 

Dukka labarin ga nawa,

Ka yi tsinkayar batuna.

 

Nasabarsu da illimina,

Shuhura tak kai su guna.

 

Na tuno farkon ɗagawa,

Da ina ɗan ƙanƙanina.

 

Nai furamaren garinmu,

Da Sakannidire sanina.

 

Na zamo alkatibinnan,

Marubucin so da ƙauna.

 

Ba domin ban iya ba,

Shahara ta hana sanina.

 

Babu wanda ya san da ALA,

Ko bare aikin wurina.

 

Tun ina Isilamiyarmu,

Nayi waƙoƙi na kaina.

 

Zaharaddini ta TM,

Za ta shaida kan batuna.

 

 

Na yi waƙoƙi da dama,

Sun fi ƙirgawa da kaina.

 

Babu sanadin a jiyo su,

Babu hanyar kar ta kwana.

 

Babu halin in bugo su,

Ku saya ku ji ‘yan uwana.

 

Babu mai ɗaukar wuyaye,

Majiɓincin lammarina.

 

Babu mai sa ni a hanya,

Ko ya ƙarfafi lammarina.

 

Na tuno wani sahibina,

A ciki na su abokaina.

 

Ko dare safe da Rana,

Sai ya gan ni ina abina.

 

Sai ya ce wahala kake yi,

An riga ka a zamanina.

 

In shiru don babu kalma,

Ta faɗi don kare kaina.

 

Yin rubutu a gare ni,

Wajibi ne a wajena.

 

Ba zaton samun muƙami,

Ko kuɗi daula sani na.

 

Sannu-sannu a kwan a tashi,

Sai gani ga Malamina.

 

 

Sani Makarantar lungu,

Shi ya zam tsani na guna.

 

Gunsa nai ilimi a waƙa,

Na rabe adadin bakana.

 

Nan na san wa ab Bahause,

Har da al’adar garina.

 

Adabin Gargajiyarmu,

Adabin ga zamanina.

 

Ba ni manta Sunusi nawa,

Musa Inya gwanina.

 

Sanadinsu da su da Malan,

Radiyo ta zamo gidana.

 

Na yi talla ta Mannufarta,

Ta zamo tsanin hawana.

 

Na zamo mai kambamata,

Ta zamo saka ayyukana.

 

Na kirata ma-ba-da-mama,

Sai ta sani dare da rana.

 

Da na ce Gagarri gasa,

Sai ta ce ka zamma ɗana.

 

Na yi shakundum gare ta,

Daga nan na fito da kaina.

 

Daga nan sai radiyoyi,

Suka nemi mu gane juna.

 

 

Da su Raypower, Freedom,

Pyramid sun ɗau amana.

 

Daga nan gangar siyasa,

Kibiyarta ta nuna kaina.

 

In na yo waƙar siyasa,

Sai in zo inyo ta kaina.

 

Sanadin waƙar siyasa,

Na ziyarci garin Madina.

 

Nai ɗawafina da sa’ayi,

Na aje farali na kaina.

 

Masu saurare da binaaaaaa,

Rukunin farko bayana.

 

Rukunin ga na tarihi,

Mu tara a gaba bayana.

 

Rukunin ga na tarihi,

Ku muje gaba kwai bayana.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments