Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta'ziyyar Maitama

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi I

Ɗan Masanin Kano mutuwarka,

Ta gwada gwargwadon kimarka.

 

Amshi II 

Da kuri'a ake dangina

Ɗan Masani ba zai ƙaura ba.

 

Shimfiɗa

Jallah wa azza babban Sarki,

Mai ara mamlaka gun sarki,

Yai mutuwa a gun wasu sauƙi,

Yai mutuwa a gun wasu aiki,

Yarda da buruka na mafarki,

Ɗan Masani ka ba shi masauki,

Don ahalin gida na ma'aiki,

Yarda da sahibi na ma'aiki,

Kyautata kwanciya a masauki,

Ƙamsasa kabbarinsa da miski.

 

Rabbu Ubangiji Masarauci ga ni a durƙushe a gabanka.

Na zaka durƙushe a gareka don marsiyya gun bawanka,

Ɗan Masanin Kano bawanka Maitama mai yabo a gareka,

Wanda ka ba aron numfashi yau ka kira shi barzahu gunka,

Da kuri'a ake ɗan Yusufu Maitama da ba zai ƙaura ba.

 

Na yabi annabi da salati ali wa sabihi na gidansa,

Salli ALA rasulullahi Rabbu wasilatun a gurinsa,

Mai matsayin muƙamai annabi wanda ka ɗauka darajarsa,

Wanda ka ɗaukaka kololo gun matsayi ba ay yi kamarsa,

Don matsayinsa fadar Allah 'Ɗan Masani a mai marhaba.

 

Ran uku ga watan Yulin nan ta riske ni ne a Kaduna,

Ranar Litinin tai daidai two tHausand seɓenten rana,

Na buɗe wayata kenan sai na ga saƙuna da idona,

Saƙon muttuwar gwarzona inda na bincika hotunna-

Sun cika ko ina ta'aziyya ke yi wa Maitama da muhibba.

 

Sai na mayar da linzamina BBC da murya Amurka,

Neman tabbaci da yaƙini don raba kai da mai kundin ka,

Nan na ishe bayanai tsantsa kan mutuwar gwani saka kuka,

Sai mutuwar jiki ta ishe ni can ciki zuciya na kuka,

Sai na tuno rabon mu da baba an yi rashi ba za a mayar ba.

 

Wannan shekaru fa Kanawa an yi rashin mazajen fama,

Mai Kano ya tafi ba nisa sai ko galadima mai girma,

Ga kuma sahibi na haƙiƙa jagoran matasan fama,

Maitama tarrago na matasa koko na ce kadarkon umma,

Mai horo ga ulul amri su riƙe gaskiya ba gaba.

 

Wannan muttuwar jagora ta sa ka nai lakwas da jikina,

Ta katse buruka da muradai ta sarayar da al'amrana,

In da na juya kai da tunani sai na ji laffuzan gwrzona-

Na ya gizo suna karakaina in yi kamar in ce wai kaina,

Yanzu mazan jiya an ƙaura wa ya rage Arewa da hubba?.

 

Yai hidimar ƙasa ba ƙaidi Maitama Yusufu gogana,

Ya yi minista loton jigo Sardaunanmu mai raba gona,

Ya yi jakada ambassada Ɗan Masani abin so ƙauna,

Sannan yai fice a siyasa ya zama zakkara a sanina,

Shi ya ci takarar NPN aka hana shi ba ƙarya ba.

 

Ya zama shugaba na matasa duk na Arewa mai alfarma,

Zamanin Gawan can baya Ɗan Masani mazajen fama,

Loton Audu Baƙo a Kano nineten seɓenty-fiɓe ba dama,

Ni haka nab biya da idona littafin uba mai girma,

Ɗan uba Adamu na Daneji jagora garen kuma baba.

 

Taro ko Arewa da Kudu ƙasaitarsa Maitama nawa,

Taron mamlaka ta sarakai Maitama ne ake dubawa,

Taron mamlaka na hukuma Maitama ne ake hangowa,

Masu faɗa a ji na karaɗe in ya yi nasa ya rufe kowa,

Ɗan Masaninmu rumbun baiwa mai lafuzan da kan sa haiba.

 

Kai da ganin shigar ɗan birni ka san ya fice da saninka,

Babu abin da ke burge ni sauƙin kansa babu nifaka,

Ga riƙe martaba ta mutane bai ƙyamar ka ko yarenka,

Bashi abin bugu da misali sai alfanda mai albarka,

Yanzu a kabinet Sardauna wa ya rage da bai ƙaura ba?.

 

Na tuna ɗan Muhammad Nasir justice namu bai ƙaura ba,

Kura ɗan galadiman nan justice na yaba ka da haiba,

Nasiru kai na wa ta'aziyyar Maitama don ba zan manta ba,

Na tuna sanda yay yi kirarin ka gabanka ban manta ba,

Yai maka baituka na yabonka kan alƙawwari ba wai ba.

 

Ga marasiyya nan na aiko gun ahalin gida na ubanmu,

Ga ta'aziyya nan na karanto gun jama'ar Kano ƙaryarmu,

Ga alhini nan na taya ku lardinmu Arewa ƙasarmu,

Yan Nijeriya ku taya mu yi masa addu'a babanmu,

Don rasa Maitamanmu rashi ne ya taɓa duniya ba wai ba.

 

Rabbu Ubangiji mawadaci mai rahamar da ba ƙarewa,

Kai mana alkawar mui roƙo kai kuma kai kake badawa,

Ka kuma ce idan mun gode aiki naka kai ƙarawa,

Mun gode da kyauta tsoho ka karɓe shi kai mar yalwa,

Yalwata kabbarin babanmu Maitama addu'ata Rabba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments