Ticker

6/recent/ticker-posts

Jami’a Gidan Bankashi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Jami’a gidan ban kashi ‘yan uwana

 

Na ga laccara mai koyi da faɗar Allah,

Na ga laccara mai koyarwa don Allah,

Na ga laccara mai tausan bayin Allah,

Na ga laccara mai ƙaunar bayin Allah,

Mai kwaikwayon halayen manzon Allah.

 

Mun ga laccara mai tottoshe halin ɓarna,

Mun ga laccara mai kakkau da halin ɓarna,

Mun ga laccara mai ƙin hali mummuna,

Mun ga laccara mai kyarma da an yi ɓarna,

Mun ga mai halin ɗan akuya yankan ƙauna.

 

Rabbana tsare ni da sharrin mutum da aljan,

Zan yo yabon ALA mai kwarmaton nan,

Munafuki mai ƙwaƙwa da kishin nan,

Kar ka ba ni ikon kushe don na ga kaina.

 

Rabbana salati ga magayyar tiƙewa,

Gurin mafi aminci mai kyan hali da tsaiwa,

Sayyidul wujuhillahi abin yabawa,

Mai cikar kamala mai tir da halin ɓarna.

 

Gidan sani gidan rushewa,

Jami’a ce.

 

 

Gidan haki gidan tauyewa,

Jami’a ce.

 

Gidan farraa gidan buɗewa,

Jami’a ce.

 

Gidan dariya gidan kokawa,

Jami’a ce.

 

Gidan ‘yar gusau gidan ƙosarwa,

Jami’a ce.

 

Gidan suttura ta tsiraitawa,

Jami’a ce.

 

Jami’a gidan kokawa wayyo Allah,

Jami’a gidan wahalarwa ‘yan samari.

 

Kun ga jami’a ita at tushen al’umma,

Dukka shugaba daga can ne ke ɓullowa.

 

Kun ga likkita mai lura da masu cuta,

Dagga jami’a ke zauwa babu musawa.

 

Mai da hankali ga ma hamshaƙin ɗansanda,

Ya yi jami’a ba mai suka da musawa.

 

Je ma’aikatar shari’a taron alƙalai,

Dagga jami’a kowannensu yake zauwa.

 

Ko a ɓangaren lauyoyi in mun lura,

Jami’a suke tafiya sannan zakkowa.

 

Shi ya sa nake waƙa ba sassautawa,

In ta gyaru al’umma ba sauran ɓarna.

 

 

Da nay yi laccara mai cizo da kamar ceto,

Gwara nai fado ko wasan gardo-gardo,

Umm Allah gatan bawa.

 

Da nay yi laccara mai cutar ‘ya’ya mata,

Gwara nay yi tallar gwanjo riga wando,

Umm Allah gatan bawa.

 

Da nay yi laccara mai kama karya,

Gwara nay yi tashen nan mai surar dodo,

Umm Allah gatan bawa.

 

Da nay yi laccara mai zaluntar ‘yan yara,

Gwara na yi suu ko na kakkamo kwaɗo.

Umm Allah gatan bawa.

 

Da nay yi laccara in sassai da mutuncina,

Gwara nay yi wasan dambe ko na yi jido,

Umm Allah gatan bawa.

 

Ya Ubangiji mai kyauta mai gyarawa,

Gyara jami’a ka rabauta ta da ‘yan ɓarna.

3.2 Jami’a Gidan Bankashi - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 44)


Post a Comment

0 Comments