Ticker

6/recent/ticker-posts

Gabatarwa - Daga Diwanin Wakokin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Waƙa zance ne mai tattare da hikima da tsari cikin sautin murya mai zaƙi da jan hankali, wadda ake yin ta domin isar da saƙo ga al’umma. Irin wannan saƙo shi ake kira da jigo, wanda kuma ke bijirowa ta fannoni daban-daban cikin sha’unan rayuwar al’umma. A wannan babi za a gabatar da waƙoƙin ALA ne masu jigon ilimantarwa da wa’azantarwa da kuma faɗakarwa. Duk da cewa waɗannan batutuwa suna cin gashin kansu, to ana kuma iya samun su ɗamfare a farfajiyar ilimantarwa. Wato kamar yadda batutuwan wa’azantarwa kan nufi al’amuran addini, kuma na faɗakarwa suka fi karkata ga wayar da kai, to a gaba ɗaya ana iya dunƙule su a matsayin ilimantarwa. A taƙaice dai, jigon waɗannan waƙoƙi ya taɓo waɗannan muhimman batutuwa guda uku.


Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar

Post a Comment

0 Comments