Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutuwa Rigar Kowa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Mutuwa na ce rigar kowa wanda yas saka bai kufce ba,

Wanda anka yi masa numfashi dole muttuwa zai ɗana ta.

 

Lala'ila ha illAllah Allah khaliƙi guda da ake bauta,

A ƙuluhiyarka buwayayye kai ka keɓu mu yi ma bauta,

A rububiya ta halittunka kauni kai ka keɓu da ƙaga ta,

Asamu al-husuna Allah naka ne saninsu cikin bauta.

 

Rabbu darraja da kamalarka ka daɗa su gunsa masoyinka,

Da ka ɗaukaka shi ka fifita a saman halittu bayinka,

Mai Muƙamal Mahamudun nan da ka ce da shi makusancinka,

Daɗa wanda zai zama da'im yau ba kamarsa dukka abin bauta.


Inda rayuwa aka jirkinta kullu nafsu za'ikatul mauta,

Mutuwa na ce rigar kowa wanda ke da rai zai dana ta,

Kullu nafsu za'ikatul mautu sadarar da ke kada hantata,

Sun rigamu ba su yi sauri ba haka za waɗanda ka jirkinta.

 

Duk wanda ya sa rigar rayi ya sa taguwar mutuwa kanta,

Wani zata zo a ruwan sanyi wani sai anai masa firfita,

Wani muttuwa a garai hutu wani jannatu wani shi ko wuta,

Rabbu karɓi baƙuntar Abdu huru'ini sui masa firfita.

 

Wani ta ishe shi a jinka tai shigifarsa har a gadon barci,

Wani ko yana tasbihinsa wani yanzu ya gama kalaci,

Wani ya tafi a gurin nema don halaliyar masu fatauci,

Abdu gabiya an sha jinya Rabbana ka sanya ya huta.

 

Almautu wahidun haka za kuma sabbabinta kasiran ne,

Ma takaddama min zambihin wa ma ta akkara duka ja'iz ne,

Rabbuna gafuru rahimun ne rahamarsa ta gama komai ne,

Rabbu ka jiƙan magabatanmu kabari ya zam masu mahuta.

 

Shi ya sa ake son duk mai rai ya yi saddaka daga samunsa,

Sadakattu jariya don kansa mai gudanuwa ko ba ransa,

Ka yi ɗan gini na masallaci rijiya ka yo da mudarrisa.

Ko ka haifi ɗa mutumin kirki ko abin yabo daga maƙƙota.

 

Shaidar mutane na a ciki na sahun gaba a zaton rahama,

Shaidar iyalai na a sahu na gaban gaba a zaton rahama,

A zato na kirki sai shukuran da yabo a bakin al'uma,

To bara na baku kaɗan a yabo na amarsatu gun angonta.

 

A’ishatu Idi ta shaidar ta yaba da halayya tasa,

A cikin shaƙiƙai gun Abdu ta isar ta ƙarfafi shaidarsa,

Matsayinta matar aurensa takabarsa ta yi a dakinsa,

Ga yabon da tay yi a kan Abdu na abin da yai a idanunta.


Mai faranfaran ga iyalai ne mai halin a so layin kyauta,

Mai haba-haba da iyaye ne kyauta yinsa ya fi na lasafta,

Babu inda anka baro Abdu in ji su Anas mai shaddata,

Allah karɓi baƙuncin Abdu rahamarka Rabbu ka ninka ta.

 

A cikin shahidai an zano wanda yac cika da kiran Allah,

Haka mumini da ruwa yac ci koko gobara da ka sa ƙwalla,

Mace mai ciki da mazam fama masu jaddada kalmar Allah,

Ga ko mumini da wafatinsa Juma'attu ranar yin bauta.

 

Kai baƙar takobi mai yanke soyuwar miji a gurin mata,

Ɗanɗano na ɗaci ko galmi babu makkawa a tsotsa ta,

Mai maraita manya har yara ta gwagwarta sahibbar mata,

Raɗaɗinta ba a misalta shi sai fa anbato na abin bauta.

 

Rabbana ka kyauta makwancinmu ran da za mu amsa kira naka,

Yarda annabinka ya cece mu gafararka Rabbu nake roƙa,

Randa babu babu wajen hutu babu innuwa sai zatinka.

Sa da gabiya a cikin ceto na Muhammadu baban Binta.

 

Malam Abdullahi garin Tsoho Dotti na yi ma ta'aziyyata,

Sai uwa ma ba yaya mama A’ishatu ga ta'aziyyata,

Doktoro. Hakim B. Ahmad na yi baitukan ta'aziyyata,

Anas M. Shadda sahu sahun wanda nay yi wa ta'aziyyata,

Na haɗo Sadiƙ Abdullahi sahibi shaƙiƙi ba wauta.

A’ishatu Idi Maman boy rukunin sahun ta'aziyyata.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments