Allah na sani kana jin zancena,
Domin kai ka zam mafi kusa a gurina,
In na yi kuskure ka yafen zunubaina,
Don haka na saka ka farkon zancena.
Sallul alaika ya Rasulu uban Nana,
Mai tsarki da tsarkakar asali guna,
Wanda ya zam sila ta riskar saƙona,
Ko kuma sanadi na samun haskena.
Dangi wata ran a kwance ina barci,
Ran nan na yi wani mummunan barci,
Da mafarki na wattsake ni da lalaci,
Aka mini izini in tsaro waƙena.
Allah kai ka ƙagi ruhi a jikina,
Ka yi mini rayuwa da kaidin kwanana,
Ka ɗauke ubanmu Ladan a gabana,
Yau fa gareni gobe sai ga maƙwabci na.
Allah kai ka yi ni ba mai tsoro ba,
Ba mai fargabar abin da ka ƙaga ba,
Amma ka sakan tunani mai jazaba,
Mutuwa ta hana sakata a tunanina.
Mutuwa na ji na gani da idanuna,
Na san babu makawa ai wata rana,
Zan zamto abin kwatance dangina,
Allah san a ribato alkhairaina.
Na zamto kamar farar kura Allah,
Na gaza in sake in wala ni "Ala",
Allah ka yi mini gamo da katar Allah,
In cikasa da da kyau a ƙarshen kwana na.
Duniya ba madauwamar ɗorewa ba,
Ba bigire na miƙe sawaye ne ba,
Mai barci ka wattsake tun ba ta zo ba,
Mai raba gardama da yayyanke ƙauna.
Mutuwa ta bi na ciki tun bai zo ba,
Ta ɗauko jira-jirai tun ba su zo ba,
Kai har mai cikin da ɗan ba ta ƙyale ba,
Balle kai da ke ɗagawa ikhwana.
Kai baƙo baka taho yin wasa ba,
Mai ci rani baka sami makwanci ba,
Balle ka yi gyangyaɗi har ka yi kwana,
Wata ran za ka wattsake ba gun kwana.
Mai tafiya ka duba salkarka ta fata,
Ka yi guzurin ruwa da kyakkyawan fata,
Ka yi wa kanka tanadi tarkon fata,
Tafiya ta zamo fa dole a hangena.
Kai ba a maka albishir ɗorewa ba,
Ka ga da mutuwa ba ku yi amana ba,
Ba ka da hanzarin da ya fi ka bar ɓarna,
Ka yi kicin-kicin da aikin sarkina.
Mai zuba jari ka sa hannun jari,
Mai kuwa asusu ka zo neman jari,
Mai yin dashi taho ka yi saurari,
Sirrin duk yana ga bautar sarkina.
Wata ran in na kalli tarin 'ya'yana,
Ga su suna dara suna shauƙin ƙauna,
In na tuno tta sai na kauda idanuna,
Sai ka ga ɓulɓular hawaye a idona.
Na san babu makawa sai ta bi su,
Ɗaya da ɗaya za ta tsittsince mini su,
Fata na Ubangiji ka tsare mini su,
Su yi gamon katar a ƙarshen bankwana.
Ita aljanna ba shiga otel ne ba,
Balle in biya kuɗi in wuce gabba,
Sannan ba shiga da ƙarfin ƙwanji ba,
Kai mai bindiga ka gane zancena.
Ita aljanna ba shigarta da alfarma,
Balle mai naɗi da siffar ban girma,
Mai girma ga Wahidun sarkin girma,
Mai aiki akan tafarkin manzona.
Ita aljanna babu wayo ɗan boko,
Balle in shiga siyasar 'yan boko,
In yi aringizo da biro bokoko,
Mai wayo mabi tafarkin manzona.
Ba a shigarta da siyasar ɓaɓatu,
Yanzu gareku 'yan siyasar ɓaɓatu,
In kun yarda zantukan da nake battu,
Mutuwa za ta gincire ku kuna kwana.
Allah babu sofanen son kai gunsa,
Ba ɗan wane ko uban wane a gunsa,
Don haka ya yi kansa babu tsatso gunsa,
Sarki mai nufin adala insana.
Allah kattsare fa harshen nan nawa,
Kadda ya kaini yabbaro ni kamar gawa,
Na san ka yi lamunin tarin baiwa,
Ga hikima kashi-kashi a ƙwaƙwalena.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.