Ticker

6/recent/ticker-posts

3.30 Jami’a Gidan Ban Kashi 2- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 110)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Na ga ka yi tuya ba ka sa da albasa ba,

Ɓera da sata ai daddawa da ɗoyi,

Alan Kanawa kan tsangayar karatu.

 

Na ga ka yi tuya ba ka sa da albasa ba,

Ɓera da sata ai dadadawa da ɗoyi,

Alan Kanawa kan tsangayar karatu,

Jami’a gidan hoɗijan yan ka saƙe hange.

 

Amshi

Alan Kanawa wai me kake nufi ne?

Na ji ka yi waƙa fat wan da tu a baya,

A baya ka yi suka kan munin ɗabi’u,

Yanzu me kake so ka faɗa wa jami’a ne, Alan Kanawa!

 

Wahidun assamadun lam yalid ga Allah,

Bai haifa ba ba a haifar ba Zuljalala,

Son zuciya ka katarshe Zuljalala,

Ya zama idan na ɗau kalam warƙa Allah,

Kar na zana cin fuskar bayinka Allah.

 

 

 

Jami’ar farko na yiwa maluma na,

Ta biyun na sabunta kalamaina,

Ta uku zan juya ga gwamnatina,

Ta huɗu ga ɗalibai takwarorina,

Jami’a kashi ta biyar fa’ida in nuna.

 

Wata rana na ɗau kaya na bincike na,

Sai jami’a can na iske malamai na,

Matsalar admission ce ta soki raina,

Cunkuso ne ɗalibai takwarorina,

Kan biɗar karatu a tsangayar ku nuna.

 

Can na iske farfesa malamin karatu,

Na ce da farfesa na taho karatu,

Malam ya ce sam guri ka sha karatu,

Na ce da shi Malam tsangayar karatu,

Tai cikar fari ba masaka ta ɗan karatu.

 

Na ce da farfesa tambayoyina,

Ɗalibai dubu maitan ƙarƙashin sanina,

Suna biɗar karatu nan Jami’a sanina,

Kuna sayar da form adadin oɓer sanina,

Sai ku ɗebi ɗalibai ‘yan kaɗan ganina.

 

A baya kun ka ce ƙa’idar ɗaukar karatu,

Sai fa mai credit adadi biyar karatu,

Sai da jarrabawar jamb za a ɗau karatu,

Ɗalibanmu sun cikashe ƙa’idar karatu,

Amma suna ta ragaita ba wurin karatu.

 

Na kalli farfesa nai ƙasƙas da kaina,

Ya ce da fa kai sara kan gaɓa ganina,

Haƙƙi na gwamnati ne ba Jami’a ba zauna,

Ƙa’ida da doka duk malamai sanina,

Alal aƙal zai ɗauki ɗalibi sanina,

Ashirin da biyar ko hamsin sanina,

Amma yanzu malamai ƙarƙashin sanina,

Mutum guda yana ɗaukar ɗalibai dubu da ko ɗari biyar ko ko saman hakan a kan sanina.

 

Malamai fa sun yi ƙaranci a kan sanina,

Ɗalibai fa sun yi yawa ba gurin su zauna,

Ba ajujuwan zuba su ya zan da kaina,

Babu yalwatar kayan aiki sanina,

Dole su ta ragaita ƙarƙashin sanina.

Sannan a ɓangaren ilimi su zama raunana,

Gwamnati ta tarayya ta ƙi kan sanina.

 

Na yi murmushi na gyaɗa kai cikin takaici,

Na tashi ba nauyi ya na mai jin barci,

Ya gwamnati za tai wa abin nan sakaci,

Tattalin ilimi a ƙarsarmu an yi barci,

Kira nake da babbar murya na daina barci.

 

Alan Kanawa zan zo na taimaka ma,

In ka zo bayani kan ɗalibai na yi ma,

Taimako da halin na ɗalibai na zoma,

Don ka feɗe Gata har bindinsa ne ma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments