Ticker

6/recent/ticker-posts

Mu Zauna Lafiya

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Amfanin ilimi aiki da shi gaskiya ce faɗɗake,

Yau Sa'adu Zungur ke kira da amo mai karsashi.

 

Zaman lafiya da juna,

Zama na riƙon amana,

Da massalaha da juna,

Da soyayya da juna,

Dangi mu fahimci juna,

Mu ɗau ilimi mu zauna,

Mu yi amfani mu nuna,

A aikace 'yan uwana,

Ba ƙyama ba kiyana.

 

Allah Al'raziƙu, kai ka ƙagi sani a cikin mashiyya,

Ka zamo Al'alimu masanin sirrin sarari da ƙurya,

Ka sallaɗa a yi ma bautar da sani a cikin biyayya,

Amfanin ilimi aiki da sani bisa tsinkaya.

 

A gani na Malamai su ya kyautu a baiwa kaso da yawa,

A fage na gudunmawa ta a zauna lafiya da kowa,

Haka nan kuma su ya kyautu a ɗorawa laifi da yawa,

Kan tashin tashina da rashin aiki da sani ya zauwa.

 

Ilimi gun ɗan Adam gishiri ne mai armasawa,

Ilimi gun ɗan Adam tirgaɗar ƙarfe ke zamowa,

Ilimi kam ginshiƙi ne kacokan gun kowa da kowa,

Sannan aiki da shi ke fassara halayya ta kowa.

 

Ilimi aiki da shi, shi yake saka soyayya ga kowa,

Sai an san ilimi za a san ƙauna da ake ga kowa,

Sai an san ilimi za a sami shigar hulɗa da kowa,

Kasuwanci ko sana'a sai da sani suka haɓɓakuwa.

 

 

Haka nan kuma malamai da sani suka ilmantar da kowa,

Da sani suka haddasa aka sami firaku take fitowa,

Don hakanga na ɗau ra'ayi na malumma su sun fi kowa,

Damar sadar da saƙon sada zaman lafiya ga kowa.

 

A san ulama'u na gargarun nan masu halin yawa,

Ba masu shiga gafaka ta malunta ba suna fakewa,

Masu shiga inuwar mutanen kirki su laɓewa,

Suna gwara kayin al'umma, manufarsu suke ɗagawa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments