Ticker

6/recent/ticker-posts

Bara a Kufai

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

Zo mu je bara Mairamu zo mu je bara a kufai.

Alan waƙa Mairamu ba ta yin bara a kufai.

Mai ya sa haka Mairamu ba ki yin bara a kufai?

Yin bara a makwantai ne bara a kufai,

Yin bara a makwantai ai ba za a ji ba,

Yin bara a kufai ma ai ba za a ji ba,

Yin bara a muhallan da ba za a ji ba,

Ka ga ka yi bulayi bara a kufai.

 

Amshi: Gara nai bara da bulayi bara a kufai.

 

Ubangijin Annabi Musa da Haruna,

Ubangijin alyassa hal Sulaimana,

Ubangijin Annabi Ayuba manzona,

Ubangijin Ibrahimu Isa manzona,

Ubangijin Zakariya da Nuhu manzona,

Ubangijin afalal kairi kalƙi indalla,

Muhammadu rasulullahi mai halin dubbai.

 

Eh, duniya mai yayi mai yawar yalwa,

Duniya mai auren ribatar wawa,

Ɗuruwar wawa marar rabon baiwa,

Yau a wayi gari kai ne ka walawa,

Watta ran ai da waninka ka zamo gawa

Sai a kai ka kushewa can a bunnewa,

Sai halinda ka aika yau cikin dubbai.

 

Na sani adon tafiya waiwaye adon tafiya,

Taffiya babu ado ni ba za ni yi ba,

 

Ki mai shirin tamɓele af fagen tafiya,

Ai watan wata rana ai ba za ka yi ba,

 

Kyan taffiya dawowa af fagen tafiya,

A taffiya mai dace ni ba za na ƙi ba.

 

Gaya wa mai sara in ya ɗauki fartanya,

In ya sara duba ko ba za ta ci ba.

 

Gaya wa mai ratse ya fa ratse kan yanya,

Kar ya kai kansa mahallaka ba zan so ba.

 

Rabbu kats tsare mu bulayi yin bara a kufai,

Yin bara a muhallan da ba za a ji ba.

 

Malamai ‘yan duba,

Sun bara a kufai.

 

‘Yan siyasar banga,

Sun bara a kufai.

 

Shugabannin cuta,

Sun bara a kufai.

 

Masu halin ɓera,

Sun bara a kufai.

 

Mai shirin tamɓele,

Yai bara a kufai.

 

Mai zaman kashe wando,

Yai bara a kufai.

 

Dandalin ‘yan caca,

Sun bara a kufai.

 

Masu waƙar batsa,

Sun bara a kufai.

 

Mai rubutun batsa,

Ya bara a kufai.

 

Masu fim ɗin batsa,

Sun bara a kufai.

 

‘Yan rawar nanaye,

Sun bara a kufai.

 

Da masu kayan maye,

Sun bara a kufai.

 

Mayaudaran ‘yammata,

Sun bara a kufai.

 

Masu ƙwacen hanya,

Sun bara a kufai.

 

 

Fasiƙai munafukai,

Sun bara a kufai.

 

Masu mufun aiki sun bara a kufai,

Gara nai bara da bulayi bara a kufai.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar

Post a Comment

0 Comments