Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanar Gizo-Gizo

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:  Ya mai tafi da kukan bayi kai mini agaji.

Yanar gizo-gizo,

Yanar gizo-gizo,

Ta sa a danne haƙƙoƙina,

Yanar gizo-gizo.

 

Yanar gizo-gizo,

Yanar gizo-gizo,

Hanyar nishaɗuwar ruhina,

Yanar gizo-gizo.

 

Allah abin nufi da buƙata na zo a firgice,

Roƙo na zo da shi Sarkina sura a birkice,

Ƙara na zo a kan angona ya bar ni yakice,

Yanar gizo-gizon da ya aura ya sa na haukace,

Ya kasa bibiya ga haƙina ya bar ni ɗimace.

 

Ki haƙuri fa mai ɗakina kar na yi bincike,

Na ba ki suttura da abinci ya za ki firgice,

Yanar giza-gizai na da aura aikace-aikace,

Zan zaga duniya a taƙi ne kafin a fargace,

Hanya ta walwala da nishaɗi domin na yo fice.

 

Na zo da durƙuso angona ba ni da walwala,

Ka ƙaurace muhallin bacci ka bar ni santala,

Dubanka na saka ni nishaɗi na sa ni walwala,

Haƙƙin zamantakewar aure shi ke da fallala,

Yanar gizo-gizo angona ta zo da baɗala.

 

Hanya ta ilmantarwa ce yanar giza-gizai,

Kafa ta saduwa da nishaɗi yanar giza-gizai,

Zango na ɗebe kewar bayi yanar giza-gizai,

Saƙo na saduwa da zumunta yanar giza-gizai,

Ba za ni bar kafar sadarwa yanar giza-gizai.

3.3 Yanar Gizo-Gizo - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 46)


Post a Comment

0 Comments